Yadda fitattun sinimomin Kano suka zama kufai

A da muna ganin alkalai, masu sarautun gargajiya kai har da malamn addini suna zuwa wurin.

Yadda fitattun sinimomin Kano suka zama kufai

Sinima ko gidan kallo ne wanda a da aka sani a matsayin wuri na gudanar da abubuwa da dama musamamn abin da ya shafi nishadantar da al’umma daga kowane bangare amma a yanzu sun tasar wa zama kufai.

Binciken Aminiya ya gano cewa kadan din da suka rage suna gudanar da aiki ne a wahalce kasancewar babu ciniki sosai sakamakon samun finafinai a wayoyin hannu.

Haka kuma ko irn yanayin da ake zama a yi kallon a baya yanzu yana bacewa.

Aminiya ta gano cewa ’yan kadan din sinimomin da suka rage ana amfani da su yanzu duk sun tsufa, kuma babu tsafta kuma ba su samun kulawar da ta kamata.

Tarihi ya nuna cewa sinima ta farko da aka fara kafawa a Arewacin Najeriya an kafa ta ce a 1937, wanda wani dan kasar Lebanon ya yi aikinta mai suna Red Cinema a mahadar Titin Sabon Gari.

Daga baya an samu wasu sinimomin da suka hada da Elduniya wanda aka bude a 195,1 sai dai bayan da ya yi gobara an sake gina shi a shekarar.

Sai siniman Palace wanda aka bude a ranar 2 ga watan Yulin 1952. Haka kuma akwai Queens Theatre da Orion da Eldorado da Wapa wanda aka sa masa sunan wurin da aka bude shi. Sai kuma sinimar Marhaba.

A shekarun 1930 da 1940 da 1950 sinimomin da aka bude a wancan lokaci mallakar wasu Amurkawa da Turawan Ingila ne.

A shekarun 1950 sai wadannan sinimomi suka fara nuna finafinan Indiya da na Masar.

A tsakiyar 1960 kuma sai aka daina kallon finafinan Masar aka koma kallon finafinan Indiya wadanda suka shahara musamman a wannan bangare na Arewa.

Duk da cewa a wancan lokaci rashin isassun mabiya ya janyo ba a amfani da finafinansu.

Binciken da aka gudanar a 1990 ya nuna cewa ana nuna finafinan Indiya sau biyar a mako, rana daya kuma ana nuna fim din Amurka sannan wata ranar ana nuna fim din kasar Hong Kong.

Ana nuna finafinan Afirka kadan-kadan a wadannan sinimomi sai kuma finafinan Yarbawa wanda kuma aka rika nuna su a wuraren da ba cikin sinimomin ba.

An kafa Sinimar Marhaba a farkon 1980 sinimar da za ta zama babba a tarihin Jihar Kano.

A yau ginin ya zama kamar gona, wanda kuma a yanzu ke kusa da manyan ginegine da kasuwa a gefensa.

Babu wanda yake iya gane shi a yanzu sai wadanda suka san wurin tun a baya.

Da yake bayani a kan tsohuwar sinimar wacce ta shahara a shekarun 1980, Sa’idu Mustapha ya ce siniman ya shahara inda kuma ya agaza wa mutane da yawa.

“Marhaba! Har yanzu ina iya tunawa shi ya sa ma a yanzu ka same ni a wannan wuri. Duk inda na je kafin in tafi gida sai na zo nan wurin domin mu hadu da abokai.

“Nan ya zama mana gida na biyu. A da ana gudanar da hada-hada sosai, amma yanzu kalli yadda wurin ya koma.

“Bari in fada muku a da ko da gawa ka dauko za ka kai makabarta, to, dole sai ka yi hakuri saboda yawan jama’a ba za ka iya kiyasta yawan mutanen da suke zirga-zirga a wurin nan ba.

“ Kasuwanci yana bunkasa a lokacin musamman masu sayar da kayan makulashe da abin sha.

“Hakan ne ma ya sa ake samun makanike a wannan wuri. Amma abin bakin ciki wuri ya zama kufai,” in ji shi.

An rufe siniman Marhaba shekara 10 da suka gabata a yanzu ma an sayar da wajen ga wani wanda kuma ba lallai ne yana da sha’awar farfado da shi ba.

Ahmad Muntari Sabo ya bayyana cewa siniman wuri ne da ya hada kowa har ma da mutanen da suke fadi-a-ji a cikin al’umma.

Ya ce, “Sinima wuri ne da mutum ke zuwa don debe kewa. Lokacin da muke yara muna ganin manyan mutane.

“Muna ganin alkalai, masu sarautun gargajiya kai har da malamn addini suna zuwa wurin.

“Haka za ka ga mutanen gida guda sun zo bisa jagorancin babansu su yi kallon fim abinsu.

“Mun bar komai a baya. Mun yi watsi da al’adunmu muna kwaikwayon Turawa.”

Shi ma da yake bayani, Hamisu Baba Agadasawa ya ce, “Sinima wata cibiya ce da za ka je ka koyi wasu al’adun mutanen da suke a wajen muhallinka ba wai kawai wurin nishadi ba ne har ma da koyo.”

A da mutanen da ke zuwa sinima manya ne domin cikin sauki za su gano abin da ake yi, su kuma koyi wani abu daga nan.

Amma yanzu sai dai ka ga yara kananan suna zuwa wurin don kallon kwallon kafa.

Yayin da wasu sinimomin aka rufe su kamar na Marhaba sauran kamar su Plaza an shafe tarihinsu sakamakon an rushe ginin an gina kasuwar zamani a wurin.

“Su kuma irin su Eldrado da Queens wadanda suke a Sabon Gari a Karamar Hukumar Fagge suna ci gaba da rarrafawa don ganin sun rike kansu saboda rashin ciniki.

An gano cewa abin da ke rike sinimomin a yanzu shi ne yadda mutane ke zuwa kallon kwallon kafa don kusan kullum ana a mako.

Sai dai har yanzu ba su samun mutane da yawa da suke zuwa don kallo a sinimomin.

Manajan Siniman Eldorado ya ce “Abin da muke nunawa a yanzu shi ne kwallon kafa. Babu kasuwa. Kamar yadda kuka sani abubuwa duk sun canza. Ina iya tuna yadda lamarin yake a baya.”

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa