Yadda gurgu mara hannu ke koyar da masu hannu a makaranta *Burinsa ya zama Lauya
Masu iya magana na cewa,“Ba nakasasshe, sai kasasshe!”. A kan haka ne Aminiya ta tattauna da wani matashi, mai suna Muhammad Nura, wanda gurgu ne kuma mara hannaye, da ke zaune a Kaduna. Amma larurorinsa ba su hana shi zama malamin makaranta ba, a bangare guda kuma kwararren mai gyaran babur. Ga yadda hirar ta […]

Masu iya magana na cewa,“Ba nakasasshe, sai kasasshe!”. A kan haka ne Aminiya ta tattauna da wani matashi, mai suna Muhammad Nura, wanda gurgu ne kuma mara hannaye, da ke zaune a Kaduna. Amma larurorinsa ba su hana shi zama malamin makaranta ba, a bangare guda kuma kwararren mai gyaran babur. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ka bayyana mana tarihinka?
Assalamu alaikum, sunana Muhammad Nura Adam, zan kai kamar kimanin shekara 27 da haihuwa. An haife ni ne a wani gari mai suna Maje da ke yankin karamar Hukumar Igabi, a Jihar Kaduna. Dalilin dawowa ta garin Kaduna kuwa shi ne, rasuwar mahaifiyata lokacin ina da shekara uku. Wannan ya sa kakata ta dauko ni muka dawo garin Kaduna da ita. Kamar yadda kake gani, ni gurgu ne,kuma Allah Ubangiji bai ba ni hannaye ba. Har ila yau, na yi karatun addini da na zamani, inda na yi sauka har sau uku, bangaren boko kuma na tsaya ne a matakin sakandare bayan kammala karatuna a makarantar Tunawa da Sardauna wato (Sardauna Memorial College) da ke Kaduna. Kodayake, tun daga gida na fara fuskantar kalubale lokacin da na bayyana sha’awata kan neman ilimi, inda kakata da kanta ta nuna kamar ba zan iya ba da farko. Bugu da kari, ni malami ne a makarantar Markas Alhaji Adam da ke Dutse Road, a unguwar Dosa. Na fara aiki da su ne a farkon wannan shekarar.
Aminiya: Yaya kake rubutu a allo?
Saboda sun san cewa ina da matsala bangaren amfani da allo, ba a ba ni darussan da za su bukaci amfani da shi ba. Inda aka ba ni karantar da Al-kur’ani da Hadisi da Hisnul Muslim, a aji biyu da uku, sai kuma aji biyar. Kuma Alhamdulilahi mu’amalata da dukkannin dalibaina kyakkyawa ce, saboda suna girmamani da daraja ni kamar yadda ya kamata. Duk abin da na umarce su da yi, suna yi. Hakazalika, duk abin da na hane su, suna guje masa. A gaskiya ba na samun wata matsala da dalibaina da ma sauran malaman makarantar baki daya.
Aminiya: Yaya kake gudanar da aikace-aikacen yau da kullum?
Maganar gaskiya babu wata matsala. Misali wanka da wanki da kaina nake yi. Kai hatta janyo ruwa daga rijiya ba na jira sai wani ya yi mini, da kaina nake yi. Hakazalika zuwa makaranta, da kafata nake yi. Kodayake, a wasu lokuta ina hawa babur kafin a hana acaba a garin nan, amma a yanzu yawanci da kafata nake zuwa.
Aminiya: Ya karatunka ya kasance lokacin kana dalibi cikin dalibai masu kafafu da hannaye?
A gaskiya ban fuskanci wata tsangwama daga takwarorina dalibai ba, tun daga kan firamare har sakandare, ba wata matsala, sai dai ma goyon baya da kauna daga ’yan uwana dalibai da kuma malaman da suka koyar da mu a lokacin.
Aminiya: Wane tsawon lokaci ka kwashe wajen koyon rubutu da kafa?
