Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa

Yawan shigo da kayan amfanin gona da aka yi a baya-bayan nan shi ma ya taimaka wajen faɗuwar farashin.

Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa

Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna.

Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar.

Haka kuma an ce, jihohin da ba sa noma suna jin tasirin rage farashin kayan abinci.

Masana sun danganta faduwar farashin da aka samu a kasuwa ga karancin kudi da kuma yadda aka yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, wanda hakan ya haifar da faduwa farashin sosai.

Wasu kuma sun ce, yawan shigo da kayan amfanin gona da aka yi a baya-bayan nan shi ma ya taimaka wajen faɗuwar farashin.

Misali, buhun fulawa mai nauyin kilo 50, wanda ake sayar da shi kan Naira 80,000 a ’yan makonnin da suka gabata, yanzu ana sayar da shi ne tsakanin Naira 61,000 zuwa Naira 63,000 ya danganta da kasuwa.

Farashin hatsi ya ragu, sai dai na gyada da koko da dawa da dankalin Turawa da dabino da mai da kayan lambu sun dan yi tsada a kasuwanni da dama da wakilanmu suka zagaya.

Kaduna

A kasuwar hatsi ta Saminaka da ke Jihar Kaduna, buhun masara mai nauyin kilo 100 da ake sayar da shi tsakanin Naira 70, 000 zuwa Naiera 75,000 a mafi yawan kasuwanni a lokacin girbi, yanzu ya dawo Naira 47,000, yayin da waken soya da ake sayar da shi a baya a kan Naira 110,000, yanzu ya koma Naira 68,000.

Hakazalika, nau’in farin wake da ake sayar da shi kan Naira 150,000 a lokacin girbi, yanzu ya zama N100,000.

A kasuwar Giwa da ke Jihar Kaduna, ana sayar da gero da dawa tsakanin Naira 50, 000 zuwa Naira 51,000 sabanin Naira 79,000 zuwa N80,000 da aka sayar a bara.

Farashin wake ya fadi daga Naira 120,000 zuwa Naira 80,000; farin wake daga N160,000 zuwa Naira 88,000; irin shinkafa, Naira 75,000 zuwa tsakanin N55,000 zuwa N60,000.

Taraba

A kasuwar hatsi ta Mutum Biyu da ke Jihar Taraba, farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 100 a yanzu ya kai Naira 45,000 sabanin Naira 50,000 a watan da ya gabata; buhun masara mai nauyin kilo 100, ana sayar da shi a baya a kan Naira 57,000, yanzu yana tsakanin Naira 40,000 zuwa N45,000; buhun rogo mai nauyin kilo 100, a baya Naira 25,000, yanzu ya zama Naira 18,000 da N19,000.

Binuwai

A Kasuwar Wadata da ke Makurdi a Jihar Binuwai, buhun shinkafa ta gida mai nauyin kilo 50 a yanzu ya kai Naira 26,000 zuwa Naira 29,000 sabanin Naira 45,000 zuwa Naira 55,000 da ake sayar da shi kimanin wata shida da suka wuce.

A Kasuwar Zamani, farashin laka na shinkafa ya ragu daga Naira 2,700 zuwa N1,800, kamar yadda Aminiya ta tattaro.

Haka kuma babban kwandon tumatur, wanda a baya ana sayar da shi kan Naira 45,000, yanzu haka yana kan Naira 30,000 zuwa Naira 35,000.

Farashin mudu na masara da gero da masarar Guinea ya fadi daga Naira 3,200 zuwa Naira 1,200; kwanon dabino, yanzu ya zama N1,800 daga Naira 2,500; robar garri Naira 2,300 daga Naira 3,500; doya 10 tsakanin Naira 10,000 zuwa Naira 15,000 daga tsakanin Naira 12,000 zuwa Naira 18,000.

Kano

A Jihar Kano ma wakilinmu ya ruwaito faduwar farashin kayan abinci. A kasuwar Danhassan, farashin kwano na wake ya ragu zuwa Naira 2,500 daga Naira 3,500; gero Naira 1,200 daga Naira 2,700.

A Kasuwar Dawanau, kwanon masara yanzu yana tsakanin Naira 1,200 zuwa Naira 1,300; gero, Naira 1,000 da Naira 1,100; wake tsakanin Naira 2,000 zuwa Naira 2,200 kowane mudu.

Neja

A kasuwar Manigi da ke Karamar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, farashin buhun jan wake ya fadi daga Naira 200,000 zuwa Naira 90,000 daga Naira 200,000; sai farin wake ya koma Naira 90,000 daga N160, 000; inda farashin farar masara da ja ya koma Naira 40,000 a kowane buhu, maimakon Naira 85,000 da ake sayarwa a baya; gero a yanzu Naira 45,000 ne; dawa Naira 40,000; buhun wake Naira 78,000 sabanin Naira 135,000 a bara.

A Kasuwar Lemu, a halin yanzu ana sayar da buhun gero da masara da dawa kan Naira 42,000; da buhun shinkafa (nika) 100 kilo Naira 108,000.

A garin Bida, wani dan kasuwa, Mohammed Mahmud ya bayyana cewa, farashin shinkafa ’yar gida ya fadi daga Naira 130,000 zuwa Naira 120,000 kan kowane buhu.

Buhun dawa da gero yanzu ya zama Naira 45,000; masara Naira 48,000. A kasuwar karshen mako ta Gwadabe, wakilinmu ya ruwaito cewa, farashin shinkafa da masara da dawa ma sun fadi.

Gombe

A babbar kasuwar Gombe bangaren ’yan shinkafa da a kwanakin baya ake sayar da babban buhun shinkafar dafawa mai nauyin kilo 100 a kan farashi mabambanta bisa ga kyawun shinkafar da ya kai hawa uku na Naira dubu 180,000 da dubu dari 160,000 da dubu 150,000 yanzu haka farashin ya fadi.

 

An kama ɓarayin waya a Kano

Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa

HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato

An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe