Yadda gyaran manyan babura ya sa na zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura – Bawada (3)

A makon jiya ne muka fara kawo wannan tattaunawa da Malam Muhammad Husaini Bawada, fitaccen makaniken manyan baburan nan da ake kira da Power Bike a Abuja, inda ya fara bayyana yadda gyaran wadannan babura suka kai shi ga zama jami’in Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC), yau ga karashe: To da aka sanya mu […]

Yadda gyaran manyan babura ya sa na zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura – Bawada (3)
Yadda gyaran manyan babura ya sa na zama jami’in Hukumar Kiyaye Hadura – Bawada (3)

A makon jiya ne muka fara kawo wannan tattaunawa da Malam Muhammad Husaini Bawada, fitaccen makaniken manyan baburan nan da ake kira da Power Bike a Abuja, inda ya fara bayyana yadda gyaran wadannan babura suka kai shi ga zama jami’in Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC), yau ga karashe:

To da aka sanya mu a motar sai na ga Abdurrazak din yana da masifa da yawan fada, muka dawo Kano sai na ce wannan ba zan iya aiki da shi ba. Sai na rabu da shi, shekarar 1990 na dawo, 1991 ban je ba, a 1992 sai aka ce ka ce za ka yi aiki da Road Safety, amma ka yi shiru. Na ce zan yi, sai mutane suka ce ba zan iya ba, mai samu kudi kamata ne zai iya aikin. Na ce zan iya. Abin da ni nake fata in ka gama aiki da gwamnati za a ba ka fansho, saboda na taso cikin rauni don haka zan yi hakuri da duk wulakancin da za a yi min don in samu fansho. Sai na koma hukumar na samu Ajingi shi ne kwamandan jihar na gaya masa abin da ake ciki. Ya ce tuntuni me nake jira? Ya ce to, amma tunda ana bukatar masu gyaran babur din sai ya karbi takardun ya tura sai aka dawo min takardar daukata aiki na fara a lokacin Kabiru Nadabo shugaban sashin ma’aikata shi ya yi min tambayoyi ya bude min fayil aka dauke ni a mataki na 3 karamin mataki na 2 (03/2), amma a can Legas matakin na 5 suka dauke ni, saboda jinkirin da na yi aka dauke ni a haka. To da aka dauke ni, na dauka in aka gan ka da bakin mai shi ne za a dauke ka makanike, ka san haka kanikawa muke, to sai aka ajiye ni gefe. Ina zaune saboda babur din ba kullum zai baci a gyara ba, mota kuma ba a san na iya gyaranta ba. Sai wata rana gidan wani ma’aikacin Kwastam ya kama da wuta, aka ce yaya za a yi a je hukumar kwana-kwana a sanar da su? Sai aka ce ba ga ni ba, tunda na ce na iya babur din a ba ni mana, sai Ajingi ya ce, a’a shi ba ya so a ba ni wannan babur mai gudun kilomita 300 a cikin awa daya in je in mutu. Sai aka ce tunda aikinsa ne ai abin da aka dauke shi ke nan, sai aka ba ni na hau babur din nan na ajiye musu wata kura ba a kara ganina ba, kafin me na taho da ’yan kwana-kwana, sai aka ce ashe ba mu da mahaya babur, muna da wannan amma ba mu sani ba, nan da nan aka mayar da ni dan sintiri. Ni ne hanyar Katsina zuwa Jibiya, Kunya zuwa babura, hanyar Maiduguri da sauransu. Har ta kai in direbobi masu laifi za su bi hanya in aka ce ni ne a kan hanya sauke lodi suke yi, da sun tambaya mai jiki ne ko dan tsamurmurin nan, aka ce tsamurmurin ne, sai su sauke lodi, saboda sun san ba za su iya guje min ba.
