Yadda jama’ar gari suka kashe ’yan fashin daji 37 a Zamfara

’Yan bindigar sun je sun sake dawowa, amma duk da haka mutanen ƙauyen Matusgi suka ƙara aika da dama cikinsu lahira

Yadda jama’ar gari suka kashe ’yan fashin daji 37 a Zamfara

Wasu daga cikin ’yan bindigar Jihar Neja.

Al’ummar ƙauyen Matusgi da ke Jihar Zamfara sun yi kukan kura sun aika ’yan fashin daji 37 lahira a lokacin da ’yan ta’addan suka kai musu hari.

Mazauna ƙauyen Matusgi da ke Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda sun ɗanɗana wa ’yan fashin daji da suka je yin garkuwa da su kuɗarsu ne da tsakar ranar Laraba.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa wannan ne karon farko da ’yan bindiga suka kwashinsu a hannun ƙauyen ba, duk da cewa a baya al’ummar ƙauyen sun sha yin fito-na-fito na ’yan fashin daji.

Majiyar ta ce da misalin ƙarfe 2na rana ne ’yan fashin daji suka shiga kauyen a bisa suna harbul kan mai uwa da wabi, ba su sani, ashe mutnen garin sun riga sun samu labarin zuwansu kuma sun riga sun shirya musu.

Suna cikin harbe-harben ne jama’ar garin suka yi musu kawanya, suka nemi hana su tserewa, suna yi musu luguden wuta, har suka kashe ’yan fashin daji da dama.

An shafe kimanin awa guda al’ummar ƙauyen Matusgi suna ragargazar ’yan bindigar, kodayake su ma sun rasu mutane 10 a musayar wutar.

Bayan ’yan fashin dajin sun tsere, daga bisani sun sake dawowa, amma suka yi rashin sa’a mutanen sun shirya musu, suka kara aika jimillar ’yan ta’adda 37 lahira.

Hakimin Matusgi, Alhaji Ciroma Muhammad, ya ce bayan ɗauki-ba-daɗin, mutanen ƙauyukan da ke kusa da su sun ce sun ga ’yan fashin daji suna wucewa da gawarwakin ’yan uwansu a kan babura.

Ya ce “karo na 13 ke nan da ’yan fashin daji suke kawo mana hari, makonni uku da suka gabata sun sace mana mutane 23, yawancinsu mata.

“A wancan har suka fice ne ba yi ba, sai sai bayan da suka tafi suka yi kafin muka san sun shigo mana.”

Ya ce sun buƙaci kuɗin fansa N150,000 a kan kowane mutum guda, amma bayan an biya kuɗin mata bakwai kawai suka sako, har yanzu suna riƙe da sauran.