Yadda iyaye ke zuwa kasuwa don neman mai auren ’ya’yansu
Iyaye na rubuta bayanan ’ya’yansu a kan allon talla ko za su samu mai so.
Matsalar rashin miji ko matar aure ta kai makura ta yadda iyaye ke zuwa kasuwanni suna tallata ’ya’yansu don nema musu miji ko mata.
Duk da cewa masu neman aure da dama a sassan duniya na fuskantar kalubalen samun irin miji ko mata da ta dace da zabinsu – saboda dalilai daban-daban – yanayin girmar wannan matsala a kasar China ya wuce misali.
- Tsananin neman mijin aure ya sa tana tallar kanta a titi
- Idan na samu aikin gadi zan bar kasuwanci — Matashi
Hakan ne ya sa aka kafa ‘kasuwannin neman aure’ a biranen Shanghai da Beijing da wasu yankunan kasar, inda iyaye ke zuwa su tallata ’ya’yansu maza da mata da suke son aurarwa.
Yadda ake cin kasuwar
A kowace ranar Asabar da Lahadi mutane na yin tururwar halartar kasuwannin neman auren da aka fara kafawa a 2004 a yankunansu ko unguwanninsu.
Iyaye da kakanni sukan halarci wadannan kasuwanni ne musamman domin nema wa ’ya’yansu mata ko mijin aure da ya dace da su. A wani lokaci ba tare da sanin ’ya’yan ba.
A kasuwar neman aure da ke dandalin People’s Park a birnin Shanghai da ire-irensa a birnin Beijing da sauran wurare, da suka damu saboda rashin auren ’ya’yansu sukan tallata ’ya’yan nasu ne ko za su dacen sama musu irin abokan zama da ake so su aura.
Salon tallar marasa aure
A kasuwannin, iyaye sukan samu takarda su zayyana irin nagarta da dacewar da suke ganin ’ya’yansu na da su a matsayin mazaje ko matan aure ko surukai, gami da irin nagartar da suke bukata daga mai son auren ’ya’yan su, sannan su lika takardar a jikin allon talla.
Masu cin kasuwar neman auren za su rika bin allunan suna karanta ire-iren wadanda ake tallatawa da irin nagartar da ake bukata daga manema domin zabo irin miji ko matar da ’ya’yansu za su aura – wato surukansu.
A wani lokaci kuma sukan lika takardar tallar a jikin lemarsu, sannan su ajiye lemar, mutane su rika zuwa suna karanta; Zuwa wani lokaci kuma sai su sauya wuri, har zuwa lokacin da za a dace.
Idan har aka yi sa’ar cin karo da bayanin wadanda suka dace, sai iyayen kan tattauna a tsakaninsu, sannan idan sun daidaita sai su tsara yadda ’ya’yan nasu za su hadu da juna.
Abubuwan da ake dubawa:
Wani bincike da aka gudanar a kasuwar neman aure ta birnin Shanghai a 2018 ya nuna daga cikin irin nagartar da ake tallatawa na mata na maza a kasuwar neman aure sun hada da:
Shekaru:
Yawancin manema auren da ake tallar su a kasuwannin masu shekaru 25 zuwa 30 ne.
Maza sun fi son matan da ba su kai su shekaru ba, mata kuma sun fi son namijin da bai girme su sosai ba.
Matakin ilimi:
Matakin aiki da na ilimi na daga cikin bayanan da yawancin takardun tallar neman aure ke kunshe da su.
A cikin kowadanne takardun neman ma’auri uku, mutum biyu na da shaidar karatun matakin digirin farko.
Yawancin mata sun fi son auren mazan da matakin iliminsu daya, maza kuma sun fi son matan da ba suka gaza su zurfin ilimi da kadan.
Karfin aljihu:
Akwai kuma batun karfin aljihu da irin kadarorin da wanda za a aura ya mallaka.
A bisa tsarin, an fi so namiji ya mallaki gida da mota kafin ya yi aure; Saboda haka masu halin sama wa mace gida da mota sun fi saurin auruwa.
Dacewa da juna:
Ana kuma la’akari da dabi’un manema auren ta hanyar camfin Canisawa da kuma ilimin taurari – wadanda duk ake bayyanawa a takardun tallar mata da mazajen.
A bisa abin da suka yi amanna, da hakan ake iya tantance dacewar mutanen juna ta hanyar la’akari da lokacin haihuwarsu, da taurarinsu, da sauran abubuwansu na camfe-camfe.
Matsalar karancin mata a China:
Kasar China na fama da karancin mata, inda yawan mazan kasar ya zarta na mata na akalla miliyan 30, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.
Ana danganta matsalar da abubuwa da dama, cikin har da tsohon tsarin kasar na kayyade haihuwar da daya daga 1979 zuwa 2017.
Wata matsalar kuma ita ce dabi’ar mutane ta son haihuwar ’ya’ya maza fiye da ’ya’ya mata, wanda a wasu lokuta suke zubar da cikin ’ya’ya mata.
Akwai kuma dabi’ar kin aure a da wuri a tsakanin mata matasa masu zurfin ilimi da masu samun albashi mai kauri.
Irin wadannan mata sun fifita aikinsu a kan yin aure da wuri, gami da wasu hanyoyi da suke bi na samun biyan bukata ta bayan fage.
Duk da haka ana goranta wa matan da suka doshi shekara 30 babu aure ba a kasar, har ana kiran su da shèngnǚ (ragowar mata).
A kasuwannin neman aure, matan da suka doshi shekara 30 ba su fiye yin kasuwa ba, saboda haka ba su da zabi sosai.
Hasali ma wani lokaci sai dai su hakura da irin ma’aurin da suka samu ya taya su.