Yadda jadawalin FIFA Club World Cup na bana ya kasance
A wannan makon ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ta fitar da jadawalin gasar FIFA Club World ta baɗi da aka faɗaɗa. Za a yi fafatawar wasannin FIFA Club World Cup da aka faɗaɗa zuwa ƙungiyoyi 32 a Amurka tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli a shekara mai zuwa. Firimiya: […]
A wannan makon ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ta fitar da jadawalin gasar FIFA Club World ta baɗi da aka faɗaɗa.
Za a yi fafatawar wasannin FIFA Club World Cup da aka faɗaɗa zuwa ƙungiyoyi 32 a Amurka tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli a shekara mai zuwa.
- Firimiya: Liverpool ta ci gaba da jan zarenta bayan doke Man City
- Van Nistelrooy da Lampard sun samu aikin horaswa a Ingila
An fitar da jadawalin ne a wani taro da aka yi a wurare biyu a birnin Miami kuma an kwashe sama mintina 90 ana gudanar da shi, yayin da aka nuna sabon gasar da za a ci gaba da amfani da shi.
Jami’an kulub-kulub da tsaffin ‘yan wasa sun taru domin fitar da jadawalin a birnin Miami sannan Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya aike da sakon fatan alheri ta bidiyo gabanin fara bikin.
Gwarzuwar da ke riƙe da kofin FIFA Club World Cup, Manchester City za ta fafata a matakin rukuni da Juventus, yayin da Chelsea za ta yi nata wasa da Flamengo ta Brazil.
Pep Guardiola wanda ya yi nasarar doke Fluminense ta Brazil ya ci kofin a 2023 karon farko a tarihi, zai fara wasa ne da Wydad ta Morocco da kuma Al Ain ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a rukunin G.
Chelsea wadda ta lashe gasar a 2021, tana cikin rukuni ɗaya da ƙungiyar Mexico Leon da ƙungiyar Esperance Sportive de Tusisie a rukunin D.
Ƙungiyar Inter Miami inda Lionel Messi ka taka leda za ta haɗu da takwararta ta kasar Masar, Al-Ahly yayin bude gasar a ranar 15 ga watan Yuni mai zuwa, kamar yadda jadawalin gasar da aka bayyana a ranar Alhamis.
An sanya kungiyar Palmeiras ta kasar Brazil da takwararta ta kasar Portugal Porto a rukunin “A” tare da kungiyar Inter Miami ta jagoran cin kofin duniya dan kasar Argentina Messi wanda FIFA ta bata gurbi bayan da ta yi zarra a gasar MLS ta wannan kakar.
Dan tsohuwar ƙungiyar Messi ta Barcelona, ɗan asalin Brazil, Neymar, zai sake haɗuwa da abokan dabinsa na gasar La Liga kuma zakarun nahiyar Turai Real Madrid a rukunin “H”.
Kungiyoyin nahiyar Turai 12 ne za su fafata a gasar inda Manchester City za ta hadu da Juventus a rukunin “G”.
An sanya kulub din PSG a rukuni mai zafi tare da Atletico Madrid da ƙungiyar Botafogo da ta lashe gasar Copa Libertadores ta ƙasar Brazil da kuma Seatle Sounders.
Za a buga wasan ƙarshe na gasar a filin wasa na Metlife da ke New Jersey a ranar 13 ga watan Yuli mai zuwa.
Jadawalin FIFA Club World Cup na 2025
Rukunin A: Palmeiras, FC Porto, Al Ahly, Inter Miami
Rukunin B: Paris St-Germain, Atletico Madrid, Botafogo, Seattle Sounders
Rukunin C: Bayern Munich, Auckland City, Boca Juniors, Benfica
Rukunin D: Flamengo, Esperance Sportive de Tunisie, Chelsea, Club Leon
Rukunin E: River Plate, Urawa Red Diamonds, Monterrey, Inter Milan
Rukunin F: Fluminense, Borussia Dortmund, Ulsan, Mamelodi Sundowns
Rukunin G: Manchester City, Wydad, Al Ain, Juventus
Rukunin H: Real Madrid, Al Hilal, Pachuca, Salzburg