Yadda Jama’a Ke Shan Wahalar Haɗa Lambar NIN da BVN a Bankuna

Masana na ganin matakin na CBN zai yi tasiri sosai wajen dakile hada-hadar kudaden haram

Yadda Jama’a Ke Shan Wahalar Haɗa Lambar NIN da BVN a Bankuna

Tun bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba da umarnin a hada lambar shaidar dan kasa (NIN) da na tantance asusun banki (BVN) ’yan kasar ke ta turuwa domin ganin ba a rufe asusunsu ba.

Masana na ganin wannan mataki zai yi tasiri sosai wajen matakan tsaro a fannin hada-hadar kudaden haram.

Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin matakin na CBN da kuma yadda mutane ke shan wahala gameda hakan.

Domin sauke shirin, latsa nan