Yadda gurgu ya zama babban likita(3)

Ko za ka fara da gabatarwa?Sunana Dokta Waheed Ola Bodulorin Oki. An haife ni a Legas, a 1961 kuma da lalurar shanyewar kafafu aka haife ni. Na yi karatun firamare a Surulere, daga nan na je FGC da ke Ilorin Jihar Kwara. Na koma Legas na yi karatun Kiwon Lafiya a Kings College, sai na […]

Yadda gurgu ya zama babban likita(3)
Yadda gurgu ya zama babban likita(3)

Ko za ka fara da gabatarwa?
Sunana Dokta Waheed Ola Bodulorin Oki. An haife ni a Legas, a 1961 kuma da lalurar shanyewar kafafu aka haife ni. Na yi karatun firamare a Surulere, daga nan na je FGC da ke Ilorin Jihar Kwara. Na koma Legas na yi karatun Kiwon Lafiya a Kings College, sai na je Jami’ar Legas na yi karatun likitanci. Na kammala a cikin shekaru 6, na yi aikin gwaji a Asibitin Jami’ar Sakkwato. Bayan nan na yi hidimar kasa a Badagry Legas, inda tun a wannan lokacin har zuwa yanzu nake aiki kuma a halin yanzu ni ne Babban-Darakta a cibiyar lafiya ta Oloki da ke a Badagry.
Kasancewarka mutum mai tattare da nakasa, ko hakan na da wani tasiri a rayuwar karatunka na likita da kuma ba ka damar yin aikinka yadda ya kamata?
Nakasata ba ta tauye mini komi ba a lokacin da nake karatu, illa kawai ’yan wahalhalun da na fuskanta saboda rashin kafafuna. Misali, idan muna da darasu a saman bene ko makamancin haka kuma ni ban dauki wannan a matsayin wata matsala ba, don hakan shi ya ba ni kwarin gwiwa. Shi karatu musamman na likitanci, cike yake da kalubale ba ma ga nakasasshe kadai ba, har ga masu cikakiyyar lafiya. Dalili kuwa, za ka ga da yawa daga dalibai kan shafe sama da shekaru 10 a makaranta, wasu a haka za a kore su, wasu kowa tun a shekarar su ta 2 ko 3 za a sallame su bisa dalilan kasawarsu ko makamancin haka. To ka ga ni alhamdu lillahi, cikin shekaru 6 na kammala. A farkon karatun ne na yi niyyar sauya sheka saboda wahalhalun karatun na likita bisa la’akari da hallitar jikina amma da na ba da himma kwarai sai Allah cikin ikonSa Ya dafa mini na kammala cikin nasara, ba tare da na taba gamuwa da wata cikas a lokacin da nake karatun ba, sannan ban taba samun wata tsangwama daga malamaina ko abokan karatuna ba. A bangaren aiki kuwa sai da na zama likitan da marasa lafiya suka fi so ya kula da lafiyarsu a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman danfodio da kuma asibitin da na yi hidimar kasa, inda nake aiki a halin yanzu.
Ko me ya sa marasa lafiya suka fi so ka zama likitansu?
Ba wani abu ba ne illa irin kulawa ta musamman da nake ba su. Ina yin aikina cikin nutsuwa tare da ba da hankali sosai ga marasa lafiya. Wannan shi ne dalilan da suka sa marasa lafiya ke matukar kaunata, wanda hakan ya sa ban iya rabuwa da asibitin da na yi hidimar kasa ba saboda shakuwa da marasa lafiyar wurin suka yi da ni. Hakan ya sa na yanke shawarar ci gaba da kulawa da su, a maimakon in je in nemi aiki da gwmnati. Na yi hakan ne domin in samu cikakken lokacin da zan ba jama’a gudunmawa.
A bayanan da muka samu, taimakon da kake bayarwa bai tsaya ga marasa lafiya kadai ba har da ma nakasassu ’yan uwanka. Ko za ka yi mana karin haske a kan hakan?
Ai idan ba na taimaka wa ’yan uwana nakasassu sai Allah Ya tambaye ni. Dole ne in taimaka musu ta hanyar da Allah Ya hore mini. Na kafa kungiyar taimakonsu da kare hakkinsu, na kuma rubuta littattafai da dama a kan yadda ya kamata a ba su kulawa ta musamman, a horar da su ta yadda za su amfani kansu su amfani jama’a da duniya baki daya. In ana maganar, horarwa ba wai horon da za a yi wa gangar jiki ta iya yin wani abu kadai ba, a’a, akwai horon da za a yi wa kwakwalwa ta amfani kanta ta kuma amfani al’umma. Kowace irin nakasa ce da mutum, mutukar za a ba shi horo na kwakwalwa, to zai amfani kansa ya amfani kasa baki daya. Da gwamnati za ta maida hankali a horon kwakwalwa ga nakasassu, da an samu lokitoci da injiniyoyi da akantoci da dai sauransu a cikin nakasassun; ka ga da an magance matsalar bara an kuma ba su damar a dama da su a ci gaban kasa.  Ka ga da gwamnati da iyalansu sun huta da daukar dawainiyarsu.