Yadda hukumar NABDA ta yi wata biyu babu shugaba

Wata majiya daga hukumar bunkasa kimiyya ta kasa ta NABDA ta bayyana wa Aminiya cewa hukumar da ke karkashin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta shafe kimanin watanni biyu ba tare da shugaba ba saboda Minista, Dokta Ogbonnaya Onu yana son a hada mutumin da ke da kashi a gindi.   Aminiya ta gano cewa sakamakon […]

Yadda hukumar NABDA ta yi wata biyu babu shugaba

Wata majiya daga hukumar bunkasa kimiyya ta kasa ta NABDA ta bayyana wa Aminiya cewa hukumar da ke karkashin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta shafe kimanin watanni biyu ba tare da shugaba ba saboda Minista, Dokta Ogbonnaya Onu yana son a hada mutumin da ke da kashi a gindi.
 
Aminiya ta gano cewa sakamakon saukar da shugaban wucin gadi na hukumar, Farfesa Lucy Ogbadu ya yi sakamakon wata badakala da ta auku a watan Nuwamban da ya gabata, Dokta Onu ya baiwa sakatariyar hukumar ta dindindin, Dokta Amina Bello Shamaki ta nada babban daraktan fasaha na hukumar, Farfesa Alex Akpa a matsayin daraktan hukumar na wucin gadi.
 
Wata majiya ta tseguntawa Aminiya cewa sakatariyar dindindin ta baiwa ministan shawara cewa nadin Farfesa Alex yana da hadari saboda laifukan da ake zargin ya aikata.