Yadda farashin kaya ya yi tashin gwauron zabi a Jigawa

Farashin kaya, musamman abinci da sukari, ya yi tashin gwauron zabi a jihar Jigawa. Hakan dai ba ya rasa nasaba da kamawar watan azumi da kuma karancin kayan sakamakon annobar coronavirus da ta addabi duniya baki daya, lamarin da ya haifar da cunkoso a shaguna yayin da jama’a ke rububin sayen kayan shan ruwa. Wakilinmu […]

Yadda farashin kaya ya yi tashin gwauron zabi a Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar

Farashin kaya, musamman abinci da sukari, ya yi tashin gwauron zabi a jihar Jigawa.

Hakan dai ba ya rasa nasaba da kamawar watan azumi da kuma karancin kayan sakamakon annobar coronavirus da ta addabi duniya baki daya, lamarin da ya haifar da cunkoso a shaguna yayin da jama’a ke rububin sayen kayan shan ruwa.

Wakilinmu na Dutse, babban jihar ta Jigawa, ya ziyarci kasuwa da ma wasu shaguna da ke birnin, inda ya gane wa idonsa yadda jama’a suke neman sukari da shinkafa.

Wani mai shayi, Alhaji Umaru Ado Fagoji, ya ce a baya suna sayen kwanon sukari N950, amma a ranar Juma’a farashin ya kai N1,500.

“Kuma ma babu, ya zama nema. Yanzu kaf kwaryar Dutse babu shagon da ake sayar da sukari, ya kare; sai dai idan kasuwar bayan fage ce”, inji shi.

Ita kuma Hajiya Bilkisu Mai Abincin Gayu cewa ta yi farashin kayan abinci ya hau sosai.

“Shinkafa ‘yar gwamnati a da ana sayen ta N1,200, a yau ta zama sai nema a kan N1,500.

“Ita Kuma shinkafa ‘yar Hausa wadda kafin azumi ake sayar da ita a kan N750 mai kyau yanzu ita ce N800”, inji Hajiya Bilkisu.

Ta kuma ce akwai bukatar gwamnati ta taimaka a kan matsalar rayuwar da ake ciki.

“Talakawa suna cikin halin kuncin rayuwa matuka; bayan cutar coronavirus da ake yaki da ita ya kamata gwamnati ta yi yaki da yunwa, in ba haka ba za a yi haihuwar guzuma, da kwance uwa kwance”.

Wani bawan Allah da ke sayar da kaya a daya daga cikin manyan shagunan cikin garin na Dutse ya ce ’yankasuwar suna cikin matsala saboda “matakin da gwamnatin Kano ta dauka na rufe kasuwa da jihar baki daya, ba shiga ba fita.

“Kaya sun yi tsada; babu wata hanya da sukari zai zo jihar Jigawa sai an kawo Kano; babu wata hanyar da za a kawo shinkafa Jigawa sai ta Kano”, inji dan kasuwar.

Ya kuma ce yanzu haka suna samun shinkafa daga bakin iyakar kasa a Babura a kan N20,000 zuwa N22,000 su kuma suna sayar da ita  akan N27,000, amma wasu suna sayar da shinkafar ‘yar waje har N28,000.

Ya kara da cewa matukar gwamnati ba ta dauki matakin wadata jama’a da abinci ba babu makawa za a samu katuwar matsala saboda an takure komai, kasuwa ta tsaya cik.

Gwamnatoci a sassan Najeriya daban-daban sun ayyana dokar hana fita da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Sai dai ko an rufe kasuwanni, akan kyale masu sayar da abinci da magunguna su bude shagunan su.

Ita ma jihar Jigawa ta dauki matakin rufe iyakokin ta da nufin hana shiga mata da cutar ta COVID-19.