Yadda jama’a suka tashi lakada wa dan majalisarsu duka
An ga bidiyon yadda dan sandan da ke tsaron shi da sauran mutanen suka ranta a na kare.
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Ondo ya sha da kyar bayan jama’ar mazabarsa sun nemi kama shi su lakada mishi duka saboda rashin aiki.
Honorabaul Oluwole Ogunmolasuyi, wanda aka fi sani da West, ya je yankin Iloro a mazabarsa ta Iwo, ne lokacin da wasu matasan mazabar suka ce da Allah Ya hada su, in ba da shi ba.
Ganin haka, dan majalisar ya ce kafa me na ci ban ba ki ba, ya samu ya fada a mota ya tsere tare da ayarin motocinsa.
Bidiyon lamarin ya nuna yadda matasan ke yi wa dan majalisar ruwan ashar, a yayin dan sandan da ke tsaron shi da sauran mutanen suka ranta a na kare.
Majiyarmu ta ce dan majalisar ya ziyarci mazabar ne domin ganawa da shugabancin jam’iyyar APC, lokacin da matasan suka nemi cika hannu da shi saboda abin da suka rashin gudanar da ayyuka a yankin.
Amma West, mai wakilatar Mazabar Owo 1, ya ce ba fatattakar shi aka yi ba, ’yan bangar siyarar jam’iyyar PDP ne suka kai mishi hari.
A cewarsa, ya yi wa jama’ar mazabarsa ayyuka na gani na fada ta hanyar bayar da tallafin karatu da kayan tallafi da samar da ayyukan ci gaba.
“Har abada babu wanda ya isa ya kore ni; Ganawa muke yi a Gundunar Iloro, bayan na bar wajen ne na samu labarin cewa ’yan PDP sun kai hari.
“Ba yakin neman zabe na gama-gari na je yi ba, na je ganawa ne da ’yan jam’iyya; Bayan na tafi ne abin ya faru, kuma ’yan daba ne aka gani a bidiyo.
“Bayan na bar wurin ne aka shaida min cewa bidiyon ya karade gari.”
Amma da aka tuntube shi, kakakin PDP a Jihar Ondo, Kennedy Peretei, ya musanta cewa ’yan PDP ne suka fatattaki dan majaliar.
A cewarsa, ’yan APC ne suka fatattaki Honorabul Ogunmolasuyi daga wurin taron gundumar.
“Taron APC ne, babu ’yan PDP. Sun fatattake shi ne saboda yana neman a zabe shi a karo na biyu,” inji shi.