Yadda aka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga

Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga

Yadda aka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga

Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda.

Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya.

Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya ce dubun dan shekara 65 din mai suna Nehemiah Sunday Udo ne a ranar Asabar baya al’ummar kauyen Ekpene Obo da ke Ƙaramar Hukumar Esit Eket sun ritsa shi.

John ya ce bayan samun kira daga al’ummar yankin ne ’yan sanda suka kai samame inda suka samu mutanen sun kai wanda ake zargin fadar basaraken yankin.

Ya ce ’yan sanda sun je fadar inda a suka yi awon gaba da wanda ake zargin zuwa hedikwatarsu ta jihar, kuma Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Baba Mohammed Azare, ya sa a gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce a yayin bincike “wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi mamba ne a kungiyar kwararrun maharba, amma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar da kuma haƙiƙanin manufarsa, in ji John.

Jami’in ya kara da cewa mutum na biyun kuma ’yan sanda ne suka kama shi ɗauke da karamar bindigar hannu a wani shigen bincike a kan hanyar Ikot Udoma da ke yankin Eket.

Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —Babangida

Yadda aka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga

Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan mangwaro a makaranta

NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri