Yadda gyaran manyan babura ya sa na zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura – Bawada

Malam Muhammad Husaini Bawada daya ne daga cikin fitattun masu gyaran manyan baburan nan da ake kira da Power Bike da jami’an tsaro da masu kumbar susa suke amfani da su. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana yadda gyaran wadannan babura suka kai shi ga zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRSC): Kana daya […]

Yadda gyaran manyan babura ya sa na zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura – Bawada

Malam Muhammad Husaini Bawada daya ne daga cikin fitattun masu gyaran manyan baburan nan da ake kira da Power Bike da jami’an tsaro da masu kumbar susa suke amfani da su. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana yadda gyaran wadannan babura suka kai shi ga zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRSC):

 Malam Muhammad Husaini BawadaKana daya daga cikin masu gyaran manya babura, a ina ka koyi wannan sana’a har ka kai ga wannan matsayi?
Wannan sana’a na faro ne da gyaran batir a 1970 zuwa 1975, to a cikin wadannan shekaru ne aka yi canjin tuki, wato kiliya daga hagu zuwa dama kuma aka yi Odoji. Da aka yi Odoji sai babura suka shigo da yawa, ni kuma ina sha’awarsu, a lokacin ko keke ba ni da shi, sai ya zamo akwai masu sayar da babura a wurinmu kuma suna gyarawa a Titin Faransa (Franch Road) a cikin birnin Kano, don haka sai na fara gyaran babura. Amma na fara koyon gyara ne a Oriya da ke kofar Wambai, Kano. Ka san gyara ana koya ne a kan hanya. Saboda mutanen da, sun zauna da Turawa su kuma suna koya wa mutane ainihin yadda za ka rike musu motoci da abin hawansu. Shi ya sa idan tsohon direba ya rika, sai ya koma makanike. Duk makanike da ake gani a bakin hanya, to daga wajen tsohon direba ya koya.
Kai ma a hannun tsohon direba ka koya?
Eh, na koya ne a hannun Alhaji Ali Gwano, tsohon direba ne, kuma ko da na yi aiki da Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) da satifiket dinsa na yi amfani. Amma farko a wurin wani Bayarbe mutumin Ilorin mai suna Alhaji Ibrahim na fara koyo, mun zauna a Kano a 1973 zuwa 1974, sai aka yi rusau, lokacin Uba Adunkule. Aka rushe rumfunanmu na wucin-gadi, to rusau din tamfurare ya sa muka koma Ilorin da Alhaji Ibrahim, a can na samu takardar shaidar koyon gyara a 1975.  Sai na dawo na bude gyaran babur a Kano. To akwai wani ana ce masa Ali Ado hedimasta ne, sai ya karfafa min gwiwa in yi makaranta a inda yake, sai na fara firamare a wurin na gama, iya firamaren na yi saboda halin maraici na tsaya.
Daga firamaren ka ci gaba da gyaran baburan ne ko yaya?
Kafin in kammala firamare a 1977 na koma harkar sayar da tsofaffin motoci irin wadanda suka yi hadari ko suka buga, ana cire bangarorinsu ana sayarwa. A nan na yi fama da ’yan sanda ba kadan ba, wanda hakan yana daga cikin abin da ya ba ni sha’awar shiga aikin tsaro. Saboda idan aka yi sabon shugaban ’yan sanda (DPO) sai an kawo shi wurina a Fagge, sunana na can. Tankin babur sai a zungure shi a ce ina takardarsa, kafin me an kulle ni. Ba Ingilishi da zan iya kare kaina, sai ya zamanto na wahaltu sosai. Kuma ga mu Kanawa akwai tsoron dan sanda, babu Bakanon da zai ga an zo an ce taso, ya ce, me ya faru, akwai tsoro gare mu sai ka ji suna cewa akwai abin da ya yi musu. To haka na yi ta fama da su, har Allah Ya kawo lokacin mulkin Buhari na soja. Da aka yi canjin kudi, na ga ina da kudi sai na sayi tsofaffin motoci 33 na tara. Ana yin haka kuma ya zo ya ce Yaki da Rashin da’a, aka zo aka yi mana rusau na dawo fanko ba kudi ba mota ba karatu.
Motocin tsofaffi ne?
Eh, motocin tsofaffi ne irin a saya a gyara a sayar, galibi kananan motoci in ka cire fijo da baswaja duk sauran tsofaffi ne. Saboda kamfani sai ya rike mota na shekaru, shi ya sa kusan kowane makanike da irin motar da yake gyarawa. To amma yanzu an bi an dagula aikin, shi ya sa makanikai suke ta wahalar da mutane domin yin aikin suke yi ba tare da sun san yaya ake aikin ba.
