Yadda hana almajiranci a wasu jihohi ke tayar da kura

Akalla jihohi hudu na Arewa da suka hada da Kano da Katsina da Sakkwato da kuma Nasarawa suka yunkuro  don hana bara a tsakanin almajirai, lamarin da ya tayar da kura tare da jawo cece-ku-ce. Jihar Kano ce ta fara haramta bara a tsakanin almajiran makarantun allon a lokacin da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Ganduje […]

Yadda hana almajiranci a wasu jihohi ke tayar da kura

Almajirai a makarantar allo a Sakkwato

Akalla jihohi hudu na Arewa da suka hada da Kano da Katsina da Sakkwato da kuma Nasarawa suka yunkuro  don hana bara a tsakanin almajirai, lamarin da ya tayar da kura tare da jawo cece-ku-ce.

Jihar Kano ce ta fara haramta bara a tsakanin almajiran makarantun allon a lokacin da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Ganduje ya kaddamar da shirin koyar da ilimin zamani a makarantun allo na jihar.

Ita kuwa Jihar Sakkwato za ta bullo ne da wani shiri da ta gano a wata kasar waje don aiwatarwa a jihar. Ita kuma Jihar Nasarawa har ta fara shirin mayar da almajiran da ta ce sun haura dubu 60 zuwa jihohin na asali bayan ta hana su bara a jihar.

Ba da gaske gwamnati ke yi ba – Alarammomi

Sai dai lokacin da Aminiya ta tuntubi Alaramma Bayero a Kano ya ce, “Idan gwamnati za ta hana almajirai bara to ya zama wajibi ta samar musu da wata hanya da za su rika cin abinci. To amma ba a tanadi komai ba sai kawai ta fito ta ce ta hana bara wannan ba da gaske ake ba, kuma ba ta shirya ba. Koda yake ban yi mamaki ba saboda gwamnati ba ta gama kula da makarantunta na boko ba ballantana ta kula da makarantun Alkur’ani ba. Ina ganin abin a wata farfaganda.”

AlaraMma Bayero ya bayyana batun da gwamnati ke yi na mayar da almajirai gaban iyayensu a matsayin take hakkin bil Adama domin a cewarsa kowane uba yana da zabi a kan rayuwar da dansa zai gudanar. “Duk dan kasa yana da hakki ya yi abin da yake so da inda yake so ya zauna tare da zabar wa dansa abin da zai yi. Mu ma muna so almajirai su yi karatun boko amma fa sai an biyo ta hanyar da ta dace an zauna da masu ruwa -da-tsaki. Idan gwamnati tana so almajirai su koma kauyukansu su zauna to dole fa sai ta gyara kauyukan ta hanyar sama musu makarantu da malamai da samar da abubuwan jin dadin rayuwa. Wannan zai sa kowa ma ba zai shigo birni ba,” inji shi.

Ba mu da abin da za mu ci idan ba mu yi bara ba- Almajirai

Yawancin almajiran da Aminiya ta tattauna da su a Kano sun nuna rashin jin dadinsu game da hana bara da gwamnatin ta yi inda suka ce ya zama dole su yi bara don ba su da wanda zai ba su abinci.

Rabi’u Amadu wanda almajiri ne a Makarantar Alaramma Nura Muhamamd da ke Goron Dutse ya ce bara ta zame musu dole domin idan ba su yi ba, babu abin da za sa su ci. “Idan ba mu yi bara ba, ba za mu samu abin da za mu ci ba. Muna neman gwamnati ta yi hakuri ta kyale mu tunda dai muna yin karatunmu kamar yadda malamanmu suka tsara mana.”

Shi ma wani alamajiri da ake kira Dan Sahabi ya ce duk da hana barar da aka yi suna ci gaba da yin ta a cikin unguwanninsu gudun kada a kama su. “Mu yanzu ba mu zuwa kowace unguwa yin bara sai dai gidajen da ke kusa da makarantarmu saboda muna tsoron kada a kama mu. Don Allah gwamnati ta tausaya mana ta janye dokar,” inji shi

‘Abin da ya sa muke tura ’ya’yanmu makarantun allo’

Wani mahaifin almajiri mai suna Malam Hashimu Ado wanda ya zo makarantarsu don tafiya da dansa ya ce suna kawo ’ya’yansu birni karatu ne ba don tsoron talauci ko gudun ’ya’yan kamar yadda wadansu ke tunani ba “Muna kawo ’ya’yanmu don su samu ilimi domin idan a gida suke ba za su tsaya su yi karatu yadda ya kamata ba. Kuma idan aka sa mana wani tsari za mu bi shi ba tare da kaucewa ba mu dai bukatarmu shi ne ’ya’yanmu su yi karatu nesa da mu saboda wannan shi ne ake samun karatu mai yawa.”

