‘Yadda jami’an Hukumar FRSC suka jawo aka hallaka mai gidanmu’
Wani rikicin direbobin motar haya da jami’an Hukumar Kiyaye Haxxura ta Qasa (FRSC) ya jawo bindige wani direban motar haya, mai suna Malam Husaini Andaza bayan da jami’an na Hukumar FRSC suka nemi xaukin jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSDSC), kuma xaya daga cikin jami’ansu ya harbe shi tare da raunata wani xan sanda. […]

Wani rikicin direbobin motar haya da jami’an Hukumar Kiyaye Haxxura ta Qasa (FRSC) ya jawo bindige wani direban motar haya, mai suna Malam Husaini Andaza bayan da jami’an na Hukumar FRSC suka nemi xaukin jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSDSC), kuma xaya daga cikin jami’ansu ya harbe shi tare da raunata wani xan sanda.
Xaya daga cikin ’yan uwan marigayin mai suna Malam Uzairu Muhammed ya ce marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya 18 da matan aure huxu da ’ya’yan ’yan uwa 8 da qanwarsa da yake xaukar nauyi, kuma in ban da xansa xaya mai suna Mubarak Husaini mai shekara 18 duk sauran ’ya’yan qanana ne.
Malam Uzairu ya ce lokacin da suka samu labarin abin da ya faru da xan uwansu sun shiga tashin hankalin da ba su tava ganin irinsa ba, ganin shi ne jigon gidan domin dukan ’yan uwansa babu wanda yake da qarfin da zai iya xaukar xawainiyar ’ya’yan da matansa wajen ciyarwa balle a yi maganar karatu.
Ya buqaci Masarautar Dutse ta shiga maganar domin ganin an biya su diyyar xan uwansu saboda su marasa qarfi ne ba su da qarfin xaukar nauyin yaran da ya bari.
Uwargidansa, Zainab Husaini Andaza mai shekara 40, ta ce ranar da aka harbe mijinsu hankalinsu ya yi matuqar tashi ganin cewa talaka ne kuma duk da qaramin qarfinsa shi ne yake xaukar nauyin gidansa da taimaka wa ’yan uwansa amma haka kawai wani jami in tsaro ya sa bindiga ya ragargaza masa kai ya halaka shi.
Ta ce duk da cewa marigayin mijinsu talaka ne yana lura da su yadda ya kamata komai a cikin wadata kamar yadda addini ya tanada. Sai ta buqaci mahukunta su yi adalci wajen ganin an hukunta wanda ya halaka mijinsu tare da biyansu diyya domin a sauqaqa rayuwar iyalai 26 da ya bari.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kakakin Hukumar NSDSC, Malam Adamu Shehu ya ce ba bisa ganganci ma’aikacinsu ya harbe marigayin ba kamar yadda jama’a suke ta yayatawa. Ya ce lokacin da suka je hedkwatar Hukumar FRSC sun je ne da nufin kai musu agaji saboda an samu rahonto kan rikicin da ke neman faruwa a tsakaninsu da direbobin motoci haya. Ya ce zuwansu ke da wuya sai mutane suka nemi auka musu suna qoqarin qwatar bindiga a wajen wanda ya yi harbi, inda shi kuma cikin kuskure ya harbi wani xan sanda a hannu kuma harsashi ya wuce ya samu marigayi Malam Husain a kai shi ne ya rasu a lokacin da ake qoqarin ceto ransa a Asibitin Rasheed Shekoni da ke Dutse.
Ya ce bincike ya nuna wanda ya yi harbin mai suna Jamilu xan asalin Qaramar Hukumar Kiyawa yanzu haka yana hannun ’yan sanda suna bincike kuma da zarar sun kammala za su gabatar da shi a gaban kotu.
Ya ce xan sandan yana babban asibitin Dutse, kuma hukumarsu ta kai masa Naira dubu 25, a matsayin tallafi, inda ya ce su kuma iyalan marigayin an ba su agajin Naira dubu 100 da shinkafa da dawa da gero da wake buhu xaixai da jarka biyu na man gyaxa tare da kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Ya ce sun yi nadamar faruwar lamarin, ya ce wannan ne karo na bakwai da suke taimaka wa jami’an Hukumar FRSC, amma ba a tava samun matsala ba sai a yanzu.
Wani mazaunin Dutse mai suna Malam Shehu Musa Limawa ya ce ba domin taimakon da ’yan sanda suka kai ba, da an hallaka ma’aikatan Hukumar FRSC da dama tare da qone musu ofishi da ababen hawa.
Kakakin Hukumar FRSC ta Jihar Jigawa Malam Adamu Ado ya ce ba ya da ikon yin magana a kan lamarin. Yayin da wani jami’in hukumar ya ce shugabanninsu na qasa sun aiko shugaban, wanda xan qabilar Ibo ne, ya tafi Abuja.
Bayanai sun ce ana zargin shugaban hukumar yana sanya ma’aikatansa suna takura wa direbobin motocin haya da sauransu ta hanyar yi wa jama’a tara mai yawa kan laifin da bai kai ya kawo ba.
Mataimakin Shugaban Qungiyar Direbobi ta Qasa reshen Qaramar Hukumar Dutse, Malam Adamu Shehu, ya ce sau bakwai suna zama da Shugaban Hukumar FRSC amma baya xaukar shawararsu, ya ce a taronsu na qarshe har likita ya xauko yana cewa wai zai yi wa direbobin motar haya gwajin qwaqwalwa saboda ba su da hankali. Shi ne likitan ya ce idan za a fara gwajin dole ne a fara ta kan ma aikatan hukumar, lamarin da ya sa aka tashi daga taron baram-baram.
Ya ce bayan haka ne ranar Laraba ya fito shi da kansa da yaransa suka bazu a kan titi wajen su 80 suka riqa kama mutane babu gaira babu dalili, lamarin da ya harzuka ’ya’yan qungiyar suka kai wa ’yan uwansu agaji domin ganin an saki motocin.
Binciken wakilinmu ya gano cewa Galadiman Dutse da Hakimin Cikin Gari, sun sha yi wa dogarawan hanyar nasiha a kan yadda suke gudanar da aikinsu amma suka qi gyarawa don inganta hulxarsu da jama’a.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wanda ake zargi da yin harbin yanzu haka yana sashin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar ana gudanar da bincike a kai. Ya ce rundunar ba za ta zuba ido ana asarar rayukan jama’a ba duk wanda ya taka doka dole ne doka ta yi aiki a kansa.