Yadda fataken bindigogi ke shigo da makamai Najeriya

Ana shigo da bindigogi a kan jakuna da raquma ta varauniyar hanya Najeriya tana tsaka-mai-wuya game da bala’in da bindigogi da miyagun makamai suke haddasawa yayin da miliyoyin manya da kananan makamai suke sulalowa kasar nan, inda miyagun kungiyoyi ke amfani da su wajen aikata laifuffuka. Fadin kasar da daruruwan kan iyakokin da babu masu […]

Yadda fataken bindigogi ke shigo da makamai Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari

  • Ana shigo da bindigogi a kan jakuna da raquma ta varauniyar hanya

Najeriya tana tsaka-mai-wuya game da bala’in da bindigogi da miyagun makamai suke haddasawa yayin da miliyoyin manya da kananan makamai suke sulalowa kasar nan, inda miyagun kungiyoyi ke amfani da su wajen aikata laifuffuka.

Fadin kasar da daruruwan kan iyakokin da babu masu tsaronsu tare da karancin jami’ai da kusan dukkan kafofin tsaron kasar nan ke fama da shi sun kasance silar da masu fataucin makamai ke amfani da su wajen shigo da su cikin kasar nan, inda suke sayar da su a farashin da bai taka kara ya karya ba kuma kasar ke dandana kudarta saboda hakan.

Rikice-rikicen da ke faruwa a kasashen Libya da Sudan ta Kudu da sauran kasashen Afirka Kudu da Sahara sun taimaka sosai wajen yawaitar yaduwar miyagun makamai da cikin sauki ke karewa a hannun masu tayar da tarzoma da ’yan bindiga da barayin mutane da sauran miyagun mutane.

Masana harkar tsaro sun yi amanna cewa yawaitar haramtattun makamai da ke yawo a hannun jama’a  ne ummul haba’isin rashin tsaron da ake fama da shi a halin yanzu.

“Yadda miyagu ke shigo da makamai cikin kasar nan, yana da alaka kai-tsaye da matsalolin tabarbarewar tsaro da muke kokarin shawo kansa a Najeriya a halin yanzu,” inji Salihu Abubakar, wani tsohon jami’in sojan Najeriya.

“Rashin doka da oda a Libya da Sudan da kuma Afirka ta Tsakiya ya haifar da faduwar farashin makaman, za ka iya sayen bindiga kirar AK47 a kankanen farashin da bai wuce Naira dubu 100 ba ko kasa da haka a iyakokin kasar nan.

“Miyagu na amfani da rakuma da jakuna wajen fataucin bindigogi ta haramtattun hanyoyi. Kada ka manta, muna da ’yan maza-wuka da suke sayen makaman kai- tsaye kamar mayakan Boko Haram da ’yan bindiga da barayin mutane da masu fadan kabilanci,” inji jami’in.

Kolo Mala, mazaunin Ngala a Arewacin Jihar Borno, ya ce masu fataucin bindigogin na yin bad-da-kama cewa su ’yan kasuwar yankin ne, inda suke boye bindigogi da albarusai cikin kayan da ake dauka a kan dabbobi kuma sukan ratsa ta kananan hanyoyi domin shigo da su Najeriya ga masu bukatar saya.

“Yana da mataukar wahala ka iya bankado masu harkar, sakamakon dabarun da suke yi wajen aika-aikarsu,” inji Mala.

“Kuma idan ka dubi irin makaman da Boko Haram da kuma wadansu ’yan bindiga ke amfani da su, tabbas za ka ce sun samo su ne bayan da suka yi nasarar fatattakar sansanonin jami’an tsaro; sai dai wasu daga cikinsu kuma sayensu suke yi ta amfani da kan iyakokin kasar da ke tamkar rariya; kana ma iya ganin rubutun Larabci ko na harshen Faransanci a jikin wasu daga cikin makaman da jami’an tsaro suka kwato daga hannun miyagun,” inji shi.

‘Makaman da ke hannun mutane sun dara wadanda suke hannun jami’an tsaro’

Cikin wata takarda kan Dabarun Tsaron Kasa da Ofishin Mai bai Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), ya wallafa a watan Disamban bara, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da akwai kananan bindigogi fiye da miliyan daya da suke yawo a cikin kasar nan.

