Yadda gizo-gizo a jana’izar Sarauniyar Ingila ya tayar da kura
Ganin wani gizo-gizo a kan akwatin gawar Sarauniyar Ingila ana tsaka da yi mata addu’oi ya tayar da kura.
Ganin wani gizo-gizo a kan akwatin gawar Sarauniyar Ingila ana tsaka da yi mata addu’oi ya tayar da kura.
Gizo-gizon ya bayyana a kan akwatin gawar marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth II ne a cikin jerin kayan kawanta na sarautanta da aka ajiye a kan akwatin.
- Me ya sa akuya ta ‘jagoranci’ faretin nada Sarki Charles sarautar Ingila?
- Sarkin Kano ya je ta’aziyyar Sarauniyar Ingila
Kyamarar daukar hoto ta talbijin ce ta fara dauko hoton gizo-gizon a kan akwatin gawar, inda aka ajiye kambinta da sandar mulki da aka yiwa ado da lu’lu da yakuti sai kuma wasu furanni na ado.
Kusa da furannin ne, a jikin wata ’yar takarda da magajin sarauniyar, Sarki Charles III ya yi rubutu, gizo-gizon ya hau yana kuma yawo, kyamarar kuma ta watsa wa duniya kai-tsaye.
Hoton wannan kwaro kan akwatin gawar ya janyo ce-ce-ku-ce a kafofin yada labarai musamman shafukan sada zumunta a ciki da wajen kasar.
Yayin da wasu ke cewa soyayyar sarauniyar ga dabbobi ce ta sa wannan kwaron ya zo ta’aziya, wasu kuma na cewa sakacin masu shirin bikin binne ta ne da ba su sa an yi wa wurin feshi ba.
Cocin Westminister mai tsohon tarihi, inda aka ajiye akwatin gawar sarauniyar domin yi mata addu’oi na al’ada, a nan ne dubban mutane suka je domin kallon gawar na karshe wanda gidajen talbijin suka watsa kai-tsaye.