‘‘Yadda harin bam ya rutsa da mu a Jos’’
A makon da ya gabata ne wasu mata suka kai harin bama-bamai guda biyu a babbar Kasuwar Jos da ake kira Terminus, inda hukumomi suka tabbatar da cewa mutane 35 suka rasa rayukansu kuma mutane sama da 40 suka samu munanan raunuka sakamakon wadannan hare-hare.Aminiya ta gana da Malam Shu’aibu Ali da Hassan Buba na […]
A makon da ya gabata ne wasu mata suka kai harin bama-bamai guda biyu a babbar Kasuwar Jos da ake kira Terminus, inda hukumomi suka tabbatar da cewa mutane 35 suka rasa rayukansu kuma mutane sama da 40 suka samu munanan raunuka sakamakon wadannan hare-hare.
Aminiya ta gana da Malam Shu’aibu Ali da Hassan Buba na daga cikin wadanda suka tsira da ransu kuma suke kwance a asibitin nan na Maternity da ke garin na Jos.
Da yake bayyana yadda abin ya faru, Malam Shu’aibu, dan shekaru 70 ya ce: “Bayan mun yi Sallar Magariba, mun zo za mu shirya kaya mu tashi sai muka ji bam ya tashi a ’yan kasuwar nama. Sai wasu suka tashi da gudu, sai muka ce bari mu yi kokari mu tura kurar da muke kasa kayayyakin da muke sayarwa, mu bar wannan waje. Sai yarona ya ce mu yi kokari mu gudu, mu bar kayan nan. Kafin mu yi wani abu sai muka ji wani bam din ya tashi a gabanmu. Kuma wannan bam da ya tashi a gabanmu, wata mata ce ta zo ta ajiye shi.”
Ya ci gaba da cewa: “To a lokacin da wannan al’amari ya faru sai na kama kurar da nake kasa kaya na rike, na sunkuya kasa. Daga nan sai na ji kafata ta rike, shi kuma yarona mai suna Isiyaka dan shekara 25 da muke tare da shi da abokinsa mai suna Haruna nan take suka mutu. Daga nan kuma sai aka dauko mu zuwa wannan asibiti.”
Shi ma Hassan Buba, mai aiki a kamfanin Nasco da ke garin Jos, wanda ya samu raunuka a sakamakon fashewar bom din, ya ce: “A gaskiya wannan abu ya wuce sanin kowa, sai dai mu yi ta addu’a, Allah Ya tona asirin masu aikata irin wannan mummunan aika-aika. Domin a gaskiya ba daidai ba ne, a ce babu abin da mutum yake so sai dai ya dauki ran dan uwansa.”
Malam Shu’aibu kuwa ya bayyana cewa wannan abu ya fi karfin duk abin da suke tunani a kai. “Wannan abu ana yi ne don azabtar da mu, mu mutanen Arewa. Wadanda ya kamata su yi magana idan sun yi ba a sauraron su. Wannan abu da ake yi mana, wallahi idan da mutanen Kudu ko na Yamma ne ake yi wa haka, da yanzu kasar nan ba a zaune lafiya.”