Yadda fadada kasuwa ya haddasa rusau a unguwar Hausawan Sabo-Ilesha

Al’ummar unguwar Sabo Ilesha da ke jihar Osun sun wayi gari cikin tashin hankali, bayan da gwamnatin jihar ta rushe unguwarsu bayan ta aike masu da takardar da ta umarce su da su tashi cikin makwanni uku, lamarin da ya sa suka shigar da ƙara kotu, inda bayan ta saurari ƙarar ta ɗage ta zuwa […]

Yadda fadada kasuwa ya haddasa rusau a unguwar Hausawan Sabo-Ilesha

Al’ummar unguwar Sabo Ilesha da ke jihar Osun sun wayi gari cikin tashin hankali, bayan da gwamnatin jihar ta rushe unguwarsu bayan ta aike masu da takardar da ta umarce su da su tashi cikin makwanni uku, lamarin da ya sa suka shigar da ƙara kotu, inda bayan ta saurari ƙarar ta ɗage ta zuwa 18 ga watan gobe, amma kwatsam sai jami’an gwamnatin suka shigo unguwar ta Sabo Ilesha suka fara rusau a ranar Alhamis ɗin makon jiya, kwanaki biyu da zaman da kotu ta yi na ƙarshe a kan maganar.

Sarkin Hausawan Ilesha, Alhaji Alhassan Muhammad wanda ya shaida wa Aminiya cewa kimanin shekara 47 da ta gabata suka mallaki filayensu. Ya ce babban basaraken Yarabawa na yankin ne ya mallaka masu filin tun wurin yana jeji, kuma ƙaramar hukuma ta yi masu takardun wajen, inda tun a wanccan lokacin suka biya Naira 100 a kan kowane fili. Ya ce shi ne ya fara gina gida a wajen tun yana ƙungurmin daji.

 “A lokacin da na tare, mutanenmu ƙin zuwa suka yi saboda wajen daji ne ƙwarai. Daga baya sai muka buɗe kasuwa, a hankali wajkn ya zama gari. Sai yanzu gwamnatin ta ta aiko mana da takarda cewa mu tashi cikin mako uku. Mutum da gidansai? Sai muka shigar da ƙara kotu, maganar na kotu suka zo suka fara rushe mana gidaje,” inji shi.

Ya ce su ba ɓarayi ba ne da za a kore su daga waje a rana tsaka. A cewarsa, shi kan sa a Jihar Osun aka haife shi, ya kuma haura shekara 80, sai ga shi gwamnatin ta rushe gidajensu da fadarsa da sunan za ta yi kasuwar zamani. A kan haka ya yi kira ga shuwagabannin Arewa da su kai masu ɗauki.

Magatakardar masarautar ta Ilesha ya shaida cewa ganin bunƙasar yankin ne ya sanya gwamnatin jihar ta raba su da gidajensu. “Bayan da kakanninmu suka gina gidajensu a nan sai suka kafa kasuwar Sabo. Daman bisa al’adar Bahaushe a Kurmi, idan ya kafa unguwa sai ya yi kasuwar Sabo, sai ’yan kasuwa daga Arewa suka dinga sauke hajarsu. A haka har waje ya bunƙasa ya zama alƙarya. Ganin yadda wurin ya ci gaba ne ya sa gwamnatin take so ta karɓe amma idan maganar faɗaɗa kasuwa ne ai akwai fili sama da hekta biyu, wanda rami ne da ya kamata gwamnatin ta cike. Yin haka mu ma amfaninmu ne, in an faɗaɗa kasuwar kuma cike wannan ramin zai kawar da ɓata garin da ke fakewa a wajan amma sai a inda iyayenmu suka sha wuya suka gina gwamanati za ta rushe da sunan faɗaɗa kasuwa don maida ita ta zamani?” Inji shi.

Aminiya ta zanta da wasu daga cikin mazauna yankin, waɗanda aka rushe gidajensu. Alhaji Abubakar wanda gidansa ne aka fara rushewa, ya shaida wa Aminiya cewa ya yi hasarar sama da Naira miliyan 30 a tsakanin rumfunar kasuwa da gidansa da aka rushe. Ya ce ko tsinke ba a barsu sun ɗauka ba. Hakan ne ya sanya suka yi hasarar muhinmmam takardunsu da kuɗin cinikinsu da suke ajjiyarsu a gida.

Jama’ar da rusau din bai isa ga gidajensu ba a lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci yankin suna ta cire kwanukan rufin gidajensu da ƙyamare da tagogi da nufin kada su yi hasarar gidan kacokan.

Wata malamar makarantar sakandare mai suna Maryam Bello Akinyola ta shaida wa Aminiya cewa ta shafe sama da shekar 25 tana gina gidanta. “Da ɗan abin da nake samu na albashina da adashin gatan da muke yi, shekaru biyu ya rage mani na yi ritaya daga aiki, don haka nake aikin gidan domin na saka haya na dinga samun kuɗin kula da kai na da ’ya’yana da suke makaranta. Kwatsam sai aka faɗa mani cewa an fara rusau a Sabo Ilesha, don haka na sa ma’aikata su cire kwnon rufin gidan. Na kashe sama da Naira miliyan 15 amma ginin sai ga shi a rana tsaka an rushe. Fatanmu gwamnatin ta tausaya mana ta biya mu diyya,” inji ta.

Aminiya ta tuntuɓi mai ba Gwamna Ra’uf Arebgesola shawara a kan harkokin baƙi, Malam Bashir Imam wanda ya tabattar da cewa gwamnatin jihar za ta gina kasuwar zamani ne a yankin, don haka ta tashe su. Ya ƙara da cewa maganar ta daɗe a ƙasa. Ya kuma yi iya bakin ƙoƙarinsa don ganin ya taimaka wa al’ummar yankin saboda wakilcin da yake masu. Ya ce matsalar ita ce, mutanen sun yi gudaje ne a filayen da ba su da takardu. “Babu wata gwamnati da za ta rushe wa mutane gidajensu matuƙar suna da takardunsu. Na yi bakin ƙoƙarina na cewa su nuna takardun, sun ce suna da su amma ni ban gansu ba,” inji shi.

Tuni dai mata da yara ke ci gaba da rayuwa a cikin ɓaraguzan gidajen da aka rushe, yayin da aka kama wa Sarkin Hausawan hayar wani gida a gefen garin.