Yadda jama’a suka kashe barawon babur a ofishin ’yan sanda

Ana zargin matashin da yi wa kaninsa yankan rago sannan ya sace babur dinsa

Yadda jama’a suka kashe barawon babur a ofishin ’yan sanda

Wasu ’yan sandan Najeriya a bakin aiki

Wasu fusatattun matasa sun kutsa ofishin ’yan sanda suka kwato wani matashi da ke tsare, suka kashe shi, kan zargin ya yi wa kaninsa yankan rago a garin Maigana da ke Karamar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna.

Ana zargin matashin da aka kashe a hannun ’yan sanda da sace babur din kanin nasa  da ya yi wa yankan rago, a kauyen Hayin Ice.

Wani dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa da wakilinmu cewa a gabansa fusattattun matasan suka aika wanda ake zargin zuwa barzahu.

Ya ce mutanen da suka kewaye ofishin nasu dauke da makamai da duwatsu suna ihun cewa sai an fito da shi ba za su kirgu ba.

“Ganin babu yadda muka iya dole muka fito da shi muka mika shi, inda a nan suka fara saran sa kafin daga bisani suka cinna masa wuta suka babbake shi,” in ji jami’in.

Wasu mazauna yakin sun shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin ya nemi kanin nasa raka shi unguwa, amm suna cikin tafiya sai ya soka wa kanin nasa wuka a wuya ya kashe ya, dauke babur dinsa.

Sun kara da cewa wasu matan Fulani da ke wucewa ne suka hangi abin da ya faru, suka sanar da wani da ke kan hanya, shi kuma nan take ya buga waya kauyen da ke gaba, inda aka tare wanda ake zargin, aka cafke shi aka mika shi ga ofishin ‘yan sanda da ke garin Maigana.

Bayan watsuwar labarin abin da ya faru ne matasa daga kauyakun da ke kewayen garin suka yi kukan kura suka dumfari ofishin ’yan sandan, suna neman rama abin da ya yi wa kaninsa.

Shaidun sun bayyana cewa wanda ake zargin ya dade yana yin kwacen babura yana guduwa ya bar garin sai bayan wani lokaci ya dawo.

A cewarsu, akwai lokacin da ya yi wani mummunan laifi sai da mahaifinsa ya sayar da gonarsa ya karbo shi a garin Obajana na Jihar Kogi.

Mahaifin wanda da ake zargin, wanda shi ma mazaunin kauyan Tashan Ice ne, ya ce, bai san da labarin dawowar dan nasa gari ba, domin a saninsa, yana Kano.

Kwatsam sai aka ce ga shi can ya kashe dan uwansa Abubakar, ya dauke babur dinsa, kuma an kama shi yana caji ofis kuma mutane sun yi gungu cewa sai sun kashe shi.

A cewarsa har ya fito zai je wajen sai mutane suka hana shi zuwa domin gudun kada wani abu ya faru da shi saboda yadda suka fusata.

Ya tabbatar da cewa dansa Sani wanda aka kona da Abubakar, dukkansu ’yan uwan junane, kakansu daya.

Adamu Garba ya ce yanzu abin da ke damun su shi ne irin halin da zumuncinsu zai kasance da daya bangaren ’yan uwa saboda tuni sun dauki zafi , sai dai kawai Allah Ya kawo sauki.

Duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sanda Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ci tura, duk da cewa ya ce zai kira wakilin namu bayan kiran da ya yi mashi ta waya, amma har aka gama hada wannan rahoton, magana da shi ba ta yiwu ba.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC