Yadda gizo-gizo ya tada hankulan jama’a a Texas
Wata kyamarar ’yan sanda ta dauki hoton wani babban kwaro mai siffar gizo-gizo a garin Texas da ke Amurka wanda yake tafiya a hankali yana son ketare hanyar da motoci ke bi. ’Yan sandan yankin Fulshear ne suka yada bidiyon a farkon makon nan wanda ya ta da hankulan jama’ar da suke ganin wannan babban […]
Wata kyamarar ’yan sanda ta dauki hoton wani babban kwaro mai siffar gizo-gizo a garin Texas da ke Amurka wanda yake tafiya a hankali yana son ketare hanyar da motoci ke bi.
’Yan sandan yankin Fulshear ne suka yada bidiyon a farkon makon nan wanda ya ta da hankulan jama’ar da suke ganin wannan babban abin al’ajabi ne da ba a taba ganin irinsa ba.
Gizo-gizon yana kokarin kusantar wani dan sanda ne wanda ke bakin aiki kusa da inda ake dakatar motoci don bincikensu.
Da farko dai bidiyon da ke nuna gizo-gizon na nuna abin kamar ba da gaske ba ne. Daga bisani aka tabbatar da babban kwaron gizo-gizo ne ke yunkurin kusantar motar ’yan sanda.