Yadda hukuma ta kama masu gurbata manja
Babbar Kasuwar Potiskum ta shiga cikin rudani sakamakon samame da Hukumar Tabbatar da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) da kuma jami’an Hukumar NCDSC suka kai domin kama wadansu batagari da ake zargi da gurbata manja da lauinin Jawa domin sauya wa manjan launi.Wannan lamari ya tayar da hankalin jama’a musamman bayan da aka […]

Babbar Kasuwar Potiskum ta shiga cikin rudani sakamakon samame da Hukumar Tabbatar da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) da kuma jami’an Hukumar NCDSC suka kai domin kama wadansu batagari da ake zargi da gurbata manja da lauinin Jawa domin sauya wa manjan launi.
Wannan lamari ya tayar da hankalin jama’a musamman bayan da aka tabbatar da cewa launin na Jawa yana haifar da ciwon daji (cancer) da ciwon koda.
Shugaban Hukumar NCDSC na Jihar Yobe, Malam Kabir Gambo ya tabbatar wa Aminiya cewa sun kama wadanda ake zargi da gurbata manja ne sakamakon ziyarar ba-zata da hukumar ta kai kasuwar domin tantance launukan manja da ake sayar wa mabukata. “Yaranmu sun lura cewa ana sayar da manja mai launi daban-daban a cikin kasuwar, wannan ya sa muka yi zargin ana iya samun gurbatacce. Sai muka samu samfur din kowane daga ciki, muka kuma gabatar da shi ga Hukumar NAFDAC domin bambance ingantacce da gurbatacce ta hanyar amfani da na’ura.”
Malam Kabiru ya ce, bayan mako biyu da gabatar da samfurin manjan sai Hukumar NAFDAC ta fitar da sakamako cewa guda daya ne tak ba a yi wa algus da wani sinadari da ake kira Dye color, wato Jawa ta yin rini. Kuma sun tabbatar da cewa wannan launi yana kunshe da wani sinadari mai haddasa cutar daji da ciwon koda.
Shugaban ya kara da cewa hukumomin biyu sun kai samame a kasuwar, inda suka yi nasarar kama masu safarar gurbataccen manjan wanda hakan ya haifar da kulle shagunansu domin hana ci gaba da yaduwarsa da kuma gudanar da ingantaccen bincike. Ya ce ba za su bayyana sunayen wadanda ake zargin ba, domin kada hakan ya kawo nakasu ga binciken da suke gudanarwa.
Da wakilin Aminiya ya tuntubi Ko’odinetan Hukumar NAFDAC a jihar, Lawan Musa Dadingelma ya tabbatar masa cewa akwai sinadarin Jawa a cikin manjan da suka tantance, wanda kuma yana da matukar illa ga rayuwar dan Adam.
Ko’odinetan ya kara da cewa wadanda ake zargin sun tabbatar wa hukumar cewa suna amfani da sinadarin a cikin manjan, amma suna samunsa ne daga Galadimawa da ke Kano. Ya kara da cewa hukumar tana ci gaba da bincike kan sauran kayan masarufi da suka hada da kifi da wake da ayaba da kuma zuma da ake zargin ana gurbata su ta amfani da maganin kashe kwari ko sinadarin da ke hana su rubewa, wanda hakan na haifar da illolin ga lafiyar jama’a.
Shugaban Asibitin kwararru na Sani Abacha da ke Damaturu, Dokta Garba Fika ya ce tabbas akwai karuwar mutane da ke dauke da ciwon daji a Yobe amma ba zai iya cewa kai-tsaye sun same shi ne sakamakon cin gurbataccen manja ba. Ya ce launin na Jawa na iya haddasa ciwon daji sakamakon sinadarin Carcinogen da yake dauke da shi. “Dalili kuwa, sinadarin na taruwa ne a jikin dan Adam a hankali har ya kai mizanin da zai cutar da shi, ta hanyar sanya masa ciwon daji a koda ko sassan jiki,” inji shi
Ya ya kira ga duk wanda yake ci gurbataccen manja ya je asibitin kwararru da suke da da kayan gwaji domin tabbatar da yanayin lafiyarsa. Kuma ya bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta daukar mataki a kan lamarin tun kafin ya girma ya haifar da wata sabuwar matsala.
Shugaban Masu Sayar da Manja a Kasuwar Potiskum, Malam Alaramma Mai-Manja ya yi Allah wadai da masu yin wannan algus a cikin abokan kasuwancinsu. Ya tabbatar da cewa ba za su yarda ba a matsayinsu na shugabanni su ga ana cutar da mutane ba.
“Suna kara wa manjan launin Jawa ne domin kiran kasuwa da cin kazamar riba, ba tare da tunanin mawuyacin halin da za su jefa mutane ba,” inji shi.
Ya yi alkawarin cewa za su tsaya wajen ganin an hukunta duk wanda aka kama a cikin harkar algus din.