Yadda harin bam ya yi barna a Somaliya

Akalla mutum 300 ne suka rasa rayukansu sannan sama da mutum 400 suka jikkita a wani mummunan harin ban da aka kai a kasar Somaliya, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana.  Wannan fashewar bam din ya faru ne wani wuri da ba ya rabuwa da cunkuson jama’a, wadda ta lalata otel-otel da ofishoshin gwamnati da […]

Yadda harin bam ya yi barna a Somaliya

Akalla mutum 300 ne suka rasa rayukansu sannan sama da mutum 400 suka jikkita a wani mummunan harin ban da aka kai a kasar Somaliya, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana. 

Wannan fashewar bam din ya faru ne wani wuri da ba ya rabuwa da cunkuson jama’a, wadda ta lalata otel-otel da ofishoshin gwamnati da kuma wurin cin abinci a Mogadishu babban birnin kasar kamar yadda BBC ta ruwaito. 

Ita dai gwamnatin kasar ta dora alhakin harin kan mayakan Al shabaab, kuma wannan ne hari mafi muni tun bayan da kungiyar ta fara tada kayar baya shekaru goma da suka gabata. 

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin tukuna, amma birnin ya saba fuskantar hare-haren kungiyar al-Shabab wadda take yaki da gwamnatin kasar.

Yawan wadanda suka “mutu zai iya ci gaba da karuwa”, kamar yadda wani jami’in dan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP. 

Wannan ne hari mafi muni a kasar tun bayan wani hari da kungiyar al-Shabab ta kai a shekarar 2007. 

Shugaban kasar Mohamed Abdullahi Farmajo ya ayyana kwana uku na makokin wadanda harin ya rutsa da su. 

’Yan sanda sun ce mutum biyu sun mutu a wani hari na biyu a wata unguwa mai suna, Madina wadda take birnin.

An ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su sun taru, suna neman ’yan uwansu a wurin da aka kai harin a safiyar ranar Lahadi, kamar  yadda wata kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

…Wata ta rasu a harin saura kwana daya ta zama likita

Sa’o’i 24 gabanin Maryam Abdullahi ta kammala karatun aikin likita ne harin bam din ya rutsa da ita.

Wata ’yar uwar marigayiyar, Anfa’a, ta shaida wa BBC cewa lamarin ya kidimata “kwarai da gaske.”

“A cewarta “Danginmu sun girgiza sosai, musamman mahaifinmu wanda ya taho Mogadishi daga birnin Landan domin ya halarci bikin yayeta, amman maimakon hakan sai ya halarci jana’izarta.”

Anfa’a ta ce ta yi magana da ’yar uwarta minti 20 kafin tashin bam din.

“A wanna lokacin tana cikin asibitin Banadir Hospital inda take aiki. Ta gaya min tana jiran wasu fayel-fayel daga asibiti.” Daga nan sai ta dauki alkawarin da Ubangiji bai ba ta ikon ciwa ba, “zan kira ki zuwa an jima,” in ji marigayiyar.

Wani wakilin Sashen Somali na BBC a wajen da lamarin ya auku ya ce Otel din Safari ya rufta kuma mutane da dama sun makale a barazugan ginin.

Wani shaida da ke zaune a birnin, Muhidin Ali, ya shaida wa AFP cewa ita ce “fashewa mafi girma da na taba gani, ta daidaita wajen gaba daya”.

Hakazalika, daraktan asibitin Madina Hospital, Mohamed Yusuf Hassan, ya ce matakin harin ya tayar mishi hankali.

“Abin da ya faru jiya ya wuce hankali, ban taba ganin irin wannan ba, mutane da dama sun rasa rayukansu, gawarwaki sun kone kurmus.”

…An birne gawa 165 da ba a gane su ba

A ci gaba da ayyukan ceto a kasar ta Somaliya, gwamnatin kasar ta bayar da umarni a birne gawa kusan 165 da ba gane sub a.

Wasu daga cikinsu sun kone kurmus ta yadda zai yi wuya a gane su, kuma kasar ba ta da bayanan ’yan kasar na zamani a ajiye, don haka ba zai yiwa ba ayi amfani da fasahar DNA wajen gano wadanda suka kone, wanda hakan yasa hukumomi a kasar suka bayar da shawara kawai a birne su a haka.

…Ana neman agajin jini

kasar Somaliya ta yi kira ga kasashen duniya a kan su taimaka mata da agajin jini domin kula da wadanda suka ji raunuka a sanadiyar harin. 

BBC ta ruwaito ministan yada labarai na kasar Abdirahman Osman yana cewa watakila adadin wadanda suka rasu ya sake karuwa kuma ana bukatar karin taimako. 

Turkiya da Djibouti sun tura da ma’aikatan agaji zuwa kasar a ranar Litini kuma jirgin sama sojin Turkiya ya wuce da wasu mutane 40 da suka ji raunuka zuwa kasar domin a yi mu su magani.

kasar Kenya makwabciya ta nuna anniyar kwashe wasu da suka ji raunuka zuwa birnin Nairobi da jirgin sama domin a yi mu su magani. Haka kuma daruruwan mutane sun bada agajin jini.