Yadda Hausawa ke gudun sunayensu na asali zuwa na gargajiyar Larabawa

Shin ko me ya sa Bahaushen yau ke gudun sunayen Hausawa na gargjiya?

Yadda Hausawa ke gudun sunayensu na asali zuwa na gargajiyar Larabawa

Farfesa Abdallah Uba Adamu

An ki cin biri an ci dila, shi ne za a iya kwatantawa da yadda Hausawan wannan zamani suka dukufa da kuma yin rigerigen sa wa ’ya’yansu sunayen Larabawa a maimakon nasu na gargajiya ko kuma na asali, ko da kuwa ma’anar na Larabcin daya ne da na Hausar ko ma na Hausar ta fi shi.

Bahaushen yanzu ba zai sa wa ’yarsa suna ‘Lema’ ba, amma kuma zai rada mata suna ‘Shamsiyya’ kalmar Larabci ta Lemar.

Haka kuma ba zai sa mata suna ‘Kujera’ ba, amma cikin murna da alfahari zai kirata ‘Kursiyya’.

Ni da kaina na ga yarinyar da aka rada mata suna ‘Bakara’ a yayin wata ziyara da na kai wani kauye.

Amma na yi imani idan da za ka kira ta ‘Saniya’ wanda haka sunan yake nufi da Larabci, sai kun kwashi ’yan kallo da ita, har ma da iyayenta watakila.

Farfesa Abdallah Uba Adamu shehun malami a jami’ar Bayero kuma mai bincike da talifi kan Hausa da al’adun Hausawa ya ba da labarin yadda wani abokinsa a wasu shekaru da suka wuce ya yi kokarin rada wa dansa suna ‘Maikudi’, aka hana shi, dole ta sa ya yanka wa yaron ragon suna da Ibrahim domin ya zauna lafiya da magabatansa.

Sai dai da yake kasancewar sunan da aka tilasta masa rada wa dan sunan surunkinsa ne, dole aka ci gaba da kiransa Maikudi, a matsayin alkunya.

Hakan kuma ta sake faruwa a lokacin da ya haifi ’ya mace, ya kuma bayyana sunanta ‘Tabawa’, nan ma aka yi ca a kansa, dole abokin nasa ya rada mata suna ‘Hajara’, sannan ya samu lafiya.

Amma kuma kamar haihuwar farko, sunan ba zai fadu a gidan ba, sai da alkunya, dole aka koma kan sunan Tabawa da ya bayyana tun farko ba don ana so ba.

Koda yake wannnan lamari ya faru shekara kimanin 40 da suk wuce, kamar yadda shehun malamin ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook, amma har yanzu ba ta sauya zani ba, sai ma ta’azzara da hakan ya yi a yanzu, domin idan a wannan lokaci ne, lakabin da za a sa wa wadannan ’ya’ya, ba shakka na Larabawa za a yi nutso a cikin wasu daddadun sunayen gargajiya da kuma kakale a kakaba musu da kuma tunkaho da alfahari.

Shin ko me yasa Bahaushen yau ke gudu ko yake kyamar sunayen Hausawa na gargjiya?

Bahaushen yau zai ki sunan ‘Maikudi’ ko ‘Wada’ ko kuma ‘Goshi’, amma da gudu zai sa wa dansa ‘Yassar’ wanda ke nufin Yalwa ko ‘Kamal’ wanda za iya fassara shi da dattako ko ‘Fahad’ wanda ke nufin Damisa ko kuma ‘Anwar’ wato Haske da Larabci.

Amma fa da zai sa wa dansa daya daga cikin sunayen nan da ma’anarsu ta Hausa da sai ya rasa inda zai sa kansa.

‘Tabawa’ dai na nufin kololuwar budi ko nasara, yayin da kuma a wani waje yake nufin ’yar da aka haifa ranar Talata.

Bahaushen yau zai kyamaci wannan suna, amma zai sa wa ’yarsa ‘Mahjuba’ (abin da yake a lullube) ko kuma ‘Samira’ (Ma’abociyar dare) a cewar Farfesan.

Idan ka sa wa ’yarka suna ‘Dare’ a yanzu ka shiga uku. Idan ba ka yi sa’a ba, sai wasu sun fitar da kai daga Musulunci.

