Yadda Gwamnan Oyo ya tsallake hari a Kogi
Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo wanda ya tsallake rijiya da baya a garin Lakwaja a matsayina na jagoran yakin zaben dan takarar PDP a zaben Gwamnan Jihar Kogi da ka gudanar ranar Asabar da ta gabata ya ki cewa uffan kan batun. Sai dai Gwamna Makinde ya yi gugar zana ga masu hamayya da […]
Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo wanda ya tsallake rijiya da baya a garin Lakwaja a matsayina na jagoran yakin zaben dan takarar PDP a zaben Gwamnan Jihar Kogi da ka gudanar ranar Asabar da ta gabata ya ki cewa uffan kan batun.
Sai dai Gwamna Makinde ya yi gugar zana ga masu hamayya da shi inda ya ce, “Mun shaida musu cewa su yi hakuri sai shekarar 2023 su fito mu fafata.”
Gwamnan Makinde bayan ya koma gida daga Jihar Kogi ya kaddamar da aikin sabunta hanyar Moniya-Ijaye-Iseyin mai nisan kilomita 65 wadda za a kashe Naira biliyan 9 da miliyan 900 kuma ake sa ran kammalawa cikin wata 12.
Kafin ya kaddamar da aiki sai da Gwamnan ya soke kwangilar aikin da tsohuwar gwamnatin jihar ta kasa aiwatarwa cikin shekara takwas tana kan mulki.
Cikin jawabinsa a wajen bikin a ranar Litinin da ta gabata Gwamnan ya ce “Sun karbi kudi ba su yi aikin komai ba.” Sai ya yi tambayar cewa, “Sun kashe kudin a kan zabe shin kun jefa musu kuri’a kuwa? Idan suka dawo suka bukaci kuri’a daga gare ku za ku jefa musu kuwa?”
Amma Mai ba Gwamnan Shawara ta Musamman Mista Moses Alao, ya bayyan yadda aka kai harin ga Gwamna Makinde inda ya shaida wa ’yan jarida cewa “Da misalin karfe 12 da minti 50 na ranar Juma’a ne wadansu ’yan bindiga rufe da fuskoki suka yi wa Suitorial Hotels da ke Lakwaja dirar mikiya a kokarin shiga dakunan da Gwamna Makinde da ’yan kwamitinsa suka sauka domin gudanar da kamfe na zaben Injiniya Musa Wada da Jam’iyyar PDP ta tsayar takarar Gwamna. Mun samu tabbacin aukuwar haka ne daga Lakwaja.”
Moses Alao, ya ce “Labarin da muka samu ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun yi bad-da-kama a matsayin ’yan sanda inda suka isa masaukin Gwamnan cikin motoci kusan 100. Sai dai ba su iya cimma burinsu ba dalilin tsauraran matakan da jami’an tsaron Gwamnan suka dauka wajen fatattakarsu.”