Yadda gwamnati da masu ruwa-da-tsaki a fannin kiwon lafiya ke dakile cutar kwalara

Duk da gagarumin kokarin da masu ruwa-da-tsaki ke yi wajen inganta tsabtar sansanonin ’yan gudun hijira tare da tabbatar da ana bin ingantacciyar hanyar kula da tsabtar muhalli, cutar kwalara ta bayyana a matsayin babban kalubale ga kiwon lafiya, inda masu ruwa-da-tsaki suka tabbatar da rahoton bullar cutar ko yiwuwar kamuwa da ita a tsakanin […]

Yadda gwamnati da masu ruwa-da-tsaki a fannin kiwon lafiya ke dakile cutar kwalara

Duk da gagarumin kokarin da masu ruwa-da-tsaki ke yi wajen inganta tsabtar sansanonin ’yan gudun hijira tare da tabbatar da ana bin ingantacciyar hanyar kula da tsabtar muhalli, cutar kwalara ta bayyana a matsayin babban kalubale ga kiwon lafiya, inda masu ruwa-da-tsaki suka tabbatar da rahoton bullar cutar ko yiwuwar kamuwa da ita a tsakanin mutum 3,140 da kuma rasuwar mutum 53. Rashin tsabtar ruwa da rashin tsabtar muhalli suna iya kara munin annobar. Wuraren da aka gano cutar ta fi illa su ne Maiduguri da Dikwa da Monguno.  Kuma a cewar wata sanarwa da Ofishin Tsara Taimakon Ayyukan Jinkai na Majalisar dinkin Duniya (UNOCHA), abokan hadin gwiwa a ayyukan jinkai suna aiki da gwamnatin Najeriya wajen dakile annobar.

An samar da kayayyakin jinya na musamman a dukan wuraren da aka gano bullar cutar. Kuma zuwa yanzu an samar da gadajen kwantar da majinyata 330 domin daukin gaggawa ga wadanda cutar ta fi galabaitawa a tsakanin manya da mata da yara.

An kuma samar da cibiyoyin bayar da maganin ruwan gishiri da sukari don hanzarta bai wa wadanda suka kamu da cutar amma ba ta galabaita su ba. Kuma idan bukata ta taso ana ajiye wadanda suka kamu da cutar na kwana daya zuwa biyu a wadannan cibiyoyi kafin a sallame su. Za a iya yin rigakafin kwalara ta hanyar gudanar da allurar rigakafi. Ma’aikata Lafiya ta Tarayya tare da tallafin hukumomin bayar da agaji za su bullo da wani kamfe a wuraren da cutar ta fi shafa a wannan wata. Sannan asibitocin da suke fama da karancin ruwan sishiri da sukari da sauran magungunan hana yaduwar cututtuka da masu karfafa jikin marasa lafiya da za a iya amfani da su wajen dakile kwalara da sauran magunguna wajibi ne a sayo su.

Sanya ido yana da muhimmanci wajen hanzarta gano alamun kwalarar. Kuma a duk lokacin da aka gano wani gida yana dauke da mai cutar, majiyancin da duk wanda aka ga alamun cutar a hanzarta kai su asibiti ko cibiyar kula da cutar da ke kusa. Baya ga haka an tura jami’an kiwon lafiya su yi feshi a gidaje da rumfunan da mutanen suke zaune.

Kuma ana karfafa wayar da kai kan samar da muhalli mai kyau a tsakanin jama’a babban hanya ce ta magance yaduwar cutar. Sannan abokan hadin gwiwa suna amfani da salon ziyartar gida-gida da kamfe din wayar da kai da kungiyoyin matasa da mata da makarantu ke yi da kuma lillika takardu kamfe da watsa kamfe din a rediyo da sauran hanyoyi don fadakar da jama’a kan yadda za su kauce wa harbuwa da cutar. Har wa yau kungiyoyin jin kai suna kafa tashoshin wake-hannu a duka cibiyoyin da ’yan gudun hijirar suke a wuraren da cutar ta fi muni da kuma tsabtace wuraren bayi da kuma horar da ma’aikatan jinya.

Akwai bukatar a kara zage damtse don magance yaduwar cutar, sai dai kungiyoyin bayar da tallafi a yankin suna da takaitaccen iko. A cewar UNOCHA, hukumomin bayar da agaji a yanzu haka an tilasta su karkatar da albaraktun da suke da su daga sauran ayyukan ceto rai zuwa ga kokarin magance kwalara. Wannan barkewar annoba ta watsu zuwa wasu sassa na Arewa maso Gabas ko tana neman daukar dogon lokaci ba tare da daukar mataki ba. ana bukatar karin kudi domin a magance yaduwarta. “Wajibi ne mu magance wannan cikin gaggawa domin yin rigakafin aukuwar wahala da asarar rayuka,” inji Peter Lundberg Mataimakin Shugaban Ayyukan Jinkai na Najeriya.  Shirin kawo dauki da rigakafin cutar kwalarar an tsara shi ne don biyan bukatun mutum miliyan 3 da dubu 700 da za su iya kamuwa da annobar.