Sai aka zo aka dauki sababbin ma’aikata a Hukumar FRSC, inda aka sauke masana aikin aka kawo malaman makaranta aka zuba, wannan shi ne dalilin sukurkucewar hukumar. Ga mukami amma ba ka san aikin ba, ba rubutu ba ne Road Safety, kamar aikin duba motoci ne, kowane gari b.I.O yakan bayar da samfurin motarta, kowane gari motocinsu daban ne, haka shi ma Road Safety yake. To su da suka zo sai suka ce duk abin da yake a rubuce shi za a yi, sai aikin ya fara lalacewa, na ji ba na son aikin. Lokacin an kawo dandarman dan Hakimin Daura, na ce masa yallabai zan bar aikin nan. Ya ce yaya aka yi? Na ce, aiki tun ana tsoron mutum, yau kuma ana zagin ubana, ba zan ci gaba da wannan aiki ba. Ya ce a’a ka yi hakuri komai yana canjawa ne. Na ce, to ai ni aikina kanikanci ne, zan rasa biyu, kun ba ni sintiri babu daraja, sannan kanikancin ina nema in kasa in na tsufa yaya za a yi? Sai ya ce ka bari zan mayar da kai inda za ka rika gyaran mota bangaren technical. Shi ke nan na zauna in mota ta baci in gyara har Kwamandan Shiyyar Kaduna ya ce in zo in duba masa baburansu, na je na gyara suka yi kyau sai ya gaya wa (Manjo Janar Haldu) Hananiya. Shi kuma ya ce wannan yana daga cikin mutanen da ake so a wannan hukuma, ya tambaya wace matsala muke fuskanta game da gyaran baburan, na shaida masa. Ya taba sanina lokacin da muka je Jigawa kaddamar da sabon lamba, ina kan babur wanda a lokacin aka sa wa tayar Roadmaster muna cikin tafiya ina gudu taya ta kwance na shiga daji, tun ina kan sirdi na dawo kan tanki amma ban fadi ba. Sai wasu jami’ai suka zo da mota a kan za a kwashi gawata saboda irin gudun da nake yi, amma sai aka iske ina kokarin daura wata tayar. Shi ne da Sarkin Dutse da shi Hananiya da sauran jama’a suka fito aka rika gaisawa da ni, ana mamaki kan babu abin da ya same ni. To daga nan Janar Hananiya ya san ni. A 1997 aka sayo babura kirar Honda CS726, sai aka ce su kawo makanikansu a koya musu kula da gyaransu, to tunda su Janar Hananiya da Abdullahi Ringim na sashin ayyuka san ni, sai suka ce a nemo ni da wani Zubairu, muka je mutanen Japan masu Honda suka yi mana kwas, sai ya zamanto mun samu gada ta kula da baburan da kowane abin hawa, a cikinsa akwai kula ko bincikar lafiyar abin hawa wato b.I.O, sai kara daure abubuwa da wankewa, sai kuma sanya mai wa sassan inji sai kuma sauya wasu abubuwa in ya zama dole. Aka nuna mana wajen sanya mai ba kowane mai ake sanyawa ba, man inji yana da nau’o’i tun daga dE zuwa dL. Kuma kowane inji da nau’in mansa, wani yana iya daukar nau’o’i uku, ana samu daga L zuwa baya, wani daga G zuwa baya, in ka haura musu ne matsala. Kamar Hodu da Honda da Mazda suna amfani da dG, Mitsubishi dE ba dE40 ne man ba, ana amfani da shi don bambance yanayi ne, wato mu bangarenmu muna yankin mai zafi ne, shi ya sa duk galan dinmu za a ga 20W50 ne, wannan yana nufinmu sanyinmu bai wuce digiri 20 zafinmu bai kaiwa 50. dE40 ba shi ne mai ba, mai shi ne API samfurin man fetur din Amurka. To wannan API shi ne ajin man mota, za ka ga yawanci Mazda na mutuwa Nissan na mutuwa da sauransu, to wajen kuskuren man inji ne, kuma in makanike zai hada maka sau 100, sai ta dawo ta yi hayaki, saboda ya wuce ka’ida, dukkan motoci galibi ba abin ka’ida wajen sanya musu man inji. To haka man birki yana da ajujuwansa, akwai abubuwa da dama, takardar jagora kan yadda ake kula da baburan ta nuna yadda za a kula da komai. Gwargwadon kilomita nawa za a yi tafiya kafin a yi sabis din wannan babbar babur duk akwai a ciki.
