Yadda fiye da mutum 50 suka mutu a maulidi a Afghanistan
An kashe mutum fiye da 50 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a dakin taron da aka gudanar da taron Maulidi a Kabul, Babban Birnin Afghanistan. Jami’ai sun ce akalla mutum 83 ne suka jikkata lokacin da malaman addinin Musulunci suka taru a babban dakin da ke lardin PD15 domin tunawa da […]
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani
An kashe mutum fiye da 50 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a dakin taron da aka gudanar da taron Maulidi a Kabul, Babban Birnin Afghanistan.
Jami’ai sun ce akalla mutum 83 ne suka jikkata lokacin da malaman addinin Musulunci suka taru a babban dakin da ke lardin PD15 domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW).
Harin shi ne mafi muni da aka kai Kabul a watannin baya bayan nan kamar yadda BBC ta ruwaito.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar IS ta sha daukar alhakin hare-haren da aka kai a birnin a baya.
Hare-haren da kungiyar Taliban ke yawan kai wa sun sa an kara tsaurara matakan tsaro, sai dai a wannan lokaci ta nesanta kanta da harin.
Akalla mutum 1,000 ne a dakin taron lokacin da aka kai harin kamar yadda jaridar Tolo ta bayyana.
Ita ma 1TB News ta ambato jami’an kula da lafiya na cewa mutum 24 sun ji mummunan rauni.
Wani manajan da ke kula da dakin taron ya ce dan kunar bakin waken ya tashi bam din da ke jikinsa a tsakiyar masu bikin maulidin.
Shugaban Kasar Afghanistan, Ashraf Ghani, ya yi Allah wadai da harin da ya bayyana da laifin da ba za a taba yafe wa ba, ya kuma ayyana zaman makoki a fadin kasar.