Yadda Hausawa suka zama ’yan kasa a birnin Ikko,

Ga dukkan alamu, Hausawa da ake wa ganin su baki ne ’yan ci-rani a birnin Ikko da ke tsakiyar Jihar Legas, lamarinsu yana canjawa saboda ganin irin yawansu da kuma karfin tattalin arzikin da suka samu a jihar.Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa yanzu Hausawa na sayen gidaje da filaye suna yin […]

Yadda Hausawa suka zama ’yan kasa a birnin Ikko,

Daga hagu Alhaji Muktar Alin Magaji ne da Manjo Ali Daba ritaya da Alhaji Rabi’u Abubakar da Hajiya Hauwa Abubakar da kuma Hajiya AsabeGa dukkan alamu, Hausawa da ake wa ganin su baki ne ’yan ci-rani a birnin Ikko da ke tsakiyar Jihar Legas, lamarinsu yana canjawa saboda ganin irin yawansu da kuma karfin tattalin arzikin da suka samu a jihar.
Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa yanzu Hausawa na sayen gidaje da filaye suna yin gine-gine na zamani a jihar, ba kamar da ba da suke cewa su ba zama suka zo yi ba a jihar.
Wata dattijuwar Bahaushiya da iyayenta suka haifa a Legas, kimanin shekara 83 da suka gabata, mai suna Hauwa Abubakar, wanda ake yi wa lakabi da Baban Nuhu, ta bayyana cewa Hausawa sun dade a jihar Legas tun shekaru aru-aru. “A lokacin da muke kanana, muna zaman lafiya da Yarabawa, muna hulda ta zumunci da su, mukan ba su abinci su dafa mana, sukan ci abincinmu, mu ma mukan ci nasu, ba tare da nuna wani bambanci ko rashin yarda ba”.
Ita kuma Hajiya Asabe, wacce aka haifa a Legas shekaru fiye da 60 da suka wuce ta bayyana cewa iyayenta ma duk a Legas din aka haife su.
Ta bayyana cewa rike al’ada da addini da Malam Bahaushe ya yi shi ya sa Yarabawa suke girmama shi. “Tunda mu iyayenmu ba su bar al’adarsu ta kasar Hausa ba, shi ya sa a lokacin ba sa saka mu a makarantun boko na Yarabawa, sai dai makarantar allo don gudun kada mu yi watsi da al’adarmu. Idan za mu yi biki da suna duk irin namu muke yi. Shi ya sa muke da daraja a wurin Yarabawa. Daga baya ne muka ga abin ya shiririce kuma abin da ya janyo haka shi ne barace-barace da Hausawa suka fara daga bisani, har sai da ta kai Yarabawa suna kiranmu ’ya’yan mabarata”. Inji ta.
Alhaji Muktari Alin Magaji,  mai kimanin shekaru 60, ya bayyana cewa Hausawa sun taka rawar gani wajen bunkasar tattalin arzikin birnin Ikko da Jihar Legas baki daya. “Iyayenmu sun taimaka wajen bunkasar birnin Ikko ta hanyar yin sana’o’i iri-iri, kamar sana’ar sayar da kayan gargajiya da harkar shinkafa da kayan gwari da sana’ar fawa. Wadannan sana’o’i ne na yau da kullum, wadanda suke bunkasa kasuwa da tattalin arzikin jama’a”.  Inji shi.
Ya kara da cewa, “Kakannina sun zo Legas fiye da shekaru dari da suka wuce. Sun yi gidaje, sun zauna a wurin tamkar ’yan kasa, sun aura, an aurar musu, sun haifi ’ya’ya da jikoki da tattaba kunne”.
Shi kuwa Manjo Ali Daba, mai ritaya, mai shekaru 68, ya bayyana cewa nuna halin dattaku da gaskiya da rikon amana ya sa Hausawa suka sami karbuwa a Jihar Legas. “Akidar Malam Bahaushe ta riko da addini shi ya sa ya sami karbuwa a Jihar Legas. Shi Bahushe babu yadda za a yi ya yi watsi da al’adarsa da addininsa duk inda ya je”. Inji shi.