Yadda duniya ta yi tir da Gwamnatin Myammar kan kisan gillar Rohingya

Jami’an tsaron Myammar da Shugabar Gwamnatin  farar hula Aung San Suu Kyi na shan suka daga ko’ina cikin fadin dunjiya saboda kisan gillar da ake yi wa tsirarun Musulmin Rohingya. Kiman in mutum dubu 123 suka yi hijira daga kasar kamar yadda Majalisar dinkin Duniya ta bayyana, sannan wasu mutum dubu 90  sun bazu zuwa […]

Yadda duniya ta yi tir da Gwamnatin Myammar kan kisan gillar Rohingya

Jami’an tsaron Myammar da Shugabar Gwamnatin  farar hula Aung San Suu Kyi na shan suka daga ko’ina cikin fadin dunjiya saboda kisan gillar da ake yi wa tsirarun Musulmin Rohingya.

Kiman in mutum dubu 123 suka yi hijira daga kasar kamar yadda Majalisar dinkin Duniya ta bayyana, sannan wasu mutum dubu 90  sun bazu zuwa kasar Bangladesh cikin kwana 10 da ake ta artabu tsakanin mayaka da sojojin Myammar a filin dagar da Yammacin Jihar Rakhine, inda kabilar Rohingya suka fi yawa.

Tuni dai aka tursasa wa Rohingya zama karkashin tsarin wariya a kasarsu ta haihuwa, inda aka tauye musu  duk wata walwalar kai-kawo a fadin kasa, tare da hana su mallakar izinin zamaz ’yan kasa.

Sojojin Myammar sun karyata rahoton keta haddi da ake yi wa Rohingya, amma Al Jazeera ta ruwaito yadda tashe-tashen hankulan baya-bayan nan ya faro tun daga Oktobar bara, lokacin da wasu ’yan tsirarun mayakan Rohingya suka yi wa jami’an tsaron kan iyaka kwanton bauna, sai kawai aka far musu, al’amarin da Majalisar dinkin Duniya ta ce sojojin Myammar sun mayar da martini da kisan kare dangi.

Aung San Suu Kyi, tsohuwar fursunar siyasa Gwamnatin sojan Myammar tana fuskantar mummunar matsin lamba da la’ana saboda kin magana da daukar mataki da ta yi kan yadda ake azabtar da Rohingya bnallantan ta gargadin sojojin su shiga taitayinsu.

Yanghee Lee, Jami’ar binciken Majalisar dinkin Duniya kan al’amuran da suka shafi hakkin dan Adam a Myammar, ya yi matukar nuna damuwarsa tun a farkon da ya gabata kan cewa “dubban mutane na tattare da hadari afkawa cikin mummunan tashin hankalin keta haddin dan Adam.”

Litinin dinn da ta gabata kafofin yada labaran  Indiya sun ruwaitota tana cewa:”Halin da ake ciki ta yiwu a ce shi ne mafi muni a tsawon tarihin Myammar.”

Shi kuwa Sakatare-Janar na Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga sojojin Myammar da su yi takatsantsan, kamar yadda mai Magana da yawunsa ya bayyana.

“Wannan hali da ake ciki na nuni da daukar matakin gaugawa don magance wannan  matsalar da ke haifar da tashin hankali tun daga tushe,” kiamar yadda yake kunshe a bayanin maimagana da yawun Sakatare-Janar na Majalisar dinkin Duniya Eri Kaneko.

Ita kuwa Malala Yousafzai, ’yar Pakistan da ta samu lambar yabo ta Nobel ta kara baza sukar lamirin Majalisar dinkin Duniya kan mawuyacin halin da aka jefa rohingya a Myammar,  kamar yadda ta rubuta a shafinta na Twitter.

“A kowane lokaci na nma gani a labarai, sai zuciya ta buga kan mawuyacin halin da Musulmin Rohingya ke ciki a kasar Myammar,” a cewar Yousafzai, wadda ta shahara bayan da harsashin ’yan Taliban ya huda mata kai.

“Tsawon shekarun da suka gabata na sha sukar lamirin wannan mummunar abin kunya da ake yi. Har yanzu ina jira sauran ’yar uwata mai lambar yabo ta Nobel Aung San Suu Kyi ta kwata irin hakan,” inji ta.

Ministan harkokin wajen Malesiya Anifah Aman ya bukacin bin kadin shirun da Aung San Suu Kyi ta yi kan wannan mummunan lamari.

Saboda tur da Allah wadarai da mafi yawan kasashen musulmin Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya suka yi kan wannan kisan gillar da ake yi wa Rohingya a kasar suna barazanar daukar matakin difulomasiyya a kan kasar. Wannan kasashe dai su ne Malesiya da Indonesiya. Kuma Maldibes ta bayar da sanarwar yanke huldar jakadanci da kasar, “har sai Gwamnatin Myammar ta dauki matakin shawo kan keta haddi da ake yi wa Muslmin Rohingya,” a cewar Ministan harkokin kasashen wajen Maldibes.