Yadda fasto ‘ya babbake’ miloniya yayin yi masa addu’a

Faston ya tsere bayan konewar Miloyinan da ya dauki nauyin karatun dalibai 40.

Yadda fasto ‘ya babbake’ miloniya yayin yi masa addu’a

Tsohuwar ajiya.

Wani fasto ya ‘babbake’ wani miloniya mazaunin birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a yayin addu’ar nuna godiyar attajirin.

Miloniya Kayode Badru na tsaye fasto na masa addu’a ne wuta ta kama shi gadan-gadan a Cocin Celestial Church of Christ (CCC) a yankin Imole, a Alagbado da ke Jiharsa ta Legas.

An garzaya da dan kasuwan wanda ake yi wa lakabi da Kay Money zuwa asibiti, amma rai ya yi halinsa, shi kuma faston da ke masa addu’a, ya riga ya yi layar zana.

A watan Afrilu, Kay Money ya halarci bikin yaye matasa 40 da ya dauki nauyin karatunsu a wata kwalejin fasaha da kere-kere mai zaman kanta, mai suna Academy for Innovative Art and Technology (ACIATECH).

An gudanar da waccan bikin yaye daliban a dakin taro na otel din Edcellence Hotel da ke Ogba Aguda, Ijaiye, Legas, inda basaraken yankin Alaguda na kasar Agudaland, Oba Akeem Agbaosi ‘Ewe Obaja 1’, ya halarta tare da rakiyar fitattun mutanen da suka hada da Dokta Dayo Banjo “Basegun” na kasar Agudaland da Oloriodo na kasar Cif Kunle Familola.

Majiyoyi da dama sun ce, bayan yaye daliban daga baya sun shirya addu’ar nuna godiya ga Allah kan karamcin miloniyan, inda shi ma ya halarta.

Miloniyan ya rike kyandir kuma ya shiga tsakanin kyandir-kyandir da aka kunna musu wuta tare da rike guda a hannunsa, inda faston cocin ya fesa masa turare a jiki don sanya masa albarka a yayin addu’ar nuna godiyar.

Majiyoyin sun ce a daidai lokacin da faston yake fesa masa turaren ne, wuta ta kama jikin marigayin inda ya kuna a sassan jikinsa, kuma bayan kwana biyu da kai shi asibiti ne ya ce ga garinku nan.

Mahukuntan Cocin CCC, sun dora alhakin rasuwar Mista Kayode Badru, kan “wuce gona da iri wajen amfani da turare yayin aikin bauta.”

Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce a kafofin sadarwar zamani, inda wadansu ’yan Najeriya suka rika fadin mabambantan ra’ayoyi kan abin da ya faru.

Daya daga cikin dangin marigayin ya shaida manema labarai cewa suna zargin akwai manakisa game da mutuwar dan uwan nasu.

“Lokacin da yake durkushe, sai faston ya fara fesa masa turare a jiki yana rike da kyandir a hannunwansa, yayin da dattawa bakwai ke kewaye da shi.

“Cikin mintuna kadan, sai wuta ta kama jikinsa, saboda kusancinsa da kyandir din da kuma karfin turaren.

“An kai shi wani asibiti a Gbagada, inda ya cika. Sai dai kafin ya rasu ya ce min, dan uwana na ji murya tana ce min, ‘Ta haka ne za ka kawo karshen rayuwarka,’ kuma nan take na yi kokarin gano abin da hakan ke nufi, abin da kawai na ji shi ne kara, kuma ina jin zafi wuta tana kona ni,” inji dan uwan.

Ya ce dan uwansa ya gaya masa cewa hadarin ba na Allah da Annabi ba ne, kuma idan ya mutu ta wannan hanya, mutuwarsa za ta dawo ta dauki fansa.

Ya ce faston da ke jagoranci a lokacin mai suna Felix Alebiosu ya gudu nan take, kuma an sanar da aukuwar hadarin ga ’yan sandan yankin Panti.

“Mun je mun kama mahaifinsa, bayan awanni sai ya bayyana sai aka saki mahaifin washegari, amma shi (Felix) ya shiga hannun ’yan sanda ne ba tare da nuna nadama ba.

“Biyu daga cikin dattawan suna tsare a hannun ’yan sanda, yayin da sauran suka gudu. Biyun ma suna magana ne rambatsau, kamar an yi musu baki,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Ya kamata mutane su rika taka-tsantsan kafin su je kowane coci don yin bauta. Kuma na lura ’yan sanda a Panti ba su daukar matsalar da muhimmanci, suna ba faston kula irin ta manyan mutane, kuma dan uwana ya gaya min akwai batun kudi a tsakaninsu da Fasto Felix, akwai wani abu a boye.”

Sanawar da cocin ya fitar a ranar Asabar da ta gabata, ta ce, ya kamata ne a ce faston ya kara ruwa a cikin turaren tsarkin da za a yi amfani da shi, ko ya fesa shi kadan-kadan ko ya sanya ruwa ga kyandir din da aka kunna.

Sanarwar ta ce, fesa turaren da ba a sanya masa ruwa ba, ya keta dokar fesa turare na cocin.

“Sakamakon yawan wuce ka’ida wajen amfani da turare yayin sanya albarka a cikin cocin, Mai Girma (babban limamin cocin) yana ganin na da muhimmanci a yi gyara.

“Ya bayyana cewa duk wani turare da ake son fesawa ko watsa shi tare da kyandirin da aka kunna, tilas ne a gauraya shi da ruwa,” inji sanarwar.

Ta kuma ce, “Fesa turaren da ba a gauraya da ruwa don sanya albarka ba ya saba wa doka in aka hada shi da kyandir din da aka kunna, kuma hakan wata muhimmiyar al’ada ce ba wai ta samo asali ne daga ginshikan cocin Celestial Church of Christ ba.

“Dokar amfani da Turaren Albarka a tsakanin kyandir-kyandir da aka kunna da faston da ya assasa cocin, SBJ Oshoffa ita ce a gauraya shi da ruwa. Lokaci ya yi da za mu yi taka-tsantsan don ci gaban cocin Celestial Church of Christ.

“Muna bayar da shawarar kowa ya bi wannan umarni, duk wani fasto ko mamba da ya karya wannan umarni shi za a dora wa alhakin duk wata barna da ta biyo baya,” inji sanarwar.

Ta kara da cewa Shugaban Cocin, Emmanuel Oshoffa, ya riga ya umarci majalisar fastocin cocin su aiwatar da wannan tsari don rigakafin irin wannan wuce gona-da-iri a nan gaba.

“Faston ya kuma umarci majalisar fastocin ta fito da wani rubutaccen tsari da zai kawar da duk wasu sababbin bidi’o’i da aka sanya a cikin ginshikan cocin domin tsare koyarwar cocin kamar yadda ruhi mai tsarki ya umarci faston da ya kafa cocin,” inji sanarwar.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC