Yadda gwamnan Kogi ya bude wa dattawan Arewa wuta
Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya zargi dattawan yankin Arewa a Najeriya da cin amanar Sardauna ta hanyar yin watsi da ayyukansa. Yahaya Bello ya ce maimakon dattawan Arewa su dora a kan ayyukan Sardauna na ci gaban yankin, sai suka mayar ta yankin koma-baya, har ta kai ga attajiran yankin ba sa iya zuba […]
Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya zargi dattawan yankin Arewa a Najeriya da cin amanar Sardauna ta hanyar yin watsi da ayyukansa.
Yahaya Bello ya ce maimakon dattawan Arewa su dora a kan ayyukan Sardauna na ci gaban yankin, sai suka mayar ta yankin koma-baya, har ta kai ga attajiran yankin ba sa iya zuba jari a nan.
Ya zarge su da haddasa husumar da ke kawo zubar da jini da sunan addini ko kabila, alhali “Sardauna matsayin shugaban Arewa, ya yi wa kowa adalci ba tare da nuna bambanci ko fifiko ko rufa-rufa a harkokin gwamnati ba, shi ya sa ya samu gagarumar nasara”.
“Abun mamaki shi ne rashin tsarkin niyyar shugabannin yankin ya zama babban tarnaki ga ci gaban yankin, kuma babu mafita face yin koyi da kyawawan dabi’un Sardaunan Sokoto, wanda babu ruwansa da bambanci addini ko kabila”, kamar yadda ya ce.
A nasa bangaren, jagoran tawagar, Sanata Ibrahim Shekarau ya bayar da tabbacin cewa gidauniyar za ta ci gaba da yin iya kokarinta wurin tabbatar da hadin kai a yankin Arewa.
Ya kuma bukaci jihohi da su bayar da muhimmanci wajen yin tsattsauran hukunci ga masu aikata fyade, la’akari da yadda matsalar ke yawaita.