Amma ka kira ta ‘Laila’ da Larabci sai ka zauna lafiya, watakila ma har da yabo da jinjina.

“Suna,” in ji masu iya magana, “linzami ne,” hakan kuma ta bayyana a karshen bayanin Farfesan a rubutunsa, inda ya ce, ’ya’yan abokin nasa sun amsa sunayen nasu a rayuwa, domin sun samu tagomashi da kuma budi baya ga zama abin misali a rayuwrsu ta yanzu.

Maikudi ya zama hamshakin dan kasuwa wanda kasuwancin nasa ya sa ya tare kacokam a kasashen Gabas ta Tsakiya.

Yayin da Tabawa kuma ta kai matsayin karatun digirin digirgir, take kuma koyarwa a jami’a.

Ma’ana, “fata nagari” kamar yadda sunayen na Hausawan ke nuni, “lamiri ne,” kamar dai yadda muke sa wa ’ya’yanmu sunayen Annabawa da kuma manyan bayin Allah don neman tubarraki.

Gaskiyar magana ita ce, yayin da Bahaushen yanzu ke gudun maguzanci a sunaye, yawancin sunayen da Hausawa kuma Musulmi ke sa wa ’ya’yansu, ba su da alaka da Musulunci.

Domin wasunsu na maguzawan Larabawa ne. Masu amsa wadannan sunaye da kuma iyayen da suka sa musu, yawancinsu ba su san ma’anarsu ba.

Saboda aron da suka yi suka kuma yafa. Ko kuma in ce, fin mai kora shafawa.

Dangane da wannan, Farfesan shi da wani abokin bincikensa Abdulrazzak Ahmed Muhammad-Oumar sun gudanar da wani bincike kan ainihin sunayen Hausawa da kuma ma’anoninsu.

A cewarsa, binciken ya dauke su tsawon shekara 10 suna yi, daga karshe suka fito da jerin wasu sunaye 1001.

Sunayen zunzurutun na gargajiyar Bahaushe ne, kuma na asali wadanda ba su da alaka da maguzanci da kuma surkulle.

Wasu da yawa daga cikinsu sunayen Annabawa ne da Bahaushe ya Hausantar da su.

Misali; sunan ‘Guruza’ daga Ahmad ne, ‘Da’u’ Dauda ke nan, ‘Gagare’ kuwa alkunya ce ta Bahaushe ga mai suna Abubakar, haka ma ‘Auwa’ Hauwa ke nan, ‘Daso’ Maryam ce, ‘Babuga’ Umar ne da kuma ‘Ilu’ daga Isma’il.

Baya ga wannan, Hausawa bisa al’ada na rada wa ’ya’yansu sunaye bisa faruwar wasu abubuwa a rayuwarsu ko kuma a mu’amala ta yau da kullum, sukan kuma rada musu sunan bisa faruwar wasu al’amura ko kuma yanayi abin tunuwa.

Misali, ‘Abarshi’ dan da aka haifa bayan bari ne ko kuma an haifi wasu kafin shi duk sun mutu.

‘Shekarau’ na nufin wanda ya dade a ciki, yayin da ‘Gudaji’ ko ‘Tanko’ na nufin wanda aka haifa a tsakiyar ’ya’ya mata.

Sakamakon binciken na wadannan jerin sunaye 1001 da Farfesan ya fitar, ya karkasa su rukuni-rukuni kuma dakidaki a cikin jadawali.

Sannan kuma suka saka shi a Intanet fisabilillahi ga duk mai bukata don fadada ilimi ko kuma ga mai son ya san yadda sunansa ko na abokinsa ya samo asali a Hausa.

Ko kuma ga wanda ke son jarraba daya daga cikin sunayen ga jaririnsa.

Ni ma wannan rubutu tsakure ne daga dogon bayanin da Farfesa ya yi a Facebook.

Ga duk mai sha’awa zai iya shiga wannan rariyar ta Intanet inda zai sauko da jerin sunayen.

Allah Ya saka wa Farfesa Abdallah da kuma Abdulrazzak Ahmed Muhammad-Oumar da wannan jan aiki na adana tarihi da kuma al’adun Hausawa.

Ga rariyar sauko da sunayen: https://bit.ly/42HJI97

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025