Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara
Har yanzu ba a san musababbin tashin wutar ba.
Wata gobara da ta tashi ta ƙone kasuwar babura ta Yar-Dole da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Ma’aikatan Hukumar Kashe Gobara na Jihar, sun yi ƙoƙarin kashe wutar wadda ta ɗauki lokaci tana ci.
- Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda
- Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra
Wutar ta fara ci ne da yammacin ranar Asabar, inda ta bar ’yan kasuwa da mazauna yankin cikin firgici yayin da shaguna da rumfuna da dama suka ƙone.
Wasu ganau, sun ce wutar ta bazu da sauri a cikin kasuwar, wacce ta ke wajen sayar da babura da kayan gyaransu a jihar.
Har yanzu ba a san musabbabin wutar ba.
“Ba mu san abin da ya jawo wutar ba. Mun dai ga hayaki daga shagunan babura, amma ma’aikatan kashe gobara na ƙoƙarin kashe ta,” inji wani ɗan kasuwa.
A wajen da abin ya faru, an hangi ’yan kasuwa da masu shaguna suna ƙoƙarin ceto kayayyakinsu, amma ba su yi nasara ba saboda tsananin zafin wutar.
Ma’aikatan gaggawa daga Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara, sun isa wajen jim kaɗan bayan an sanar da tashin wutar.
Sun yi ƙoƙarin kashe wutar da kuma hana ta bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar.