Yadda gobara ta lashe kasuwanni a Jihar Legas

’Yan kasuwar da suka mallaki shaguna a kaswuwar Balogun da ke cikin birnin Ikko da kasuwar Okobaba da ke unguwar Ebute Meta da mutanen yankin Igando da ke cikin Jihar Legas sun ce sun tafka asarar dukiya mai yawa sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwanninsu da gidajensu. Binciken Aminiya ya gano cewa gobarar kasuwar […]

Yadda gobara ta lashe kasuwanni a Jihar Legas

Firefighters spray water on a building as they try to extinguish a fire at the Balogun market in Lagos on January 12, 2015. The popular Balogun market in Lagos, Nigeria’s commercial hub was gutted by fire early this morning leaving property worth thousands of dollars, including local and imported textiles, shoes and household goods consumed […]

’Yan kasuwar da suka mallaki shaguna a kaswuwar Balogun da ke cikin birnin Ikko da kasuwar Okobaba da ke unguwar Ebute Meta da mutanen yankin Igando da ke cikin Jihar Legas sun ce sun tafka asarar dukiya mai yawa sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwanninsu da gidajensu.

Binciken Aminiya ya gano cewa gobarar kasuwar Okobaba ta fara ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Lahadi ita kuwa ta kasuwar Balogun ta tashi ne da misalin karfe 6:00 na safiyar Litinin, sai ta unguwar Igando da ta fara da yammacin Litinin.
Gobarar ta kone gidaje masu yawa da dukiyoyi na miliyoyin naira, amma wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce an samu asarar rayuka hudu a gobarar. Wata ’yar kasuwa mai suna Alaja Abibata Samiyu ta bayyana cewa ta yi asarar shagunanta biyu.
Ta ce: “Na yi asara mai yawan gaske domin shagunana cike da kayayyakin tufafi duk sun kone a kasuwarmu. Gaskiya yanzu ban san yadda zan yi ba domin duk abin da na mallaka ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Sai dai fatan Ubangiji ya mayar mana da abin da muka yi asara,” inji ta.
Ita ma Funmi Amos ta bayyana cewa ta yi asarar dukiyar da ta kai ta miliyan shida, inda ta kara da cewa, “Ni ma ’yar kasuwa ce a kasuwar Balogun ina sayar da takalman mata da jakankuna, amma duk yanzu sun kone sakamakon gobarar da ta tashi. Ban san gobarar ta tashi ba sai da misalin karfe 8:00 na safe.”
Shi ma Alade Raji wanda yake kasuwanci a kasuwar Okobaba ya ce: “Ni ban san gobarar ta tashi ba a kasuwarmu sai da wani makwabcina ya bugo mini waya yana tambayata kan lamari, nan take na bugawa wani abokina da muke kasuwanci tare da shi a kasuwar, sai ya ce mini tun lokacin da ya samu labari yake kiran wayata, amma ta ki shiga, sai na tafi kasuwar cikin gaggawa domin na ga abin da ya faru, ina zuwa sai na tarar shagona ya kone babu abin da ya tsira,” inji shi.
Wata mata da gidanta mai hawa uku ya kone a unguwar Igando mai suna Iya Basirat ta bayyana cewa, “Muna cikin gida sai kawai muka ji makwabtanmu suna ihu suna cewa wuta-wata. Nan da nan muka fito waje, kafin ka ce kwabo wutar ta kama gidanmu gadan-gadan sai ka ce ana zuba mata man fetur. Duk gidan ya kone babu abin da muka tsira da shi.”
Jami’an hukmar kashe gibara na jihar da na tarayya da na hukumar bayar da agajin gaggawa da na kungiyar Red Cross da na Cibil Defence da na kula da gine-gine na jihar da jami’an ’yan sanda da motocin kashe gobara na bankin UBA da kuma na kamfanin gine-gine na Julius Berger sun kai dauki wurin gobarar tare da bayar da gudunmawa.
Daraktan kashe gobara na jihar, Mista Rasak Fadipe ya ce “Mun samu labari ne da misalin karfe 6:00 na safe cewa kasuwar Balogun ta kama da wuta. Muna zuwa muka tarar wutar tana da karfi sosai, nan da nan sai muka karo motoci bakwai daga ofishinmu, amma yayin da suka iso gine-gine uku sun kama da wuta na hudun shi ma har ya kama ci, haka muka yi ta fama har muka kashe wutar,” inji shi.
Shi ma Shugaban hukumar bayar da gajin gaggawa Dokta Abdullahi Bamidele ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce ba a samu jin ciwo ko asarar rayuka ba.
Janar Manaja na hukumar kare muhalli Mista Femi Oke-Osanyintolu ya shaida wa manema Labarai cewa hukumarsa tana ci gaba da nazarin gine-ginen da gobarar ta shafa don tantance matsayinsu.
Sai dai shugabar ’yan kasuwar jihar, Misis Folashade Tinubu-Ojo ta yi alkawari tuntubar gwamnati don ganin ta taimakawa wadanda suka yi asara.