Yadda Gwamnatin Filato ta dawo da shirin tsaftace Jos – Abdullahi Abbas

Kwamishinan muhalli da ma’adanai na Jihar Filato Alhaji Abdullahi Garba Abbas ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dawo da shirin nan na aikin kwashe shara ne, don ganin ta tsaftace garin Jos da sauran manyan garuruwan jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos. Ya ce […]

Yadda Gwamnatin Filato ta dawo da shirin tsaftace Jos – Abdullahi Abbas

Kwamishinan muhalli da ma’adanai na Jihar Filato Alhaji Abdullahi Garba Abbas ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dawo da shirin nan na aikin kwashe shara ne, don ganin ta tsaftace garin Jos da sauran manyan garuruwan jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos.

Ya ce a lokacin da wannan gwamnati ta zo ta ga cewar ya kamata a sake dawo da kwashe shara a garin Jos da kewaye, domin mun samu garin duk shara ta cika. Kuma idan aka dawo da kwashe sharar dukkan kananan cututtukan da ake fama da su za a magance su. Don haka a zaman majalisar zartarwar jihar aka dawo da wannan shiri.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa, an dauki matakai da dama don ganin an aiwatar da wannan shiri, ta hanyar taro da masu unguwanni da matasa da sauran masu ruwa da tsaki kan wannan al’amari.
Ya ce sakamakon dawo da wannan shiri yanzu garin Jos ya sake dawowa cikin tsafta. Yanzu ana cewa bayan Akwa Ibom da Abuja babu wani gari a Najeriya mai tsafta kamar Jos.
Ya ce suna da masu shara na jiha, wadanda sun kai mutum dubu biyu, sannan kuna suna da masu shara guda 150 a kowace karamar hukuma dake jihar Filato.