Yadda hidimar gida ba ta hana mata sana’ar dinkin hannu a Zariya
Kasar Zazzau ta yi fice wajen samar da rigunan ado irin na sarauta.
Addini da al’aladun Bahaushe sun dora wa mata wasu hidindimu na raino da kula da yara da sauran wasu hidindimun yau da kullum a gidajensu, amma hakan bai hana matan aure da zawarawa da ’yan mata su tsunduma cikin sana’ar dinkin hannu ba a Zariya.
Zariya ta yi fice wajan samar da dinkunan aiki hannu, irin na Hausawa da suka kunshi dinkin kayan sarauta, limanci da malanta da ma sauran rigunar da Malam Bahaushe ke sawa a yau da kullum.
- Dalilin da aka mayar wa Juventus makinta 15 da aka zaftare
- An kashe Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali
Aikin hannu sana’a ce da maza ke yi a sauran biranen Hausawa, amma a birnin Zariya mata ma sun tsunduma a cikin sana’ar dinkin hannun don sama wa kansu abin dogaro da biyan bukatunsu na yau da kullum.
A zantawarsu da wakilinmu wasu mata da suka rungumi wannan sana’a ta dinkin hannu, irin su Malama Amina Lamido wadda matar aure ce kuma take sana’ar dinkin hannu a cikin birnin Zariya, ta ce tana da yara bakwai.
Ta ce ta kwashe akalla shekara 30 tana sana’ar, domin tun tana ’yar shekara 10 ta fara koyon sana’ar a wajen mahaifanta.
Amina ta ce sana’ar ta rufa mata asiri domin da abin da take samu take sayen kayan bukatunta na yau da kullum, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.
Malama Murjanatu Kabir cewa ta yi a gaskiya sana’ar ta sa tana zaune lafiya a gidan mijinta domin ba ta da lokacin yin hira ko hayaniya, don haka ko wannan natsuwar da dinkin hannu ya samar mata ta ci gajiya da kuma amfanar sana’ar.
Murjanatu uwar ’ya’ya biyu, ta ce duk da hidimar gidan aure da kula da yara, hakan bai hana ta gudanar da wannan sana’a ba, domin ko gidan biki za ta je da sana’arta take tafiya.
Ita kuwa Safiya Gazali wacce daliba ce, kuma take jiran mijin aure, ta ce sana’ar dinkin hannu gado ta yi a wajen iyayenta, kuma tana alfahari da ita.
Ta ce ko da bukatar makaranta ita take yi wa kanta da sauran bukatun rayuwa.
Sai ta shawarci ’yan uwanta dalibai su yi kokari su koyi sana’a don samun abin biyan bukata ba tare da suna jiran a ba su ba.
Matan da wakilinmu ya tarar suna ta sana’arsu a wuri daya sun ce suna yin haka ne don su karfafa wa junansu kan ci gaban sana’ar tasu kamar yadda suka shaida masa.
Sun ce karamin aiki a cikin aikace-aikacen da suke samu kudinsa bai gaza Naira 5,000 zuwa 7,000 amma akwai wanda yakan kai har Naira dubu 20 zuwa sama.
Sai dai kuma sun ce idan mace daya de, za ta yi sai ta kwashe kusan wata biyu tana yi.
Kamar yadda ya gabata, Kasar Zazzau ta yi fice wajen samar da rigunan ado irin na sarauta da Hawan Sallah da angwanci da sauransu.
Kuma mata na daga cikin masu samar da irin wadannan riguna kamar, Shafka da Tokare da Aska Biyu da ’Yar Bayero da ’Yar Dikwa da Zubuni da Kufta da Al-kyabba da sauransu.