Yadda jagororin hamayya ke rantsar da kansu a matsayin shugabanni a Afirka

A ranar Talata ne jagoran ‘yan hammayya na kasar Kenya Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, bayan da ya sha kaye a zaven da aka sake gudanarwa a watan Oktobar bara. Ba wannan ne dai karo na farko da wani ya tava rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa ba a […]

Yadda jagororin hamayya ke rantsar da kansu a matsayin shugabanni a Afirka

A ranar Talata ne jagoran ‘yan hammayya na kasar Kenya Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, bayan da ya sha kaye a zaven da aka sake gudanarwa a watan Oktobar bara.

Ba wannan ne dai karo na farko da wani ya tava rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa ba a nahiyar Afrika bayan shan kaye a zave.

BBC ta rairayo jerin mutanen da suka tava kokarin rantsar da kansu a matsayin shugabannin kasa a nahiyar.

A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo akwai Etienne Tshisekedi da Moshod Abiola a Najeriya, da Kiza Besigye na Uganda, da kuma Jean Ping na Gabon.

Wadannan na daga cikin jagororin hamayya na kasashen Afirka wadanda suka yi kokarin ayyana kansu a matsayin shugabannin kasashensu, bayan kuma a lokacin kasashen suna da shugabanni da ke kan kujera. A ranar talatar nan Raila Odinga, shugaban ‘yan hamayya na Kenya ma ya bi layin wadannan ‘yan siyasa. 

A Uganda jagoran ‘yan hamayya na kasar Dokta Kizza Besigye, wanda ya dade yana adawa da Shugaba Yoweri Museveni, ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, inda aka nuna bidiyon rantsuwar da aka yi a wani wuri na sirri a shekarar 2016, kwana daya kafin rantsar da Museveni. 

Daga baya an kama shi aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa, inda aka rika gurfanar da shi a gaban shari’a.

Etienne Tshisekedi shi ne shugaban ‘yan hamayya a lokacin mulkin Shugaba Mobutu Sese Seko na Zaire, kasar da shi kuma Laurent Kabila ya sauya wa suna zuwa Jamhuriyra Dimokuradiyyar Congo wato DRC, daga baya kuma har zuwa yanzu ta kasance karkashin dansa Joseph Kabila. 

Wata kamanceceniya tsakanin Tshisekedi da Odinga ita ce, dukaninsu an tava tsare su ba tare da an yi musu shari’a ba, sannan kowanne cikinsu ya tava zama Firay minista, kuma duka sun kaurace wa zaven shugaban kasa; Tshisekedi a 2006 sannan Raila a 2017. 

A watan Nuwamba na shekarar 2011, Tshisekedi ya yi takara inda ya kalubalanci dan Laurent Kabila kuma ya zama na biyu a zaven. Daga nan sai ya shirya karbar rantsuwa a matsayin shugaban kasa, a wani biki da ya shirya a garinsu karkashin shugaban ma’aikatansa Albert Moleka bayan da kokarin ganin an rantsar da shi a filin wasa na Martyr a babban birnin kasar, Kinshasa ya ci tura. Shi ma daga bisani an yi masa daurin talala a gidansa.

A Najeriya, Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa lokacin Sani Abacha na kan mulki. Ya yi hakan ne bayan da ya ziyarci kasashen Turawa na yammacin duniya, yana neman goyon bayansu a kan gwamnatin Abacha. An kama shi aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa, sannan aka yi masa daurin shekara hudu, zuwa shekarar1995. 

A 2016 a Gabon, shugaban ‘yan adawa Jean Ping ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, kuma ya bukaci da a sake kirga kuri’un zaven shugaban kasar, kirgen da aka sake yi ya tabbatar da Shugaba Ali Bongo mai ci a matsayin wanda ya yi nasara. sai dai duk da haka, Ping ya kafe yana cewa, ‘’ai duk duniya ta san shi ne shugaban kasar.”