Yadda hana tukin Adaidata Sahu da daddare zai shafi rayuwarmu —  Kanawa

Hanyoyin sufurin da za su maye gurbinsa a lokacin ne babban kalubale

Yadda hana tukin Adaidata Sahu da daddare zai shafi rayuwarmu —  Kanawa

A ranar Litinin ce Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da takaita zirga-zirgar babura masu kafa uku da aka fi dani da Adaidaita Sahu a jihar daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Malam Muhammad Garba, ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 20 ga watan Yuli  2022, kuma ba za su daga wa duk wanda aka kama da karyar dokar kafa ba.

Babban makasudin sanya dokar dai kamar yadda Gwamnatin ta bayyana shi ne tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

A baya dai, an sha samun rahotannin yadda bata-gari ke amfani da baburan wajen aikata laifuka musamman ma kwacen waya, wanda a lokuta da dama ya sha haifar da har kisan kai.

Jami’an tsaro dai sun sha kamawa da daure irin wadannan bata-gari, kuma an sha shirya bitoci da mukaloli kan yadda za a shawo kan wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa.

Wadannan dai na cikin dalilan da suka sanya al’umma suka yi murna da jin wannan doka, duk da a hannu guda kuma suna da ja a kan aiwatar da ita.

Yadda muka ji da dokar — Kanawa

Aminiya ta zanta da wasu mutane maza da mata da ke jigila a baburan Adaidaitan a birnin Kano, sun kuma bayyana mana mabambamtan ra’ayoyinsu game da dokar

Wani ma’aikaci, Yunusa Hausawa ya ce duk da ya ji dadin wannan doka, amma fa za ta kawo masa cikas a dawowarsa daga aiki.

“Kin ga dai ni a asibiti nake aiki, wani lokacin da daren aiki zai kama ni na tafi, ko kuma lokacin zan dawo, kuma ba ni da abin hawa, idan irin haka ta faru irin mu ya za su yi ke nan? Sai dai idan har Gwamnati za ta dawo da motocin Tasi ko wani sufurin. Amma idan ba haka ba ma’aikata za mu cutu,” inji Yunusa.

Ita ma wata baiwar Allah da ta nemi a sakaya sunata ta ce da ita da maigidanta duk ba su da mota, don haka ba ta san yadda za su yi ba idan haihuwa ta zo mata cikin dare.

“Ni yanzu misali tsohon ciki ne da ni, yanzu idan haihuwa ta zo a lokacin da ka hana yawon Adaidata ina muka kama? Gaskiya dai Gwamnati ta samar da mafita kan irinmu kan fara amfani da dokar nan.”

Shi kuwa wani dattijo, Baba Usman ya l ce shi fa yan farin ciki da dokar, domin mutane da dama ya kamata a tuhume su abunda suke bayan karfe goma na dare a waje.

“Matasa da dama bai kamata a ce ma wai suna waje a wannan lokacin ba, ki ga mutum ba aiki yake ba, ya tafi yawon banza ya kai wannan lokacin, da shi da mai dakko shin duk ya kamata a tuhume su ai”, in ji shi.

Yadda direbobin baburan suka ji

Wani direba da muka tattauna da shi ya ce kowanne lamari yana zuwa ne da dadi da kuma akasinsa, kuma a ganinsa dokar don al’umma gwamnati ta yi, don haka fatansa shi ne Allah ya sa ta zamo alheri ga kowa.

Shi ma wani mai suna Murtala Haruna Sule Gwale da ke jan Adaidata Sahun ya ce akwai bukatar Gwamnati ta kara musu lokaci ko zuwa 11:00 na dare ne, saboda daukar masu larura.

“Kowa ya san masu karamin karfi su suka fi yawa a jihar Kano, kuma wannan ce kadai hanyar zirga-zirgar su, idan aka hana masu larura ya za su yi? Ya kamata dai a dan kara wa’adin ko zuwa 11:00 na dare ne,” inji shi.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana mana cewa, “Duk da ni ba na aikin dare sosai, saboda mu ma bata-gari sukan kwace mana babur din a wannan lokacin, amma zan so gwamnati ta kara wa’adin zuwa 11:00 na dare.”

Akwai dai bukatar Gwamnatin jihar ta ji koken al’umma, domin samar musu da mafita kan lamarin, musamman ga ma’aikata, da masu larura, har ma masu juna-biyu.