…Yadda jama’a suka gagari jami’an tsaro lokacin kamfe din Buhari
Dubban al’ummar Jihar Filato ne suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka yi wa ayarin yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kyakyawar tarba a ranar Asabar da ta gabata. Wakilinmu ya gane wa idonsa yadda tun daga filin saukar jiragen sama na Jos, ko’ina mutane ne suka fito, suna murnar zuwan Shugaba Buhari Jihar Filato. […]
Dubban al’ummar Jihar Filato ne suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka yi wa ayarin yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kyakyawar tarba a ranar Asabar da ta gabata.
Wakilinmu ya gane wa idonsa yadda tun daga filin saukar jiragen sama na Jos, ko’ina mutane ne suka fito, suna murnar zuwan Shugaba Buhari Jihar Filato. Da kyar Shugaban ya samu hanyar wucewa a garin Bukur, saboda yadda dubban jama’a suka tare hanya, suna son su gan shi da idanunsu.
A lokacin da Shugaba Buhari ya isa filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos, tare da dubban jama’ar da suka rufo masa baya, filin wasan ya yamutse bayan da dubban jama’ar da ke filin da suka yi sama da awa 4, suna jirin isowarsa suka taso saboda murnar isowarsa.
Wannan al’amari ya kai ga har ya gagari jami’an tsaro su kare jama’a don haka komai ya tsaya cik, a filin ta yadda Shugaba Buhari ya kasa yin jawabi a wajen.
Gaggan ’ya’yan Jam’iyyar PDP da suka canja sheka suka koma Jam’iyyar APC sun hada da Sanata Bictor Lar da tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Alhaji Auwalu Dankurma da Sanata Sati Gogwum da Honarabul Jacob Kassem da Barista Simon Barry da Burki Ayuba Gufwan da Wokduna Kanam.
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya nuna matukar farin cikinsa, kan irin yadda dubban al’ummar jihar suka fito suka yi wa Shugaba Buhari kyakkyawar tarba. Gwamnan ya bayyana farin cikinsa ne, a wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Yakubu Dati ya fitar.
Ya ce irin yadda al’ummar jihar suka fito daga kowane lungu da sako na jihar, ba tare da nuna bambanci kabila ko addini ba, suka tarbi Shugaba Buhari ya nuna cewa zaman lafiya ya dawo a jihar.
Sanarwar ta ce wannan tarba da al’ummar Filato suka yi, ta karyata maganganun da ake yi cewa Jihar ta Jam’iyyar PDP ce.