Yadda garin Biu ya shahara a sana’ar karago

Garin Biu da ke Jihar Borno garin ne da ya shahara a sana’ar karago ko kuli a shiyyar Arewa maso Gabas da wasu jihohin kasar nan saboda dadi da yadda mutanen garin suke inganta shi. Wakilin Aminiya da ya ziyarci garin Biu, ya zanta da wadansu masu sana’ar karagon dan jin yadda suke kasuwancinsu. Zainab […]

Yadda garin Biu ya shahara a sana’ar karago

Qaragon garin Biu a cikin leda

Garin Biu da ke Jihar Borno garin ne da ya shahara a sana’ar karago ko kuli a shiyyar Arewa maso Gabas da wasu jihohin kasar nan saboda dadi da yadda mutanen garin suke inganta shi. Wakilin Aminiya da ya ziyarci garin Biu, ya zanta da wadansu masu sana’ar karagon dan jin yadda suke kasuwancinsu.

Zainab Idris mai shekara 14 ta ce tsawon shekara biyu ke da ta fara sayar da karago, inda ta ce a kullum tana sayar da na Naira dubu biyar, idan ta sayar kuma tana samun ribar Naira 800.

Zainab Idris, ta ce ba ta yin makarantar boko sai ta Islamiyya saboda rashin kudi, kuma  ribar da suke samu a sana’ar karagon da ita ce suke sayen kayan daki suna tarawa kafin lokacin aurensu saboda idan lokacin aurensu ya zo kada asirinsu ya tonu.

Ta ce, tana so a ce sun samu dama na yin wani abu muhimmi a rayuwa da za su yi alfahari da shi amma saboda kudin bai taruwa kayan daki kawai suke saye, sauran su biya bukatun yau da kullum.

A cewarta karagon na mahaifiyarta ce kuma sun fara ne tun ba su da jari lokacin suna karbar gyadar bashi har ta kai yanzu suna da jarin da suke sarrafawa.

Ita ma A’isha Ibrahim mai shekara 15 cewa ta yi shekara uku ke nan da fara  sana’ar amma ta ga a gidansu ana yi kuma karagon ya yi suna domin daga garuruwa ana zuwa garinsu sayensa.

A’isha Ibrahim, ta ce da jarin mudu uku na gyada suka fara na Naira 1,900.

Ta ce ba ta yin makarantar boko, saboda rashin kudi, sana’ar kawai take yi ribar da suke samu da shi suke ciyar da gidansu don rufa wa kansu asiri.

Daga nan sai ta yi kira ga ’yan siyasa ko masu hannu da shuni su taimaka wa masu kananan sana’o’i irin nasu wajen kara musu jari don habaka sana’ar tasu.