Yadda hukumomin gwamnati suka salwantar da tiriliyan 3.8 a mulkin Buhari —Rahoto

Ofishin Akanta-Janar ya rika tura musu kudaden ba tare sun nema ba a hukumance

Yadda hukumomin gwamnati suka salwantar da tiriliyan 3.8 a mulkin Buhari —Rahoto

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Majalisar Dattawa ta bankado yadda hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya suka salwantar da Naira tiriliyan 3.8 a ciki shekara hudu a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Binciken da Kwamitin Asusun Gwamnati na Majalisar ya gudanar ya gano cewa hukumomi da ma’aikatu sama da 200 ne suka salwantar da wadannan kudade daga shekarar 2017 zuwa 2021.

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide, ya ce kudaden da aka salwantar an tanade su ne domin bukatun da ka iya tasowa a hukumomin da ma’aikatun.

Sanata Urhoghide ya bayyana cewa hukumomin da ma’aikatun sun, “rika karɓar daruruwan biliyoyi da suna kudin biyan ginin albashin ma’aikata, alhali kuwa a cikin kasafin kudi an riga an ware kudaden biyan hukumomin albashin ma’aikatansu, har an tura a tsarin albashi na IPPIS.

“An rika tura musu makudan kudade da ba su nema ba a hukumance, wani lokaci ma ba su san dalilin tura musu kudaden ba, ballantana asalin kudaden.”

Ya ce kwamitinsa ya gayyaci hukumomi da ma’aikatu 207 domin amsa tambayoyi a kan badakalar, amma guda 119 daga cikinsu ne kawai suka amsa gayyatar.

Da yake gabatar da rahoton kwamitin da aka amince da shi a zaman Majalisar na ranar Laraba, Sanata Urhoghide, ya bayyana cewa yawancin hukumomin sun karbi kudaden ne ba tare da tuntubar kwamitin majalisar da doka ya ba wa alhakin kula da ayyukansu ba.

Wasu daga cikinsu ma, Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa ya tura musu kudaden ba tare da sun rubuta takardar bukatar kudaden ba a hukumance.

Wadanda suka nema suka kuma samu izinin shugaba kasa na tura musu kudaden kuma, sun karkatar da kudaden zuwa wasu ayyuka mara alaka da dalilin fitar da kudaden.

Sanata Urhoghide ya bayyana cewa wasu daga cikin hukumomin kuma, sun karbi kudaden da aka rika aka ware a kasafin kudadensu tsawon shekaru.

Ya kara da cewa an wofintar da tanadin da tsarin IPPIS ya yi domin cike gibin da aka samu wajen biyan hakkokin ma’aikata, wanda hakan ke jawo zurarewar makudan kudaden gwamnati da ke bukatar majalisa ta dauki mataki a kai.

Daga cikin ma’aikatun akwai: Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa da ma’aikatar Tsaro da ta ’yan sanda da ta man fetur da ta Harkokin Waje da ta cikin gida da ta sufuri da ta lafiya da ta ayyuka da gidaje da ta yada labarai da ta sufurin jiragen sama da ta yada labarai da ta ma’adinai, da ma’aikatar wasanni.

Hukumomin sun hada da: Fadar Shugaban Kasa, Ofishin Kasafin Kudi, Ofishin Kula da Jiragen Fadar Shugaban Kasa, Rundunar Sojin Kasa, Sojin Ruwa da Sojin Sama, Hukumar Leken asiri da Hukumar tsaro ta Civil Defence.

Akwai kuma hukumar NAFDAC mai kula da ingancin abinci da magunguna, Hukumar agajin gaggawa ta (NEMA), Shirin Afuwa ga tsagerun Neja Delta,  Hukumar kula da tituna, ofishin kula da basuka, Hukumar INEC da hukumar inshorar lafiya da hukumar jarabawar NECO da sauransu.

Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Sakkwato – Sojoji

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja