Yadda gobarar dare ta kashe uwa da ɗanta a Abuja
Wata uwa tare da ɗanta mai shekara ɗaya da rabi sun rasu a wata gobara da ta tashi da dare a Abuja.
Wata uwa tare da ɗanta mai shekara ɗaya da rabi sun rasu a wata gobara da ta tashi da dare a Abuja.
Matar da ɗan nata sun rasu bayan tashin gobarar gidansu da ke kasuwar kayan kafintoci ta Kugbo, da ke Karamar Hukumar Birnin Abuja.
Shaidu sun ce wutar ta tashi ne a lokacin da Misis Jummai Sunday da ɗan nata suke tsaka da barci ta yi ajalinsu a ranar Laraba.
Sun ce maƙwabta ne suka gano gawarwakin ne a lokacin da ake ƙoƙarin gyara kasuwar bayan jami’an hukumar kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar.
Babban jami’in ’yan sanda na yankin Karu, Lakur Langyi, ya tabbatar da samun rahoton tsuntsaye gawarwakin, waɗanda ya ce sun fara bincike kan lamarin.
Ya ce abin ya faru ne a unguwar da ake kira Bakassi a yankin Kugbo.
Tuni aka yi jana’izar mamatan a yayin da ’yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike a unguwar.