Yadda gobara ta cinye gidan jarumi Aminu Asid
A ranar Lahadin da gabata ce gobara ta tashi a gidan fitaccen jarumi Aminu Ilu Dambazau da ke Kano, inda ta kone dukkan gidan da abin da ke cikinsa kurmus. Wutar ta faru ne da misalin karfe 11 na rana a gidan jarumin da ke Unguwar Shagari Kuarters a birnin Kano. Jarumin, wanda aka fi […]
A ranar Lahadin da gabata ce gobara ta tashi a gidan fitaccen jarumi Aminu Ilu Dambazau da ke Kano, inda ta kone dukkan gidan da abin da ke cikinsa kurmus.
Wutar ta faru ne da misalin karfe 11 na rana a gidan jarumin da ke Unguwar Shagari Kuarters a birnin Kano.
Jarumin, wanda aka fi sani da Aminu Asid, ya shaidawa wa Mujallar Fim cewa, “Abin da na sani shi ne na fito da safe, kuma iyalina sun fita unguwa, akwai wani makwabcinmu da zai tare a gidansa, ta je ta raka su, kawai misalin karfe 11 na rana sai wani makwabcina ya kira ni a waya yana sanar da ni gidana ya kama da wuta in yi sauri in je.”
Aminu ya ce, “Ina zuwa kusa da gidan sai kawai na ga bakin hayaƙi ya turnuke sararin samaniya, kuma babu wata dama ta shiga gidan domin gaba daya ya kama da wuta. Duk da haka, na yi ta kokarin shiga gidan, amma sai makwabtana suka rike ni, domin tunanina duk wasu kayana da suke da muhimmanci za su kone, amma haka aka rike ni na tsaya ina kallon kudirar Ubangiji.”
Ya ce “Wutar ta rika ci, babu abin da na iya yi sai kiran sunan Ubangiji, kuma duk da jami’an kashe gobara mota shida sun zo wajen, amma wutar sai da ta kai har wajen karfe 3 tana ci ba tare da ta mutu ba.”
Dangane da asarar da aka yi a gidan, Aminu ya ce, “Asarar da zan ce ba a yi ba sai ta rai, amma duk wani abu da na mallaka a gidan da ni da iyalaina, babu abin da ya saura, domin kayan da muka fita da shi na sakawa a jikinmu kadai ya saura, duk abin da muka mallaka ni da iyalina duk sun kone, kamar abin da ya shafi takardun makaranta, kayan bukatun gida da duk wani abu da ka sani. Don haka a yanzu da muke hirar nan da kai ni kadai na san abin da nake ji, ba don addu’ar da nake yi ba, ban san yadda zan samu kaina ba.”
’Yan uwa da abokan arziki sun rika tururuwa zuwa gidan domin jajanta masa kan abin da ya faru.
Cikinsu har da Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa ta Najeriya, (MOPPAN).
A cikin wata sanarwa, Sakataren Yada Labarai na Kasa na Kungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya ce, “A madadin Shugaban MOPPAN na Kasa, Dokta Ahmad Muhammad Sarari da dukkan shugabanni a matakin kasa da jihohi da ilahirin mambobin MOPPAN, ina mika sakon jaje ga dan uwanmu Malam Aminu Acid, bisa wannan ibtila’in da ya same shi. Muna yi masa fatar Allah Ta’ala Ya mayar masa da dubun alherin da ya salwanta sakamakon wannan gobara. Haka kuma muna mika jajen ga maidakinsa da ’yan uwansa da iyaye da abokan arziki. Allah Ya kiyaye na gaba, amin.”