Yadda gobara ta hallaka mutum 8 a gidan tsohuwar minista
Mutum takwas ’yan uwan juna sun rasu a gobarar da ta rutsa da gidan tsohuwar Minista a Ma’aikatar Ilimi, Hajiya Bintu Ibrahim Musa da ke Abuja da tsakar dare ranar Litinin.Marigayan da sauran jama’a suna barci ne lokacin da gobarar ta tashi a gidan da ke yanki na takwas (Area 8) a Garki, Abuja.daya daga […]
????????????????????????????????????

Mutum takwas ’yan uwan juna sun rasu a gobarar da ta rutsa da gidan tsohuwar Minista a Ma’aikatar Ilimi, Hajiya Bintu Ibrahim Musa da ke Abuja da tsakar dare ranar Litinin.
Marigayan da sauran jama’a suna barci ne lokacin da gobarar ta tashi a gidan da ke yanki na takwas (Area 8) a Garki, Abuja.
daya daga cikin mutum biyar da suka tsira a hadarin gobarar mai suna Jamila Kasimu, ta shaida wa Aminiya a ranar Talata cewa, suna cikin barci a gidan ne kwatsam hayaki ya turnuke su.
Ta ce wadanda suke gidan, mata ne da yara suna kwance suna barci ne a falon sama na ginin mai hawa biyu lokacin da wutar ta kama da tsakar dare.
Jamila ta kara da cewa, sun rude tare da firgicewa suna ihun neman gudunmawa, suna bubbuga kofofin sauran dakuna domin tayar da wadanda suke barci.
Ta ce tsohuwar ministar ta rasa biyu daga cikin ’ya’yanta mata a gobarar, kuma daya daga cikinsu ta rasu ne tare da ’ya’yanta biyu.
A cewarta, daga cikin mutum takwas din da suka rasu, shida yara ne, maza hudu da ’yan mata biyu.
Jamila ta ce ’yan uwa da aminan iyalin tsohuwar ministar sun je gidan ne saboda bikin auren daya daga cikin ’ya’yan Hajiya Bintu da aka yi a karshen makon da ya shige.
Aminiya ta samu bayanin cewa makwabta sun kai dauki ga wadanda gobarar ta rutsa da su, kuma wasu daga cikinsu sun kubuta ne ta tagogin hawa na biyu na gini sakamakon yadda wutar ta kama gadan-gadan.
Jamila ta kuma ce dukkan wadanda suka rasu a gobarar ba su yi mummunar konewa ba, illa sun rasu ne sakamakon shakar hayaki a lokacin gobarar.
Ta ce ta lura wasu daga cikin yaran suna numfashi lokacin da aka fito da su daga gidan, amma suka cika a asibiti sakamakon shakewar numfashi da hayakin ya haddasa musu.
Jamila ta ce ma’aikatan kwana-kwana sun samu nasarar kashe gobarar cikin daren.
A bayanin da asibitin ya fitar ya ce, Hajiya Binta da wasu ’yan uwanta uku, “Sun galabaita sakamakon shakar hayaki a gobarar da ta auku a gidansu lokacin da suke barci.”
“Ana kula da su kuma suna farfadowa,” inji Dokta Shibahul Hassan, Babban Daraktan Asibitin Dr Hassan’s Hospital, inda aka kwantar da iyalan.
Asibitin ya karbi majinyata hudu a dakin kwantar da marasa lafiya na gaggawa da misalign karfe 3:00 na daren Talata, sai dai Hajiya Bintu wadda ta yi Minista a Ma’aikatar Ilimi a lokacin mulkin Cif Obasanjo tana cikin kaduwar da ba za ta iya magana da manema labarai ba, sakamakon rasa iyalai takwas da ta yi a gobarar.
Asibitin ya tabbatar da cewa an kai gawa takwas daga inda gobarar ta auku a Eriya 8, amma an dauke su a motar daukar marasa lafiya zuwa Asibitin kasa domin yin gwaji a gano abin da ya kashe su.
Wata majiya ta ce gobarar ta auku ne sakamakon tartsatsin wutar daga wutar lantarki.
Lokacin da aka tuntubi Kakakin Hukumar ’Yan Kwana-Kwana ta kasa Mista Obisesan Biodun, ya tabbatar da aukuwar gobarar, wadda ya ce ta halaka mutum takwas, yayin da aka ceto mutum uku aka dauke su zuwa asibiti.
“Mun samu bayanin daga wani mai suna Malam Yusuf cewa gobara ta kama a wani gida, amma kafin mu isa wurin cikin minti 30 da kamawar gobarar, ta yi mummunan barna,” inji shi.
Ya ce hukumar tana gudanar da bincike kan gobarar.