Yadda gawa ta farfado bayan kwana 11

Wata mata ’yar kasar Brazil da aka yi wa jana’iza aka binneta ta farfado bayan kwana 11, inda aka haka kabarinta aka fito da ita, bayan da makwaftan makabarta suka tabbatar da jin karar matsanancin motsi a wani kabari. ’Yan uwan matar da ta mutu a kasar Brazil sun yi ikrarin cewa an binne ta […]

Yadda gawa ta farfado bayan kwana 11

Wata mata ’yar kasar Brazil da aka yi wa jana’iza aka binneta ta farfado bayan kwana 11, inda aka haka kabarinta aka fito da ita, bayan da makwaftan makabarta suka tabbatar da jin karar matsanancin motsi a wani kabari.

’Yan uwan matar da ta mutu a kasar Brazil sun yi ikrarin cewa an binne ta da rai, al’amarin da ya sanya ta yi ta fafutikar fitowa daga akwatin gawa. Kuma makwaftan makabartar sun ce sun ji matsanhancin motsi daga makabrtar.

Rosangela Almeida dos Santos, mai shekara 37, bayan an tabbatar da mutuwarta sai aka yi mata jana’iza a garin Riachao das Nebes a Arewa maso Gabashin Brazil. Da aka samun rahoton abin da  ke aukuwa a makabartar sai ’yan uwanta suka tono ta daga kabari, kamar yadda shafin sadarwar yada labarai a kasar Brazil na GI ya ruwaito.

Hoton bidiyo ya nuna yadda aka bude akwatin gawa, inda mutane suka taru suka ciccibo ta bayan sun bude.

’Yan uwan sun yi ikrarin cewa lokacin da aka tono ta, akwai alamun da suka nuna ta yi matukar kokarin fitowa, wato irin raunukan da ta ji a hannunta da goshinta, wadanda aka tabbatar lokacin da aka binne ta babu su a tare da ita.

Mahaifiyarta ta bayyana wa shafin sadarwar cewa an kwance kusoshin da ke rike da akwatin gawar tamkar dai yadda alamu suka nuna kokarinta na ficewa daga ciki.

Matar dai mai shekaru 37 an tabbatar da mutuwarta ne rnar 28 ga Janairun bana, sanadiyyar farmakin bugun zuciya.