Yadda Gwamnati Tarayya take asarar biliyoyin Naira a Shirin Noma na Gurara

Daya daga cikin shirye-shiryen Noman Rani na Gurara, (Gurara Irrigation Scheme) da Gwamnatin Tarayya ta ware biliyoyin Naira na fuskantar kalubale sannan bangaren na samun koma baya saboda rashin kula da shirin wanda ke Unguwar Azara a garin Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko Jihar Kaduna. Shirin wanda aka kaddamar kasa da shekara biyar, sai […]

Yadda Gwamnati Tarayya take asarar biliyoyin Naira a Shirin Noma na Gurara

Noma a yankin Gurara

Daya daga cikin shirye-shiryen Noman Rani na Gurara, (Gurara Irrigation Scheme) da Gwamnatin Tarayya ta ware biliyoyin Naira na fuskantar kalubale sannan bangaren na samun koma baya saboda rashin kula da shirin wanda ke Unguwar Azara a garin Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko Jihar Kaduna.

Shirin wanda aka kaddamar kasa da shekara biyar, sai gashi abin ya zama wani abu daban, ba kamar yadda aka kirkira da farko ba.

Majiyarmu ta gano cewa, shirin na fuskantar kalubale ta hanyar ta hanyar sace-sace,  matsalolin da ke da alaka da noman rani, gurbatacciyar kasar noma wanda ya sanya manoma da dama basu iya girbe abin da suka shuka.

Ya zama wajibi ne ga manoman yankin su tabbatar da tsaron amfanin da aka shuka a gonakin. Da wakilinmu ya tuntubi masu gadin yankin sai ya ce, sun kai watanni ba a biya su hakkinsu. Daya daga cikin masu gadin gonakin kamar Mista Shedrach Obadiah ya ce, a yanzu haka yana yunkurin ajiye aikin.

Shirin noman rani wanda yana daya daga cikin wani bangare na ayyukan kogin da gwamnatin tarayya ta ware tsabar kudi naira biliyan 15.1 a shekarar 2001 don yashe kogin Gurara zuwa karamin kogin Usuma don ya hadu da ruwan Abuja wanda ake da bukata.

A shekarar 2007 gwamnatin tarayya ta kara shirin da samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa wanda ya lakume naira biliyan 38.5 wanda ya maye kudin kwangilar na baya a naira biliyan 54.3.

Hektar noma dubu 6 da aka tanadar wa shirin ya isa kananan manoma da manyan manoma. Kamfanoni biyu ke lura da shirin wadanda suka hada da: SCC Nigeria Limited wanda ke aiki a hekta dubu 4 da kuma Kamfanin Salini Nigeria Limited da ya  yi aikin hekta dubu 2.

Kamfanin SCC Nigeria Limited na aikin rarraba ruwa a shirin da ya kai tsawon kilomita 29 (1,400mm steel) bututu da ya kai, 100,000 m3 wanda ke kula ruwan da aka adana yayin da ake rarraba sauran ruwan a gonakin na hekta dubu 4.

Wakilinmu wanda ya ziyartarci yankin ya tabbatar da cewa, harkokin noman na koma wa baya a hankali, wasu kadan daga cikin kamfanonin iri da ke Kaduna ne kadai suke kokarin raya wurin.

Wasu daga cikin manoma sun bayyana cewa, noma a yankunan ya yi matukar tsada sakamakon rashin aiki mai kyau da kamfanin huda ya yi a gonakin.

Wani daga cikin manoman Abdullahi Abubakar da ya girbe masara hekta biyu.

Ya bayyana wa wakilinmu cewa, manoman da ke sayar da amfanin gonakinsu a kasuwanni ba su iya samun abin da suka girba kamar yadda ya dace.

Ministan Ma’aikatar ruwa Suleiman Adamu ya yi alkawarin kammala ayyukan da aka bari a maimakon kaddamar da sababbi a yankin.