Yaya aka lalata motoci sama da 30 da ka saya?
Lokacin da za a canja kudi, to, mu dama Kanawa muna da matsala ta hulda da banki, saboda yanzu za a kawo kaya, kafin ka je banki wani ya cire kudin ya biya, sai muke boye kudinmu a cikin loka. Da ka zo ka yi farashi mutum matsu, sai ya sayar maka ka biya, don haka sai ya zamo kudinmu na kasa, da aka ce za a canja kudi, muna tsoron zuwa banki tunda ga layi ba iyaka, kuma mako biyu aka bayar, sai na ga tunda nawa ne, sai na sayi motoci na kara. A lokacin an taso tsohuwar Kasuwar Kwari ta kofar Wambai, nan ma muka yi ta rigima a kawo soja ya yi min bulala, har Allah Ya kawo lokacin Wada Abubakar aka zo aka yi rusau, bayan dama an yi mana rusau din tun 1974 da na gaya maka. To amma sai wannan ya zamo daban da bulala da wulakanci aka yi mana aka rushe motocin na dawo zikau. Aka sa gireda filloda ta lollotsa motocin ta tura cikin kududdufin ’Yar Fari da ke kofar Wambai.
Da aka lalata motocin sai ya zamo ba zan iya aiki irin yadda jama’a ke yi ba, tunda a lokacin ina da yara fiye da 40 da suke aiki a karkashina. Bayan na dan samu wurina daga wurin Alhaji Rabi’u ina gyara Daihatsu shi kuma yana gyara Suzuki, to Daihatsu ta fi wahalar gyara ni kuma Allah Ya hore min iya gyaranta. To sai na nemi kwangila na fara zuwa Kano Line na tambaye su ina son kwangila suka ce ba za su iya ba ni ba, sai zuwa lokaci kaza. To a lokacin duk wata fijo da aka kawo musu sai ta rika ba su wahala, da an sanya mata mai sai ta buga, sai suka ce an sa musu hannu ne an binne musu jakai, an binne mene ne. Sai suka ce a je a nemo wadanda za su yi kwangila, to sai kowa ya yi kokarin ya kawo nasa, aka kawo maigidana a Tudun Murtala wato Alhaji Ali Gwano, aka kawo Godwin na ’Yan Kaba, shi ma makanike ne, aka kawo wani Alpha dan Kaduna, shi kuma makaniken baswaja ne, ni kuma danlami Legas ya kawo ni, saboda ya amince da gyarana.
To a lokacin Manjo Daba ya tara mu aka yi mana intabiyu aka ce tunda ina da dan bambancin ra’ayi da sauran, motar Manjo Daba zan gyara, na gaya musu abubuwan da za su sayo na zo na hada mota ta tashi. Na ce kada su sanya mata man da suke sanyawa, saboda na lura man ne yake sanyawa ta buga. Sai wani Ibrahim Injiniya ya ce a’a, ban fi shi sanin aiki ba, duk motocin nan manya da kanana shi yake aikinsu, wannan man za a zuba. Na ce idan injin ya buga babu ruwana suka ce sun yarda, na sa mai a mota na tayar da ita ta fara karara kakaka, ta buga. Na ce to, yaya? Sai suka ce ai ba an gaya min asiri aka yi ba, na ce, ba asiri ba ne, man da kuka sanya ne. Suka ce to, abin da za a yi ba za a sayo kaya ba, a je a cire karanshaf din a yanka a cire biyari, na ce na yarda aka yi haka na sanya na tsallaka gidan man Mobil lokacin galan din karfe ne na sayo mai na dura. Ina tashin mota sai aka zo ana gani. To na kule ina tashinta na ba ta wuta ta yi kara, ta yi kara, Manjo Daba ya fito da gudu mene ne haka? Sai suka ga mota tana yi, na ce an gama. Akwai Ibrahim injiniyan gwaji da Ibrahim direban gwaji, sai Ibrahim injiniyan gwaji ya tuka motar zuwa hanyar Zariya ya dawo ya ce mota ta yi. Suka ba ni kudin aikina Naira 600 na wancan da na hada aka sa mai ta buga da na baya Naira dari uku-uku, wannan a zamanin mulkin Babangida ne. To, garin neman kwangila na hadu da wani mai suna Umar Aliyu Sakkwato, jami’in safiyo ne yana so ya tafi makaranta amma motarsa ta buga kuma yana son motar. To na zo wucewa sai yarana suka ce ga oganmu nan, ya ce wannan din suke ce, eh. Suka ce in ka gaya masa zai gyara. Sai ya yi min bayani na duba na ga ashe kuskure suka yi akwai wani rodi yana da dan fin in suka raba sai ya fito, sai na yanki kusa na sanya na rufe. To shi ne da ya ga mota ta yi, sai ya je ya samu shugaban jami’a a Sakkwato, ya ce yana da wani yaro kaza-kaza ya iya gyaran motoci, sai suka turo na je na duba motocinsu na gyara musu, to, in aiki ya taso sai in je.
