Yadda fatalwa ke daukar hankalin masu yawon shakatawa a tashar jirgin kasa

An rufe tashar jirgin kasa ta Begunkodar a kasar Indiya tsawon shekara 42 saboda tsoron fatalwa, al’amarin da ya mayar da wajen wurin yawon shakatawa. Wannan tashar jirgin kasa,  wadda ke tsakanin Jhalda da Kotshila a karkashin titin taragon yankin gabashin Indiya, ya dauki hankalin dimbin al’umma da ke kai ziyara don su gane wa […]

Yadda fatalwa ke daukar hankalin masu yawon shakatawa a tashar jirgin kasa

An rufe tashar jirgin kasa ta Begunkodar a kasar Indiya tsawon shekara 42 saboda tsoron fatalwa, al’amarin da ya mayar da wajen wurin yawon shakatawa.

Wannan tashar jirgin kasa,  wadda ke tsakanin Jhalda da Kotshila a karkashin titin taragon yankin gabashin Indiya, ya dauki hankalin dimbin al’umma da ke kai ziyara don su gane wa idanunsu fatalwa sanye da fararen kaya tana baza gashi buya-buya. An ce ana  da tabbacin cewa fatalwar na fitowa sau daya kowane yammaci.

Hukumomi sun ce tashar jirgin kasan an rufe ta ne tun a shekarar 1967, bayan da aka yi mata lakabin “mazaunin fatalwa” jim kadan bayan da wani ma’aikacin jirgin kasa ya mutu lokacin da yake bakin aiki.

Labarin da ake bazawa shi ne, jami’in ya mutu ne bayan da ya ga “inuwar fatalwar sanye da fararen tufafi, tana tafiya a kan tititin tarragon jirgin cikin dare.”

Al’amarin ya haifar da tsoro a tsakanin ma’aikatan tashar jirgin kasa, har ta kai ga babu wanda yake so a tura shi can. Kwatsam sai aka rufe tashar.

Rahotanni sun nuna cewa a shekarun 1960 Lachan Kumari, sarauniyar kabilar Santal ta bayaar da kyautar babban fili don fadada tashar jirgin kasa don ci gaban al’ummarta.

Ba da dadewa ba aka fara aikin fadada wurin, amma cikin kankanen lokaci sai sarauniyar ta mutu, don haka mazaunan kauyen suka yanke cewa ftalwar da ake gani ta sarauniyar ce.

Wannnan tasha ta kasance a kulle sama da shekara 40, har sai da ’yar majalisa mai wkailtar Trinamool Mamata Banerjee Trinamool ta zama babbar ministan sufurin jiragen kasa ta tarayya a shekarar 2009, sai ta sanya aka bude..

A halin yanzu dai tsoron fatalwa ya gushe., domin mutane sun dauki labarin tamkar “shaci fadi ne.”

“Xaukacin maganar da ake yi kan fatalwa shirme ne, don ban taba ganin wani abu ba tun da aka tura ni aiki can. Sai dai kawai tashar na daukar hankali dimbin mutane, wadanda ke zuwa don su ga “fatalwa,”  kamar yadda wani mazaunin kauyen Bhola Mahato ya fada wa jaridar Gulf News.

Ya ce wurin ya zama wajen dandazon ’yan yawon shakatawa da ke son zuwa don su ga “fatalwa da yawa.”

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu