‘Yadda Dokar Aikin Dan Sanda za ta inganta aikin ’yan sanda’

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu kan dokar sauye-sauye ga ayyukan ’yan sanda ta 2020 da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ita. Yanzu ta zama doka wadda ta tanadi yadda za a inganta ayyukan ’yan sanda ta fuskar samar musu da kudade da kayan aiki yadda ya kamata da kuma kare hakkin […]

‘Yadda Dokar Aikin Dan Sanda za ta inganta aikin ’yan sanda’

Shugaban ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu kan dokar sauye-sauye ga ayyukan ’yan sanda ta 2020 da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ita.

Yanzu ta zama doka wadda ta tanadi yadda za a inganta ayyukan ’yan sanda ta fuskar samar musu da kudade da kayan aiki yadda ya kamata da kuma kare hakkin dan Adam don inganta tsaro.

Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Pankshin, Kanke da Kanam na Jihar Filato, Yusuf Adamu Gagdi ne ya gabatar wa Majalisa da kudirin dokar, ya bayyana yadda dokar take da kuma amfaninta a wata tattaunawa da ya yi da BBC.

A cewarsa, “An ce a samar da yadda al’umma za ta sa hannu a cikin aikin ’yan sanda ta wajen ba da bayanan da za su kawo tsaro ga mutane.

Da yadda al’umma za ta zama cikin duk wata harkar tsaro da ta same ta, kwanakin baya Shugaban Kasa ya amince da fitar da Naira biliyan 13 don aiwatar da wannan aiki.

“Na biyu akwai abin da ya shafi al’umma ta yadda a wasu lokutan ’yan sanda kan kama mutum har ya yi sa’a 48 ko fiye a hannunsu ba a kai shi kotu ba.

“Ya kamata ne daga lokacin da aka kama mutum to ya yi sa’a 24 kawai a hannun ’yan sanda a gurfanar da shi a kotu.

“Idan ’yan sanda ba su iya sakin sa a wannan lokaci ba, to sai su samu umarnin kotu don ci gaba da tsare mutum fiye da tsawon hakan”, inji shi.

Ya ce “Sauran abubuwan sun hada da yanayin aikin dan sanda da albashinsa.

“Sau da yawa za ka ga dan sanda a kan titi amma albashinsa bai fi Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 45 ba a wata.

“Ana nufin mutum yana kan titi yana aiki tsawon wata daya amma a biya shi wannan dan kudi?

“Bai je ya kula da iyalansa sosai ba, ta yaya ma kudin za su ishe shi cin abinci da sutura da sayen man mota?

“Wannan doka ta dauki kudirin gyara hakkin ’yan sanda don ganin an magance karbe-karben kudi a hanya.

“Haka kuma daga ran da aka samar da Hukumar ’Yan sanda za ka ga shugabanninta wani ya yi shekara daya ya tafi, wani biyu ya tafi, ba a bari shugabannin su dade a kan matsayin don yin gyaran da suka zo yi.

“Wannan doka ta gyara hakan cewa ya kamata ofishin Shugaban ’Yan sanda ya samu kariya don ganin ya tsaya tsawon wani lokaci kamar shekara hudu, don samun damar yin gyaran da ya kamata, ba wai ya yi shekara daya kawai ya tafi ba.

“Idan har aka ga yana daukar shekaru bai yi aikin da ya dace ba, sai Shugaban Kasa ya cire shi bisa karfin ikon da dokar kasa ta ba shi,’ inji shi.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu