Yadda jahiltar cutar rudewa ke illa ga rayuka

Al’adar nan ta kallon cutar mantuwa ga tsofaffi a matsayin abin da aka saba gani da watsi da kuma mancewa hakan na aukuwa ga daidaikun matasa, yana jawo illa ga rayuwar mutane da dama tare da tsanantar cutar rudewa a tsakanin jama’a, kamar yadda binciken jaridar Aminiya ya gano. Cutar rudewa wata cuta ce da […]

Yadda jahiltar cutar rudewa ke illa ga rayuka

Al’adar nan ta kallon cutar mantuwa ga tsofaffi a matsayin abin da aka saba gani da watsi da kuma mancewa hakan na aukuwa ga daidaikun matasa, yana jawo illa ga rayuwar mutane da dama tare da tsanantar cutar rudewa a tsakanin jama’a, kamar yadda binciken jaridar Aminiya ya gano.

Cutar rudewa wata cuta ce da take samo asali daga tabarbarewa a kwakwalwa (rasa tunani da hangen nesa da ilimi), ta yadda halayya da ilimin mutum za su rika tabarbarewa yayin gudanar da ayyukansa na yau da kullum, mutum ya rika rayuwa yana mancewa da abubuwa.

A cewar Dokta A’ishatu Yusha’u Armiya’u wata kwararriyar likitar mahaukata da masu matsalar kwakwalwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), “Galibin mutane ba su zuwa gare su sai lamarin ya yi muni. Kuma a lokacin da marasa lafiya za su je asibitin, sun riga sun yi nisa wajen mance abubuwa sun fara rudewa. A karshe sai su kare a asibitin mahaukata, kuma da damansu suna da ciwon hawan jini ko kuma ciwon suga.’

Shi kuwa Dokta Salisu Abdullahi Balarabe, wani kwararren likitan cututtukan da suka shafi kwakwalwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman danfodiya (UDTH), da ke Sakkwato cewa yayi mafi yawan tunanin mutane game da cutar shi ne babu abin da za a iya yi game da ita saboda ta shafi yawan shekaru ne ko kuma mutumin ne kawai yake wasu halaye na ba saban ba. Ya ce wannan yana kara tabarbarewar rayuwar mutumin har cutar ta yi tsanani.

Dokta Balarabe ya ce idan wai tsoho ya fara zagin mutane sai a fara tunanin tsufa ce ta fara rikita shi. Ya ce yana da kyau ga jama’a musamman dangi su fahimci cewa cutar rudewa ita ma cuta ce kamar maleriya da taifod da sauransu da za a iya yi musu magani.

“Duk abin da za ka yi a tsari irin na asibiti ba lalli ba ne ya zamo daidai da wajensa ba, inda za a bayar da kular da ta kamata ga mutumin da yake da cutar rudewar. Misali idan kana kula da wanda kullum kuka yake yi, damuwa ta shigar masa, zai fi zama mafi muni ga rayuwarsa fiye da cutar rudewar da yake da ita,’ inji shi.

Ita kuwa Misis Susana Jurbe, mai shekara 50,  ta ce lokacin da mahaifiyarta mai shekara 76 ta fara nuna alamun mantuwa, ta mance wasu lokuta a shekarar 2015, sai dangi suka dauki hakan a matsayin abin da ke faruwa idan aka fara tsufa.

Jurbe ta ce, mahaifiyarta ta fara yawace-yawace kuma daga baya sai ta gane sai ta dawo gida. “Kuma ciwon hawan jini da na suga sun bayyana mata, don haka muka dauke ta zuwa Asibitin JUTH, an ba ta magunguna kuma aka ce mu je sashin masu tabuwar kwakwalwa, inda suka shaida mana cewa alamar cutar mantuwa da rudewa, ita ma cuta ce,” inji ta.

Jurbe wadda take kai mahaifiyarta asibiti don duba ta sau daya duk bayan wata biyu, ta ce likitoci sukan yawaita yi wa mahaifiyarta tambayoyi ciki har da ko ita (Jurbe) wace ce, wace ce ’yar uwarta, kuma yau wace rana ce.

Hajara kuwa cewa ta yi ’yar uwarta Hauwa za ta fi kasancewa da lafiya a yau da iyalanta sun san cewa cutar rudewa ce ta kama ta a lokacin da matsalar ta faro a shekarar 2011. A lokacin Hauwa tana da shekara 19, sai suka yi hadari, inda wata tankar fetur ta hallaka rayuka masu yawa a hanyarta ta zuwa makaranta.

Bayan ’yan watanni sai ta rika haduwa da muguwar mantuwa. Amma sai danginta suka tsare ta a gida, tun da babu wata alama ta rauni. Kuma lokacin da aka nemi taimakon likitoci bakin alkalami ya ruga ya bushe.

Alamun ciwon Rudewa:

Wani kwararren likitan mahaukata a Asibitin Mahukata da Cututtkan kwakwalwa na Tarayya da ke Yaba a Jihar Legas Dokta Taiwo Oduguwa ya ce shekarun tsufa suna zuwa hade da mantuwa, kuma idan wani ya fara mantuwa amma yana wasu dabi’u da halaye da suka dace, za a iya daukarsa ba wata matsala ba. Amma idan ya ci gaba ta yadda wannan mutum ba zai iya tuna yanki ko layin da ke kusa da gidansu ba, to wannan wat alama ce ta cutar.

Kuma a cewar Dokta Salisu Abdullahi Balarabe na Asibitin UDUTH da ke Sakkwato, baya ga mantuwa daidaikun mutane kan iya samu sauyin halaye da dabi’u. “Kamar mutumin da aka sani da sanyi hali, ya fara zama mai fada, ya rika rasa kame fushinsa, to wannan ma alamu na farko ne na cutar rudewa,” inji shi.

Ya ce, sauran alamun su ne, mutum kan iya kamuwa da cutar rudewa ta hanyar fara mance kalmomi, maimakon ya fadi sunan wani abu sai ya ko ta rika kwatanta shi.

 Ya ce idan ta fara bunkasa, sai mutum ya fara haduwa da matsalar rashin gane fuskokin da ya sani da tuna sunayen ’ya’yansu da abokansu na kusa da dangi.

Dokta Balarabe ya kara da cewa, a duk lokacin da mutum ya gaza dauka matakan da za su taimaka masa kan yadda zai iya fahimtar yadda zai je wani wuri, wannan ma alama ce ta cutar rudewa, inda ya ce idan ta yi tsanani sai a ga mutum ya manta da inda bahaya ko dakin wanka yake a gidansa ko gidanta.

Likitocin sun ce, sauran alamun sun hada da yadda mutum zai rika tambayarka a kana bin da ka gaya masa a lokacin da kuke tattaunawa.

Adadin masu cutar:

Dokta Taiwo Oduguwa, kwararren likitan mahaukata a Asibitin Mahaukata da Cututtukan kwakwalwa da ke Yaba a Legas ya ce, a cikin dukan cututtukan hauka, kashi 22.4 sun shafi cutar rudewa ce.   

Sannan wani nazari na shekara hudu (2007-2011) kan kula da cututtukan kwakwalwa da aka gudanar a kan mutum 938 masu shekara 60 zuwa sama a Legas da wadansu likitocin mahaukata suka yi ya nuna 216 daga cikin wato kashi 36 daga cikin 100 an gano suna da cutar rudewa, yayin da kashi 5.5 (wato mutum 56) suke da cutar rudewa mai hade da kakkarwa (Alzheimer’s dementia).

Wani masanin halayyar dan Adam kuma Shugaban Sashin Kula da Halayyar dan Adam a Asibitin Mahaukata da ke Kaduna, Oguizu J. Okechukwu, ya ce bincikensu ya gano kimanin mutum uku daga cikin 100 na masu cutar hauka da suke zuwa asibitin suna dauke da cutar rudewa.

A cewar Dokta Agbir Terkura Michael wani kwararren likitan mahaukata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwai (BSUTH) ya ce, nau’in cutar rudewa da ta fi aukuwa ita ce wadda take hade da ta kakkarwa, ya bayyana cewa tana jawo tabarbarewa ko rikicewar kwakwalwa a daidai lokacin da mutum ked ade tsufa, kuma ta fi aukuwa ne bayan shekara 65 ko lokacin shekarun tsufa. Kuma wadanda suke da iyaye ko ’yan uwa masu cutar kakkarwa sun fi kusa da kamuwa da wannan cuta.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Borno, Dokta Haruna Mshelia ya ce ba a san adadin masu dauke da cutar rudewa a jihar ba, saboda abu ne da yake bukatar cikakken bincike kuma ba a gudanar da shi ba tukunna. “Amma a kasashen da suka ci gaba inda mutane suke rayuwa har shekara 100 cikin jin dadi, yiwuwar kamuwa da cutar rudewar bai kai yadda ake samu a kasashe masu tasowa irin namu ba,” inji shi. 

Abin da ke jawo ta da masu iya kamuwa da cutar:

Dokta Musbahu Rabi’u, kwararren likitan kwakwalwa a Asibitin Murtala da ke Kano, ya ce wasu daga cikin cututtukan da suke jawo cutar rudewa sun hada da maleriya mai zafi da sankarau da kwayar cutar kanjamau da ciwon suga da hawan jini da shanyewar barayin jiki da ciwon koda da rauni a kwakwalwa da kuma tsufa.

Dokta Adebimpe Alder, wata likitar mahaukata a Asibitin masu matsalar kwakwalwa na Melbille Healthcare Resources, da ke Abuja ta ce, raunukan kwakwalwa da wadansu suka samu a lokacin hare-haren bama-bamai da  hare-haren rikicin kabilanci da farmakin sojoji duk suna jawo haduwa da cutar.

Kuma a cewar Dokta A’ishatu Armiya’u ta Asibitin JUTH, yawan zukar sigari da cin abinci marar kyau da kuma cututtuka kamar damuwa da kuma rashin shiga jama’a da harkokin rayuwa duk suna iya jawo cutar.

Shi kuma Oguizu J. Okechukwu, ya kara da cewa cutar rudewa tana iya aukuwa sakamakon karancin sinadarin bitamin B9 (folic acid) da bitamin B-Compled a kwakwalwa da kuma shan miyagun kayan maye irin su hodar Iblis da wiwi da sigari da sauransu duk suna jawo cutar.

Likitoci sun ce akasarin masu fama da cutar mantuwar ba a haife su da ita ba, kuma tana iya aukuwa a sakamakon tsoro ko firgita kamar samun rauni a kai da karar harbin bindiga da hadarin mota ko abin hawa hatta ma yawan motsa jiki kamar duka da masu yin damben boksin ke yi.

 “Idan ana yawan dukan mutum a kai, kamar yadda ake yi a damben boksin, za su iya kamuwa da cutar,” inji Dokat Agbir Terkura Michael.  

A cewar Dokta Taiwo Oduguwa, kwayar cutar HIb a jikin mutum wadda take jawo kanjamau ma tana jawo cutar rudewa da mantuwar. Kuma baya ga haka yawan kwankwadar giya da asarar kudi masu yawa ko rasa iyalai suna iya jawo cutar rudewar.

Shin za a iya rigakafin cutar rudewa?

Akwai bukatar mutane su tsakaita tsarin rayuwarsu a matsayin rigakafin kamuwa da cutar rudewar. “Yana da kyau a rage shan giya ko duk wani abu da ke shafar tunani da kwakwalwa, kuma a rika motsa jiki a kai -a kai,” inji Dokta Agbir Terkura Michael.  

Ya ce, mutanen da suke fama da cutar suga da hawan jini wajibi ne su rika kula da gudanar jininsu kuma su rika shiga harkokin rayuwa da wasu wasannin motsa jiki masu kwantar da hankali. “Sukan taimaka wa kwakwalensu su rika aiki yadda ya kamata. Hatta yawan yin rubutu kan yi rigakafin cutar rudewa zuwa wani mataki, saboda yakan sa kwakwalwa ta yi tunani yayin rubutun,” inji shi.

Alaka a tsakanin cutar rudewa da HIb: 

Likitoci sun ce harbuwa da kwayar cutar HIb, na da alaka da cutar rudewa. Dokta Adebimpe Alder, ta Asibitin Melbille Healthcare Resources da ke Abuja ta ce a lokacin da kwayar HIb ke ci gaba da bunkasa a karshe wani kan shiga halin da zai fara mance abubuwa, “tana shafar tunani da sadawarka da kuma gaba dayan harkokin rayuwarka na yau da kullum,” inji ta.

Aminiya ta gano a Kano mutane da kwayar cutar HIb ta shafa da ba su karbar maganin rage zafinta su ne ke da kashi 23 cikin 100 na masu fama da cutar rudewar.

Dokta Musbahu Rabi’u,  ya alakanta karuwar cutar kan tabarbarewar garkuwar jikinsu kan munanan cututtukan da suke harbarsu wadanda a karshe suke kara rasa tunaninsu.

Maganin cutar:

A cewar Oguizu J. Okechukwu, babu wani magani da ke warkar da cutar rudewar gaba daya, amma akwai magungunan da suke saukaka ta. “Kuma muna amfani da wasu dabaru na horarwa ko motsa jiki, saboda a kowane lokaci akan samu tasgaro a tsanakin motsawar wasu abubuwa kamar tunani da kwato bayanan da suka kubce da sauransu,” inji shi.

Dokta Taiwo Oduguwa, cewa ya yi jinyar cutar ya kunshi bayar da magungunan da za su jinkirta bunkasar cutar. Wato maimakon ta bunkasa kamar a cikin shekara uku, sai ta tsawaita zuwa shekara biyar zuwa 15. “Mutum zai iya rayuwa ta dogon lokaci bayan an gano yana da cutar rudewar, sai dai abin bakin ciki wannan mutum ba zai koma daidai kamar yadda yake a baya ba,’ inji likiyan.

Shin cutar tana jawo mutuwa?

Masanin lafiyar tunanin dan Adam, Oguizu Okechukwu ya ce a lokacin da kwakwalwa ta tabarbare zuwa wani mataki da ba za ta iya yin aikinta ba, wannan mutum zai mutu, duk da cewa zai dauki lokaci a wasu lokuta. “Mai jinyar galibi kan mace saboda cutar rudewa,’ inji shi.

Abin da dangin masu cutar ya kamata su sani da yadda za su kula da su:

Dokta Balarabe na Asibitin UDUTH da ke Sakkwato ya ce, abinda mai fama da cutar yake bukata ita ce fahimta da tausayawa daga danginsa, ya ce suna iya haduwa da bacin rai da raunin zuciya da tunani idan suka hadu da mai cutar a cikinsu.

Ya ce abu ne mai matukar wahala da kalubale kula da mutumin da yake fama da cutar rudewa ko mantuwa, don haka akwai bukatar iyalai da dangi ko masu kula da irin wadannan mutane su sadaukar da kai ba wai kawai wajen biyan kudin magani ba, har ma da lokacin da za su rika ba wanda ya kamu da cutar.

Oguizu J. Okechukwu, ya shawarci dangin wadanda suka kamu da cutar su kai su asibitin mahaukata inda ake da kwararrun likitocin kwakwalwa da masu kula da majinyatar da masu bayar da sharwari da sauransu. 

Mutane da suke zama da masu cutar rudewa ko mantuwa sukan samu kansu a cikin damuwa har ta kai sun hadu da hawan jini inji Dokta A’ishatu Armiya’u, don haka akwai bukatar a samu wani masanin halayyar dan Adam a kusa don ya rika kula da shi ko su sosai. Kuma ta bayar da shawarar a samu mutum biyu ko uku da za su rika kula da mai cutar rudewar ko mantuwa ta yadda za su rika karba-karba.  

Dokta Taiwo Oduguwa ya ce  idan ma’aurata biyu suna zaune tare daya yana da cuyatr rudewa ko mantuwa, to suna bukatar masu tallafawa mutum biyu. “Mama ba za ta iya kula da Baba ba, kuma ta kula da gida ta je kasuwa ta sayo kayayyaki tab dafa abinci ta yi duka sauran ayyuka,” inji shi.Likitocin kwakwalwar sun ce masu kulawa da su, wajibi ne a kowane lokaci su sanya su rika gudanar da wasu ayyuka na motsa jiki da rayuwa ta yadda za su rage bunkasar tabarbarewar lafiyarsu.