Yana da kyau jama’a su fahimci cewa na fara koyon rubutu da kafa ne tun kafin shigata makaranta. A lokacin nakan samu jarida, na kura idanuna ina nazari da kallon abubuwan da aka rubuta a kowane shafi. Daga nan sai na tanadi abun rubutu da takarda, na yi ta kwatantawa. Wannan ya sa ko da na shiga makaranta ban samu wata matsala ba. Har ya kai ga idan sakamakon jarrabawar darasin koyon rubutu wato (Writing) ya fito, ba na samun kasa da abun da ake bukata dalibi ya samu. Hakazalika, a darasin koyon zane-zane wato (Drawing). Wani abin mamaki ma shi ne, a lokuta da dama idan na kammala nawa a kan lokaci, wasu dalibai masu hannu kan roke ni da na taimake su na zana musu. Kuma nakan taimaka musu duk lokacin da suka bukaci hakan.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka fara koyon sana’a?
Abin da ya ja hankalina na koyi sana’ar gyaran babur shi ne, ba na so na zauna sai wani ya ba ni. Idan na ce haka zan rayu, to fa zuciyata za ta mutu kuma zan kasance cikin damuwa a kodayaushe. Saboda ta hanyar shiga jama’a tare da yin aiki da su kafada da kafada nakan ji kamar ba na fama da wata larura.
Na fara koyon sana’ar gyaran babur a nan kusa da gidanmu a shekarar 2000. Amma daga bisani a shekarar 2009, saboda yadda masu iya magana ke cewa taura biyu ba sa taunuwa a lokaci guda, sai na ajiye aikin domin na fuskanci karatuna sosai. Har ila yau, a shekarar 2010, na koyi gyaran kwamfuta, duka a nan unguwarmu. A fahimta ta bai kamata ka dora wa wani nauyinka ba, kuma hanya daya ta tsira da mutumcina ita ce neman na kaina.
Aminiya: Ka taba samun wani taimako daga wajen gwamnati?
A’a, ban taba samun wani taimako daga gwamnati ba.
Aminiya: Wacce fa’ida ka samu daga sana’arka?
Na samu fa’ida sosai, musamman ma ganin cewa ina ci da sha da kuma da sutura duka albarkacin wannan sana’ar. Ina kuma taimaka wa kakata da sauran ’yan uwana. Wannan kadan ne daga ciki.
Aminiya: Yaya mu’amalarka da masu kawo maka gyara take?
A gaskiya duk wanda na taba wa aiki yakan nuna gamsuwar da aikina. A wasu lokuta idan aka kawo aiki kuma aka yi rashin sa’a ba na wajen aiki, sukan aika gida ko kuma duk inda nake don a nemo ni. Ba sa iya ba wani aikin har sai bayan sun ji cewa uzurina ba zai bari na dawo wajen sana’ar ba. Ba na samun wasu matsaloli sakamakon wani ya ganni haka. Saboda kwadayin gobe su dawo kuma watakila mutum ya kawo ma wani, ina jajircewa wajen tabbatar da cewa na yi masu aiki mai kyau, mai inganci.
Aminiya: Kana da wasu da ke koyon sana’ar a karkashinka?
Ah, akwai akalla mutum shida da suke karbar horo a karkashina kan wannan sana’ar ta gyaran babur.
Aminiya: Wadanne kalubale kake fuskanta a halin yanzu?
A gaskiya kalubalen da yake bijiro mini wanda yake sa raina ya baci…, ka san duk wanda Allah Ya bai wa sani, idan ya ga wani abu da ya saba wa addini, to ya zama wajibi ya yi nasiha a kai. Idan kuma ya yi shuru, to Ubangiji zai iya yin fushi da shi. A irin wannan yanayin ne za ka ga wadanda ba sa son nasihar suna jifanmu da bakaken maganganu. Amma ba za mu gaji ba, saboda irin kalubalen da Manzon Allah (SAW) ya fuskanta ya fi haka. Ka ga ke nan wannan ba komai ba ne. Hakan ya sa kuma dole mu yi hakuri don koyi da shi.
Aminiya: Kana da wani buri?
Babban burina shi ne na ga na taimaka wa kasa ta. Kodayake ina da burin ci gaba da karatuna da fatan zama Lauya bayan na kammala.
Aminiya: Ya batun iyali?
Ban yi aure ba tukuna.