Muna goyon bayan hana bara-Almajirai a Sakkwato

Wani malami a Sakkwato
Wani malami a Sakkwato

Bello Katsira mai shekara 10 daga Karamar Hukumar Dange Shuni da ke almajiranci a Sakkwato don karatun Kur’ani, ya shaida wa wakilinmu cewa ya zo Sakkwato ne karatun allo yanzu ya kai Izu biyar, kuma ya ce idan ya yi karatu ya tashi sai ya je yawon barar abinci ya samu ya ci ya koshi kafin karatun maraice.

Ya ce, “Tun lokacin da mahaifina ya kawo ni makaratar Malam Ada a Rijiyar Dorawa da kayana kawai aka dauko ni ba abinci kullum sai na nema wa kaina abin da zan ci. Ina goyon bayan gwamnati ta hana mana yawon bara abu ne mai kyau hakan.”

Faruku dan shekara 8 daga Karamar Hukumar Isa, da ke almajirci a Birnin Sakkwato, shi ma ya goyi bayan gwamnati ta hana su yin bara domin suna shan bakar wahala “Nakan tafi nan da can ina yawon barar neman abin da zan ci, mafi yawan abincin da nake samu ragowa ce na wadansu sai ka samu wani lokacin miya ce kawai wani zubin kuma sudi za ka yi,” inji shi.

Faruku an kawo shi Sakkwato ne shekara uku da suka gabata, kamar yadda ya ambata.

Muhammadu Bashiru daga kauyen Unwala a Karamar Hukumar Illela ya ce ya kwashe shekara hudu a Sakkwato. “Mukan yi karatu da safe da rana da dare sannan muna samu lokacin yin barar  abincinmu. Ina zuwa tasahar mota da wuraren masu sayar da abinci don in samu wanda zan ci, ina iya kwashe dukk yini kafin in koma makaranta,” inji shi.

Malam Ahmad Jibiril, Shugaban Makaratar Aunir Rahamani da ke Unguwar ’Yar Kara a Karamar Hukumar Ilela ya ce, makarantarsu na da dalibai kusan 600 da malamai da dama da suka fito daga Neja da Kebbi da Sakkwato, “A gaskiya ba mu cika karbar yara daga Nijar ba saboda dokokin da muke sanya musu ba sa yarda, yaransu a hana musu yin aikin wanke-wanke ko aikin gida don samun kudi wadansu kuwa sun fi son su shiga da su a kuryar Sakkwato don Ilella gida ce a wurinsu. Muna karancin kwararowar mutanen Nijar sosai a nan sai dai wasu wurare daban.”

A Karamar Hukumar Wurno kuwa Malam Muhammadu ya ki ya zanta da wakilinmu saboda da cewarsa ya sha magana da jami’an gwamnati kan matsalolin makarantarsa da yadda za a shawo kansu da maganar gina makarantar almajirai ta zamani amma shiru, don haka yanzu ba zai ce komai ba kan shirin gwamnati na hana bara.

Za mu kwaikwayi tsarin Indonesiya – Gwamnatin Sakkwato

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce za ta kwaikwayi tsarin bayar da ilimin addini na kasar Indonesiya ne don musanya tsarin almajirici da yawon bara da ake da shi a jihar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da haka a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da yake karbar Jakadan Indonesiya a Najeriya, ABM Usra Hendra Haraha wanda ya kai masa gaisuwar ban girma a Gidan Gwamnatin Jihar.

Gwamna Tambuwal ya ce zai tuntubi Sarkin Musulmi da duk masu ruwa-da-tsaki don a tafi tare, saboda jihar ba ta gaggawa a lamarin kamar yadda wasu jihohi suka yi suka kashe tsarin bara ba tare da sun kawo wata mafita ba.

Gwamnan ya nuna ba zai hana bara ba sai ya samar da tsari mai kyau ga harkar almajirci.

Karatun Alkur’ani ake son a lalata a Arewa – Malam Khalid Miga

Wani malami mai makarantar allo ta almajirai a Unguwar Rafin Sanyi a Jihar Jigawa, Malam Khalid Miga ya ce karatun Alkur’ani ake wa zagon kasa ba almajiranci ake son hanawa kai-tsaye ba.

Ya ce magana ta gaskiya kudin da ake cewa almajirai suna samu ta hanyar bara ba bara suke yi ba, suna yin aiki ne ko wanki da guga ko shara ana biyansu a gidajen masu kudi sabanin ma’aikatan gwamnati da suke goge mota ko wanke kayansu su tafi yawon maula.

“Magana ta gaskiya burin gwamnati shi ne su hana mu karatun Alkur’ani. Sun jima suna yunkurin hana mu karatun kur’ani tun zamanin mulkin soja. Amma an kasa hana mu kuma duk wanda ya yi yunkurin hana mu karatun Kur’ani ga shi nan ga Allah.

“Akwai masu cewa Allah uku a kasar nan an bar su suna yin addininsu. Akwai gidajen giya suna sayar da giya ba a hana su ba. Akwai gidajen karuwai ba a hana su ba. Amma mu masu aiki da karatun Alkur’ani aka sama na ido dole sai an hana mu.”