Yadda gobara ta sake tashi a kasuwar Singa

Wannan gobarar ta tashi ne bayan irinta ta tashi ƙasa da makonni biyu a kasuwar.

Yadda gobara ta sake tashi a kasuwar Singa

Gobara ta sake tashi a kasuwar Singa da ke Jihar Kano, kwanaki kaɗan bayan tashin wata gobara a kasuwar.

Gobarar ta lalata shaguna a sashen Gidan Glass da ke kan Ado Bayero Road, kusa da titin Murtala Muhammad Way.

Gobarar ta fara ne da yammacin ranar Asabar, kuma wannan shi ne karo na biyu da gobara ke tashi a kasuwar cikin ƙasa da makonni biyu.

Wani ɗan kasuwa, mai suna Nasir Maharazu, ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 4 na yamma kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto tana ci.

Ya ce har yanzu yana ganin wutar na ci, kuma gaba ɗaya bene biyu ne suka kama da wutar.

Ya kuma ce wannan gobarar ta fi wadda ta faru kwanakin baya muni.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, motar kashe gobara guda ɗaya ce ta isa wajen domin kashe wutar.

Singa ita ce babbar kasuwar sayar da kayayyaki a Jihar Kano da ma Arewa.

Kasuwar ta yi fice wajen sayar da kayan abinci da na masarufi.