Sai dai masana sun yi watsi da alkaluman da Ofishin NSA din ya fitar, inda suka ce sun yi kadan nesa ba kusa ba, yayin da wadansu daga cikinsu ke cewa ire-iren wadannan makamai sun kai daruruwan miliyoyi a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba.

Wani masanin dabarun tsaron ma ya yi ikirarin cewa yawan makaman da ke hannun daidaikun jama’a, sun dara wadanda ke hannun daukacin ma’aikatan tsaron kasar nan.

A wata hira da Aminiya, Kyaftin Sadeek Garba (mai ritaya), wanda kwararre ne kan kananan makamai, ya yi watsi da alkaluman kananan makamai miliyan daya da Mai ba Shawara kan Tsaron Kasa, ya yi ikirari.

Ya nuna shakku kan ko ofishin ya gudanar da wani kwakkwaran bincike kan kananan makaman wajen fito da alkaluman cewa ba su wuce miliyan daya ba.

Ya ce lura da bayanan da Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya kan Zaman Lafiya da kuma Kwance Damara (UNREC), wadda kuma ita ce cibiyar da ofishin bayar da shawara kan tsaron kasar ya dogara wajen fitar da wadannan alkaluman nasa, wadda ta cewa kashi 70 cikin 100 na yawan makaman da ke yawo ba bisa ka’ida ba miliyan 500 a yammacin Afirka suna cikin Najeriya ne. Wanda hakan ke nufin cikin makaman miliyan 500 akalla akwai miliyan 350 a Najeriya.

Koda yake alkaluman nasa kan kananan makamai a yankin sun bambanta, Babban Daraktan Gudanarwa na Kungiyar Sa ido kan Ayyukan ’Yan Majalisa (CISLAC), Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani, ya amince cewa kashi 70 cikin 100 na makaman da ke a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba a yammacin Afirka suna nan Najeriya ne.

Ya ce bisa bayanan da ke kasa, kan kananan makaman sun nuna cewa cikin miliyan 640 da ke yawo a duniya baki daya, an kiyasta miliyan 100 na nan a Nahiyar Afirka ce, kimanin miliyan 30 na yankin Afirka Kudu da Sahara, yayin da miliyan takwas suke a Yammacin Afirka.

“Kashi 70 cikin 100 sun samu shigowa Najeriya. Sannan kashi 59 cikin 100 suna hannun farar hula yayin da kashi 38 cikin suke a hannun jami’an tsaro na gwamnati. Kashi 2.8 na wajen ’yan sanda sai kuma kashi 0.2 suna hannun kunkiyoyi masu daukar makamai.

Kungiyar CISLAC ta tabbatar da kiyasinta ne a kan bayanin da ke kunshe a wani kundi na ‘Kididdiga a kan kananan makamai da kuma barazanar tsaro a Najeriya.’ wanda mukala ce ta kasa da kasa ta Cibiyar Tarihi da Al’adu da aka wallafa a shafin Intanet na www.arcjournals.org

Yadda makaman suka samu shigowa Najeriya

Najeriya tana da murabba’in kasa da ya kai kimanin kilomita dubu 923 da 768, wanda hakan ya sanya ta kasance kasa ta 32 a kasashen da suka fi girma a duniya.

Kasar tana da kan iyakokin da tsawonsu ya kai kilomita 4,047 da sauran kasashen da suke kewaye da ita.

Ta bangaren kasar Benin akwai kilomita 773 sai ta bangaren Nijar akwai 1,497 sai ta bangaren kasar Chadi akwai kilomita 87 sai kuma ta bangaren kasar Kamaru inda take da kilomita 1,690. Sannan akwai kilomita 853 ta bangaren da ya shafi ruwa.

Tun a shekarar 2017 akwai barauniyar hanya ta shigowa Najeriya da ta kai guda 1,400 wanda wannan adadi ya zarta hanyoyin halal da ake da su na shigowa kasar nana da 1,316.

Jihar Ogun kadai tana da barauniyar hanya ta shigowa kasar nan da suka kai 83 yayin da ita Jihar Adamawa ke da 80.