A zamanin Babangida ne na samu sassauci ta bangarena, aka fito da Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) a 1988, na je na samu Alhaji Bappha Daneji na ce ina son zan yi aikin kwangilar gyaran baburansu. Sai suka ce ma iya gyaran wadannan manyan babura ne? Na ce eh. Wato su ABS da Jawa da Jam Breakes da sauransu, irin wanda Janar Gowon ya yi amfani da su Suzuki Ram-F System bai da matsala sosai. SuTiger da Triumph su ne suke da dan wahalar gyara. Domin makanike abin da ya fi sani shi ne timing, alhali ba shi ne iya gyara ba, na gano haka ne bayan na yi karatu a Japan. Akwai abin da inji yake ci akwai abin da yake sha, kamar yadda ake ganin akuya da kare suna da bambanci duk da cewa kafarsu hurhudu, to, haka injuna suke. To wannan ne ya zamanto Road Safety suka nuna suna son in yi aiki da su. Na ce yaya zan yi, aka ce in kawo takarduna na aiki. Na zo na dauki satifiket dina na aikin kanikanci da na firamare na kai musu. Suka ce to, ai kai ana daukarka da matsayi, yaya za ka kawo wadannan takardu. Na ce su nake da su. Shekara biyu ina bi, sai Bappa Daneji ya tura ni Legas ya ce shi ba zai iya dauka ta aiki ba, ban taba zuwa Legas ba, haka na shiga motar katako Naira 30 aka kai ni Legas ana ruwan sama, na sauka Oshodi. Dama ya ce in shiga motar Bariga domin a sauke ni a Bagada, na shiga mota har aka wuce Bagada ban sani ba, sai dai muka isa karshen tasharsu suka tambaya na gaya musu inda za ni, suka yi min kwatance na koma a kafa na samu wani dan sanda mai bayar da hannu ga ababen hawa ya nuna min ofishin hukumar.
Na shiga na ce na zo a dauke ni aiki, ba su jin Hausa ni kuma ba na jin Yarbanci ba na jin Ingilishi. Aka ce min wanda yake daukar aikin wani mai suna Injiniya Ogoro ba ya nan ya tafi Bauchi sai gobe zai dawo. Ban san kowa ba, ina zan je in jira Injiniya Ogoro ya dawo, sai na fito bakin kofar hukumar na samu wani mai suna Ali mai sayar da sigari na ce masa, na zo nan ne a dauke ni aiki, ni mai gyaran irin wadannan manyan babura ne, amma ga halin da nake ciki. Ya ce shi ma ya taba aiki da hukumar amma an sallame shi, suna da rigima wurin. Muna tadi ya ce to, kai dan Kano me ya kawo ka nan? Na ce Bappah Daneji ne ya ce in zo ga wasikar da ya ba ni, ya ce to shi ke nan. Amma abin da za a yi ba shi za ka gani ba, akwai danyaro Yakasai dan Kano ne, in ka gan shi magana ta kare ko a dauke ka ko a ki daukarka. Washegari danyaro Yakasai ya zo ya shiga, aka ce in dakata ya zauna. Dama Ali ya gaya min sunayen galibin ma’aikatan ya ce in je in samu wani maigadi mai suna Ajayi, in ce na zo ganin Malam ne daga Kano, kada in ce na zo neman aiki ne.
Shi ne bayan karfe 10 na shiga aka kai ni ofishinsa na durkusa har kasa na rasa ma me zan gaya masa. danyaro ya tambaye ni me na zo yi, na ce na zo ne a dauke ni aiki. Ya ce daga ina na ce daga Sakkwato. Ya ce ina takarduna na mika masa, sai ya duba ya gani ya ce ah, haka Bappah Daneji zai yi min? Na ce, yaya? Ya ce na farko abin da ya rubuto a takardar ya ce kada a dauke ka aiki, sannan ya turo ka Legas, wurin wa? Na ce Injiniya Ogoro. Sai ya dauki biro da takarda ya yi rubutu, har ya ba ni aiki, sai ya yi tunani ai nan Legas ce, in ya dauke ni zan samu matsala saboda rashin Ingilishi da takardun ilimi. Sai ya ce in je in same su a can, na je na samu mataimakin Ogoro mai suna Akpabio, to yana dan jin Hausa muna magana yana dariya ya ce yaya za a yi abin da Bature ya yi babu wanda ya taba cewa zai iya gyara shi, amma kai kana Bahaushe ka ce za ka iya? Sai na ce ai koya ake yi ba yare ba ne. Sai aka kawo min baburan aka ce mene ne damuwar wannan na ce kaza ne, wancan kuma ya ci kaza ne, aka yi min tambayoyi aka ce na iya hawa na ce na iya. Malam danyaro ya ce ba zai iya dauka ta aiki a Legas ba, in dawo Kano in samu Abdurrazak in ba shi takarduna ya hada mu muka nufi Kano tunda an yi min intabiyu a Legas cewa su duba.

Daga Salihu Makera

Kana daya daga cikin masu gyaran manya babura, a ina ka koyi wannan sana’a har ka kai ga wannan matsayi?