Yadda ka san jirgin sama bai tsayawa a hanya, haka babur ko mota bai kamata ta tsaya a hanya irin yadda muke gani a hanyoyinmu ana bude gaban motoci ba. Dole mota ta tafi saboda tana da garanti, in ka ga mota ko babur sun tsaya a hanya, to karancin kula ne.
Yaya aka yi ka dawo Abuja da aiki?
To  na yi wannan kwas sai aka ce a dawo da ni nan tunda nan ne hedkwata don in rika kula da baburan hukumar FRSC. To da aka dawo da ni, in na rubuta musu abubuwan da za a yi ko za a saya, sai suka dauka wannan aikin da ake yi kudin kamar ni ake bai wa. Sai aka yi kus-kus aka ce wannan yana samun kudi don haka a nemi kamfani su rika gyaran. Daga nan sai babura suka taru suka mutu a lokacin Injiniya Wakilbe, aka kirawo mutanen Japan masu kera Honda suka zo aka nuna musu babura suka rike kai ganin yadda suka mutu. Suka ce babur din da zai ci kilomita 150 kafin a yi sabis amma ga shi wannan a kilomita 25 ya mutu, suka ce bai kamata ma a sayar wa Najeriya kaya ba, babu shugabanci kwata-kwata. Suka ce ina Bawada?  Aka ce ina nan, suka ce yaya aka yi haka? Na ce ba su son su ba ni kula da su ne, wai na yi kankanta a aiki. karamin ma’aikaci ne ni, yaya zan yi magana da manya a saurare ni. Shi ke nan babura suka lalace ko gwanjonsu aka yi ba za a saye su da kima ba. Kuma a ka’ida ma ba a gwanjon irin wannan babur a duk duniya sai a Najeriya, in kun gama amfani da su sai dai a kira kamfani ya kwashe su. Kowane babur yana da suna, bangaren namu G1 ne, ko kwamfuta ka shiga ba za ka taba samun bayani a kansa ba. Haka aka rika kai wa makanikai har aka gaji ba su gyaru ba, in ba wurinmu aka dawo mu da aka koya mana ba, ba za su gyaru ba, su kuma suna ganin arziki za mu yi, tunda abu ne da za ka je Fatakwal ko Enugu ko Legas, wannan hadari na shiga mota ka duba baburan ma ana kallon za ka samu kudi ne, haka aka bar abubuwan suka lalace. Sai dai in aka samu wani darakta ya zo yana so ya samu kudi sai ya ce a sayo sababbin babura. Ana ta asarar kudi ga kasa ana sayo babur daya Naira miliyan biyar, miliyan bakwai, saboda zalunci ya yi yawa. Ba fansho ba garatuti wane darakta ne ko ma’aikaci zai tsaya ya yi aiki tsakani da Allah a Najeriya, don ba zai yarda ’ya’yansa da iyalansa su zama marayu ba. Misali daf da zan yi ritaya na karye a kafa na rubuta wa Hukumar FRSC cewa asibitin kashi na Dala sun rubuta min za a kashe Naira dubu 147, na kawo musu, amma babu abin da hukumar ta yi, haka kafar ta gaji ta warke. Wane ne zai rike baburar Hukumar FRSC irin yadda na rike? To amma ga yadda na kare. Kuma ya kamata a yi min ritaya a matakin albashi na takwas ne, amma a na bakwai aka yi min, aka ce karatuna bai kai in kai matakin ba.
Yanzu daga ina kake samun gyaran manyan babura?
Muna da kulob na masu manyan babura. Sai dai matsalar ta shafi kowane bangare na rayuwa. Yanzu misali mutum zai kawo babur dinsa amma ya ce a sanya masa taya samfurin 190, alhali rim dinsa 180, in an sa taya ta fashe ya fadi. Ba gudu ne yake sa tayar fashewa ba, rashin bin ka’ida ne. Ainihin tayar beka ajin G za ta iya gudun kilomita 300 a cikin awa daya ba tare da ta fashe ba, wajen kwana sai taya ta fashe. Kuma ko ba ka yi gudu ba, babur din tilas ya yi gudu. Lokacin da nake tashena awa daya da rabi nake isa Kano daga nan Abuja.