Hanyoyin kan iyaka wadanda gwamnati ta yarda da su 84 suna da tsawon kilomita 4,047.

Domin a samu tsare kan iyakokin kasar nan, Hukumar Kwastam ta Kasa ta raba manyan ofisoshi na yankuna zuwa hudu inda a karkasshinsu aka samar da manyan ofisoshi 25. Haka wannan hukuma tana da ma’aikatan da suka kai 17,000 duk kuwa da yake Shugaban Hukumar ta Kana, Kanar Hameed Ali ya fada a ’yan kwanakin nan cewa har yanzu ba su da isassun ma’aikata, wadanda za su iya ba da tsaro a kan iyakokin kasar nan.

A daya bangaren kuwa Hukumar Shigi da Fici ta Kasa tana da yawan jami’ai 25 da 303 da kuma ofisoshi a yankuna takwas da kuma manyan ofisoshi a jihohi 36.

Wannan kari ne a kan Babban Ofishin Hukumar da ke Gwagwalada a Birnin Taryya Abuja da kuma ofishinsu da ke Apapa da ofishinsu da ke Seme a Badagry, da wanda ke Onne bakin ruwa da kuma ofisoshin kan iyaka a jihohin Ribas da Legas.

A cikin watan Agusta bara,  jami’an Hukumar Kwastam da na Hukumar Shigi da Fici da hadin kwiwar sauran jami’an tsaro sun kaddamar da wani shiri mai taken “Shara” inda hakan ya kai ga rufe dukkan kan iyakokin kasar in ban da na ruwa.

‘Ba wanda zai iya tantance hakikanin yawan miyagun makamai a Najeriya’

Wani Birgediya Janar mai ritaya kuma shugaban wata Cibiyar Nazari da Ilimi mai suna WISER a takaice, Saleh Bala, ya ce makaman da ake batu a kansu, ba abu ne mai yiwuwa a iya tantance hakikanin yawansu ba, sai dai ya yadda cewa batun yawan kananan makaman ya kai “matakin da za a kira shi bala’i.”

“Lokacin da ka yi batun haramtattun makamai, ke nan kana batun wadanda ba su da rajista kuma ba a san da zamansu ba, wanda ba a iya sanin inda suke don haka sai dai ka yi ta hasashe kawai.

“Ya kamata mu tambayi masu wannan hasashe, yaya suka samo alkaluman? Galibin makaman suna hannun daidaku da kungiyoyi daban-daban tun gabanin samun ’yancin kan kasar nan, sakamakon haka wannan ba sabon al’amari ba ne.

“An yi zargin tashe-tashen hankali a yankin Neja-Delta da kuma rikicin Libya da zama ummul haba’isin yaduwar haramtattun makamai a Najeriya.

“A wannan kasar akwai batun haramtattun bindigogin da ke gogayya da halattattun bindigogi; kuma a fili yake cewa haramtattun sun dara wa halattattun yawa a kasar nan.

“Yawan zaratan sojijin kasar baki daya bai wuce dubu 400 ba; akwai kuma ’yan sanda dubu 400 a daya bangaren, yayin da sauran jami’an tsaron har ma da masu leken asiri dukkansu ba su wuce dubu 350 ba.

“Mu kaddara kowannensu yana da makami a hannunsa, za ka iya kiyasta ke nan muna da halattattun bindigogi miliyan 1.2. Idan ka hada wadannan alkaluman da yawan makaman da ake yawo da su ba bisa ka’ida ba, kuma ma mu kaddara yawan ’yan Boko Haram ya kai kimanin dubu 200 zuwa 300 (bisa kiyasin alkaluman leken asiri) to a gaskiya wannan babbar matsala ce.

“Kada ka manta cewa ba kowane ma’aikacin tsaro ne ke da bindiga ba, don haka lura da wadannan alkaluman za ka gane cewa yawan halattattun makaman da ake da su bai kai yawan wadanda suke haramtattun ba; ka ma hada da wadanda aka ajiye a rumbun adana makamai da haramtattun wadanda su ma babu wasu bayanai game da su,” inji Janar din mai ritaya.